Babi na sittin da biyar ( 65 )

956 83 1
                                    

Kwana biyu da tafiyan Fadila ya dawo Daman tun ranar da Fadilan tazo ya tafi da dare. Zuwa lokacin ta sake sosai don har school ta koma. Ta yi kokarin maida lamarin ta ga Ubangijin ta and everything is going good now don ko har ta fara maida jikin ta.

Tun daga bakin kofa ya fara jiyo kamshi. Murmushi ya saki sai kuma ya daure fuska ya karasa dakin shi bayan yayi sallama. Turo kofan dakin nashi tayi ta shigo da murmushi kwance kan fuskan ta tace "Love Sannu da dawo wa"

Ba tare da ya juyo ya kalle ta ba yace "sannun ki"

Jikin ta ne yayi sanyi ganin yanda ya Mata. Daurewa tayi ta shiga bayi ta hado mishi ruwan wanka. "Na hada ma ruwa" ta fada. Nodding kawai yayi ba tare da ya amsa ta ba. Dinning table fita ta fara kokarin hada abinci.

Ko da ya fito wanka ya tadda komai is ready sai dai ko kallon arziki bai ma dinning in ba. Cikin shiga mai kyau ya fito kaman Wanda ke Shirin fita "Love your food is ready"

"Am invited to lunch" ya fada yana nufan kofan. Kafe shi da ido tayi har ya fice. Shiru tayi ta rasa abin yi domin ta San ita ta ja komai. Sai dai she won't give up.

Bai dawo da wuri ba. Ko da ya iso ya dauka zai iske ta yi bacci Amma ga mamakin shi sai ya iske ta zaune a falo. Da alamun shi ta tsaya jira.

Da murmushi kwance akan fuskan ta tace "Sannu da zuwa"

"Sannun ki" ya amsa ya na nufan hanyan dakin shi. Samun kanta tayi da bin shi a baya. Bai ce Mata kala ba har ya yi wanka ya fito yayi nafilolin shi. Ganin ta na kwance tana Danna way kawai ya kashe wutan dakin shima ya kwanta ta daya gefen.

Sai da ta bari ya kwanta sosai sannan ta lallaba a hankali ta daura kanta akan kirjin shi tana shafa fuskan shi a hankali. Bai tanka ba duk da haka. In a very slow tone tace "Loveee" saurin runtse idanuwan shi yayi jin yanda muryan ta ya ratsa jikin shi. She truly have a huge effect on him da ya ke ganin ta dauka for granted ta mishi abinda ta ga dama.

Sautin kukan ta ya fara ji a hankali ganin ya ki tanka ta. Still shiru ya Mata duk da yanda ya ke jin kukan har cikin ranshi. Saukan ruwa ya fara ji akan rigan shi hakan ya tabbatar mishi kwalla ne. A hankali yace "ki dagani am sleepy"

Kara shigewa jikin shi tayi sabanin abinda yace. Murya ta na rawa ta ce "pls.. pls... L o v e I'm very sorry for the pain and embarrassment I caused you. You are a devoted partner, and you didn't deserve my thoughtless words and actions. I hope you can forgive me and give me a chance to make things better between us."

Ajiyan zuciya ya saki jin she finally admit her mistake and she is apologizing. Sai dai kuma bai niyyan barin ta haka ba saboda gaba. "We are going back to Nigeria after your Exams. I've already booked the tickets"

Saurin tashi tayi ta kunna fitilan dakin. Sannan ta zuba mishi ido tana girgiza Kai "I don't want to, not anymore. Please let it go"

"I respect your decision Asmau, so am giving you what you want, am taking you home"

Zaro manyan idanuwan ta tayi "But Love you are my home, ba inda zani Ni kam"

Dauke kanshi yayi daga kallon da ta ke mishi yace "it ur choice after all"

Komawa jikin shi tayi ta dago hannayen shi ta daura kanta "love am not going so you can go alone. Kuma fa na baka hakuri pls"

"Ke wani irin hakuri ne ban baki ba Asmau"

Juyo da ita yayi ta yanda za su iya kallon juna. Kwayan Idonta ya kafawa ido yana kallon how sorry she look. She is not a pretender and he knows it. Tana it's hango soyayyan ta kaman yanda ta saba gani kwance a idanun sa, hakan ya kara ma ta hope.

"The problem is you are taking Me and my love for you for granted. You are using it against me saboda kinsan i will tolerate you ko?" Girgiza Kai tayi tace "believe me ba haka bane Ni fa Ina son ka kaman yanda kake so na remember"

ABINDA KAKE SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang