Babi na hamsin da biyar ( 55 )

1K 102 21
                                    

A hut in shakatawan Daddy su ke zaune. Ya hade giran sama da na kasa sai dai ko a jikin ta domin hakan ba bakon abu bane a gare ta.

"Za ki iya Fada min dalilin ki na yin abinda kika yi"

Murmushi tayi sannan tace "Sorry Ya Faisal, i think it of benefits to both of us"

Wani irin kallo ya aika ma ta. Irin Wanda ya ke firgita Yan Mata Amma banda kallan su Meema.

Dauke idanuwan ta tayi tace "Mummy ta dade ta na son in yi aure sai dai ni hakan kwata kwata bai cikin tsari na a kwana kusa. Tun Daddy bai sa baki har ya zo ya fara supporting inta. Na fahimci problem in mu kusan daya da Kai domin kullum magana mama kenan kayi aure. Nasan ka zo wurin mummy ne ka fada ma ta yanda ku kayi da Maman da kuma baba akan batun ka fiddo Mata kayi aure which nasan ba ka da ra'ayin hakan kaman yanda ni ma hakan ne"

Kallon ta ya ke gabadaya yana mamakin karfin halin yarinyar. Ya tuna zuwan ta kaduna kafin ta karaso Abuja. Kusan a gaban idon ta aka mai maganan auren, har lokaci su ka deban mai ko ya fiddo ko su sa mar mai ko wacce ma. Murmushi yayi tuno yanda maman ta Kira shi bayan nan ta ke fada mai "Ni kam in na wajen sun gagara mai zai hana ko meeman ka nema Faisal rashin auren Nan naka bai min Dadi Allah kana saurayi mai jini a jiki. Anya Faisala ba matan banza kake bi ba a Abujan nan kuwa?"

"Subhanallah Mama ki min kyakyawan zato mana"  ya amsa ta.

"To in ba hakan ba duk sa'anin ka ba sunyi auren ba? Ince duk cikin Yan uwana wadanda kuka taso tare duk sunyi sun barka. Sun ba yan uwan su ka aura ba ka ga wani abu ya faru?"

"To Wai Mama ita yarinyar tace Miki tana so ne?"

"Yo ai meema ta fika shiriri ta da har za ta kalli wani tace tana so. It's a suggestion and it may work"

Kallon meeman yayi yanda ta dage tana zubo mishi bayyanai "so what are you trying to say"

"Shine naga mai zai hana mu rufawa juna asiri ayi auren for some months sai muce mu su is not working anymore. Kaga ta hakan kowa ya fita daga matsala kenan"

Dariya ta so ta bashi Amma sai ya fuske. Tana ganin kaman tafi kowa wayau sannan da alamun akwai special rainin da yarinyar ta mai Wanda shi bai San dalili ba. "In Kinga hakan ya Miki tou shknn ba matsala"

Ajiyan zuciya ta saki ganin plan inta yayi working. Daman ta San yanda ya ke dinnan da wuya ta samu problem tunda shima solution ya ke nema. Sannan ta San bai da magana ko ra'ayin da zai sa ya hana ta aikin ta da dukkan sauran plans inta.

"Thank you Amma wata nawa kake ganin ya isa?"

Zuwa yanzu kunshe dariya ya keyi yace "Duk yanda kika yi deciding i don't like too much talking"

"Ina ga 1 year will be okay. 12 months kenan"

Shrugging shoulders in shi yayi alamun he don't care. Which is the thing she sees in him da har ya sa ta zabe shi a wannan fannin.

"Ina kaman ya Kama ta mu sa rules yanda plans inmu zai yi working zuwa time in da zai kare"

Lallai abun naki yayi kamari. Ya fada a ranshi. Shi dai earn in shi daya zai je ya fadawa mama yayi abinda tace, zai auri ita meeman.

"Okay list your rules"

  "Daya ne ma ai ba yawa shine: kowa zai yi rayuwan shi freely ba takura. Kowa yayai minding business in shi kawai. Like zan iya zuwa duk inda naga dama ba tare da tmby ba haka kuma am free to do anything am willing to. Sauran na ka"

"Am okay with everything you said"

"Toh Ina ganin we are done I. Do we need to sign it and keep an evidence" hararan ta yayi "we are enough evidence"

Nodding tayi kafin ya tashi ya Mike ba tare da sallama ba. Tabe baki tayi ko a jikin ta ma ita.

.....

Iyaye sun shiga maganan meema da Faisal. Su Suhaila kam mamaki duk ya cika su. Kasa jurewa Asmau tayi sai da ta Kira ta "so all these hatred ashe love ne in the most silent way"

Tsaki meema ta ja "Kinga ban fa son tone tone, abinda ya wuce ai ya wuce"

"Ah Yaya meema bar ni nayi tsokana na. Miye bakin ki bai fada ba?" Dariya tayi kawai.

An tsaida magana akan tana gama school date in zai Kama. Tuni har kowa ya fara shirye shirye Amma banda Iyayen shagalin domin ko ko numbobin juna ba su da shi balle wani abu ya shiga tsakanin su. Kowa kawai life in shi yake yi ba tare da ya damu da na dan uwan shi ba.

.....

Zaune su ke suna hira bayan sun gama dinner. Yanayin shi kadai ya tabbatar ma ta da akwai abinda ya ke so ya sanar ma ta. Rahma mace ce mai matukar kokari wurin fahimtan mijin ta ta kowani bangare. Hakan ya sa Muhsin ya ke matukar jin dadin zama da ita haka kuma ya ke girmama ta saboda ita ma duk wani al'amari na shi to tabbas yana da mahimmanci a gare shi.

Matsawa tayi sosai kusa dashi ta shige jikin shi. Murmushi yayi ya kara jawo ta ya kwantar kan kirjin shi tana sauraron yanda zuciyan shi ke bugawa. "Say it please" bai yi mamaki ba domin ya San za ta gane in.

"Promise you will understand me and it won't upset you"

Tana son dagowa ta kalli idanun shi jin irin amsan da ya bata Amma bai bata Daman hakan ba. Kara matsota jikin shi ya ke yi.

"I don't want to make a fake promise Amma i will try and understand ko ma menene kaso dashi"

Ajiyar zuciya mai nauyi ya saki yace "Rahma Ina so zan nemi auri" wani irin bugawa zuciyan ta tayi. Da sauri ta rike kirjin ta ba tace komai ba for minutes. Duk da ta San zai so tace wani abu, sai da tayi calming kanta da ambaton sunan Allah a zuci sannan ta ce "Dr so soon haka? Any problem?"

"Not at all the lady ke ma kin sani da akwai zan fada Miki. Remember we always communicat..."

Da sauri tace "to what happen?"

"You will know everything"

"Ina sauraron ka" ta fada da murya mai rauni. Tausayin ta yaji ya mamaye shi Amma kuma he can't no longer denied his feelings.

"Ban fara neman ba, ita kanta ban fada Mata ba tukunna. I want to tell you first"

"Kana so kace min you are not in relationship with her now?" Girgiza Kai yayi yace "Aa, ban so naji kaman in a cin Amanan ki. Nayi making decision in neman ta shiyasa na ke sanar Miki kafin na fara"

Shiru ne ya ratsa tsakanin su. Ya San Rahma ba ta da wuyan sha'ani Amma surely this will be hard for her. Musamman da ta ke fama da laulayin ciki . Jin Shirun na ta yayi yawa ya sa ya katse "Rahma, I need you support."

"How long do you know her" shiru yayi yana fargaban yanda amsan zai zo mata.

"All my life" ya fada a takaice

"Yaushe ka fara son ta to?"

"All my life" shiru tayi tana jinjina maganan. Ta San Muhsin ba zai mata karya ba.

"So meyesa ba ka aure ta ba? Why do you decide to marry me instead?

"Na dade da giving up akan ta. Na so na hakura da ita Amma zuciya ta ta kasa hakurin. I tried my best but it seems futile"

Wani irin zafi ta ke ji yana ratsa zuciyan ta jin bayanin da mijin ta abin kaunar ta ya ke Mata akan wata mace. Ta tabbatar soyayyan da ya ke ma yarinyar ba karamin so bane. Amma ya zata yi? Tunda ta riga ta tabbatar ma kanta mijin ta na kaunar ta.

"Allah yasa alkhairi"

"Ba ki tmby wacece ita ba"

Amsan da ta bashi ya sa yayi freezing a wurin. Da sauri ya runtse ido yana jin abinda ta fada yana ratsa tsakiyan kanshi "I know, Suhaila ce"

A zuciyan shi ya fadi "is it that obvious?" Unknown to him ya fito fili.

"I've been suspecting..."

Shiru su kayi yayin da su ke sauke numfashi kusan a tare. Kowa da abinda ya ke ji yana ratsa zuciyan shi.

"Will you please support me?" Ya fadi a hankali cikin kunne ta.

"I wish the best for us"

Pecking inta yayi akan goshi sannan ya rungumo ta sosai kan kirjin shi "Thank you my lady".

ABINDA KAKE SOМесто, где живут истории. Откройте их для себя