Tun Suhaila na sa ran Muhsin zai neme ta har ta cire. Yau kwana uku kenan da yin case insu na mahmud. Kokarin mantawa da lamarin shi ta keyi Amma Sam Ina abun ya ci tura.
Da sallama ya shiga cikin gidan nasu. Kasancewar week day ne ya sa ba kowa a gidan. Mami da Abbah duk suna aiki. Yaran sun tafi school sai Suraj da yake kyautata zaton baya gidan. Kamshi da yaji na busowa tun daga kofa ya sa ya gane Suhaila na gida don ko ba su da cook a gidan.
Direct kitchen in ya nufa. She is very busy tana hada kayan salad in da ke gaban ta. Ko sallaman shi ba ta ji ha saboda ear piece in da ke makale akan kunnen ta. Da karfi ya buga kofan kitchen, hakan ya sa tilas ta waiwayo. Tayi mamakin ganin shi Amma sai tayi kokarin boye hakan. Kasa magana tayi kawai tayi still tana kallon shi.
Siririn murmushi yayi yace "Sannu da aiki princess" kallon mamaki ta bishi dashi coz shi can't remember ya taba Kiran ta da wani suna makamancin hakan.
"Fushi kike da wani dan na koran Miki prince?"
Sai yanzu ta gano kan zancen. Tabe baki tayi tace "Ina wuni? Ya aiki? Ya sister Rahma?"
Idanuwan shi na kanta. Ya karasa dinning in kitchen in ya zauna.
"Tana lfy, tace in gaishe ki"
"Ina amsawa, ta warware?" Ta fada a ranta tana fadin ba sai ka nuna min kana son matar ka ba by choosing to ignore the rest gaisuwan.
"Ahh ta warke sosai. Let me help you"
Kallon shi ta danyi. Kaman za tayi objecting sai ta basar ta dauki salad in da ta ke yanka wa da tumatir da cucumber da sweet pepper ta ajiye mai kan dinning table in.
Dauka yayi ya cigaba da yanka Mata ita kuma ta fara kokarin hada stew.
"Yanzu ki daina kiwuya ne?"
Kallon shi tayi kaman za tayi kuka tace "I don't have any choice, zama gida da maza gabadaya"
"In kinyi zuciya kiyi harama ki bar gidan mana"
Girgiza Kai tayi tace "bayan ka koran min saurayin"
Ba ta fuska yayi yace "me yace Miki?"
"Nothing"
"You are lying"
"He said he couldn't come kuma nasan akwai abunda ka fada mai ne shiyasa"
Hararan ta yayi yace "ke dai yi min sharrin kawai"
Shiru tayi ta cigaba da aikin da take yi.
"So yanzu har ignoring questions Ina ake? In yi magana a share Ni"
Kaman za tayi kuka ta kalle shi. Don har ga Allah shi is not in the mood of talking. Ya ma barta da halin da ya ke saka ta Amma zai zo ya cika ta da surutu.
"Na ishe ki koh?"
"Wai what happen ya Muhsin? Da baka da surutun nan."
Shiru yayi na Dan seconds kafin yace "You happen" a hankali ya fada Amma he is very sure taji shi.
Cike da kunya yace "Nine kike cewa na cika magana ko? Thank you and don't worry i won't talk again" yanda yayi maganan a hankali ya sa jikin ta yayi sanyi duk da ta San tsokanar ta ya ke.
Bai ko kara maganan ba har ta kammala girkin ta amshi salad in ta hada. Shi dai yana zaune a kitchen. Fridge ta bude ta dauko zobon da ta hada since, zubawa tayi a jug ta ajiye mishi akan dining in. Bai ce komai ya dauka ya Sha, Daman ta San yana son zobon.
Yana zaune har ta gama tattare kitchen in sannan ta ce "are you eating?"
Yi yayi kaman bai jita ba sai can yace "ashe ke marowaciya ce?"
ŞİMDİ OKUDUĞUN
ABINDA KAKE SO
RomantizmCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...