Babi na talatin da bakwai ( 37 )

971 105 12
                                    

Ranar juma'a bayan an sauko sallah dukkanin jama'a su ka shaida daurin auren Muhsin da Rahma akan sadaki Naira dubu hamsin, lakadan ba ajalan ba. Daurin auren ya samu halattar mutane da dama, can na hango ango baki yaki rufuwa kaman gonan auduga sabanin amaryar da ta ke ta faman kuka duk da dai kowa yasan kasan ranta farin ciki ne cike tab.

Duk wani farin ciki da sha'anin da ake ciki Suhaila gefe tayi. Ba taso kawai tace za ta bar gidan ne domin ko Mami ba za ta bar ta ba. Amma gabadaya ranar kanta juyawa ya ke. Shin wannan wani irin kaddara ne haka? Me ke damun ta ne Wai? Ta San cewa bakomai bane ya ja Mata wannan abun sai sharrin So. Tabbas ta yarda cewa Abinda kake so shi ke wahalar da Kai... Duk da halin da ta ke ciki ba kowa bane ya ke iya fahimta sai Wanda ya mata mugun sani Amma banda hakan miskilanci ta da taurin zuciyan ta ba zai bari a fahimci halin da ta ke ciki ba.

Ana idar da sallan isha'i a ka tafi dauko Amarya, da kyar aka rabo ta da gidan su. Ta Sha kuka har ta koshi. Sai da aka fara kaita wurin Mami aka danka ta sannan aka tafi da ita gidan ta da ke badawa lay-out. Ba laifi mamin ta danyi faran faran duk da ta raina musu a bangaren komai, su ko komai dai dai iyawar su su kayi. Washegari, aka kara dauko Amarya gidan Mami in da aka yi budan Kai Wanda ya koma event mai zaman kanshi. Da yamma kuma aka tafi walima a cewar Mami fa kenan. Ai ko an ga sabanin haka, tabbas anyi wa'azi Amma kuma da kida aka tashi taron. Tuni su meema su ka shiga cikin amare suna jan amaryar a jiki Amma fa banda Suhaila. Dan waliman ma latti ta ja kuma mid way ta dawo gida abinta.

Ko da ta shigo gidan ba ta tarar da mutane sosai ba sai dan wadan da ba a rasa ba dake duk an tafi waliman manya da kanana. Ta dai hango maza a tsaye ba ta na lura dasu waye ba kawai ta karasa cikin gidan tayi dakin ta da su ke zaune yanzu tare da Yan matan.

Kaman an ce ya daga idanu ya hango ta za ta shiga gate in. As usual sai da gaban shi ya buga kaman sauran lokutan, sai dai in bai sa ta a idanu ba. A yanda ya lura kaman akwai abinda ke damun ta, gabadaya kwana biyu a ce mutum kaman Suhaila ta dawo sukuku ai dole da alamun tmby. Haka kurum ya ji ba dadi duk bai San miye matsalan ta ba. Bai San dalilin da ya damu da ita a cikin yan kwanakin ba. Samun kanshi yayi da son jin damuwan  ta, kallon Faroukh yayi sannan yace Dan ban 10 minutes bara na shiga gida kafin mu wuce. Bai tsaya sauraron complains in Faroukh in ba ya shiga gidan kawai direct. Sai dai yayi rashin sa'a ta riga da ta Kai daki kuma no way zai shiga can cikin gidan. Tunanin kiran ta yayi sai dai kash! Ya tuno bai da numban ta. Wani zuciyan ke fada mishi Wai Kai ina ruwan ka? Ya kayi tafiyan ka kawai ka kyale ta sai dai mafi rinjayen barin zuciyan ya hane shi da hakan. Idea ne ya fado mai, da sauri ya Kira Suraj yace mai ya turo mai numban Suhaila zai sa ta abu urgently, ai ko ba yai cikakken minti biyu ba Suraj ya turo numban. Da azama ya Kira ta sai dai har ya katse ba a dauka ba. Gaban shi ne ya tsinke ya daure ya sake Kira ai ko gab da zai katse ta daga wayan.

Sallama ya mata, muryan shi kawai taji tasan shi ne Amma ta kasa gasgata hakan, tasan ba sa jituwan da zai iya daukan waya ya Kira ta. Amma kuma tabbas shine din lfy kuwa? "Kina ina ne?"

Kai tsaye tace "gida"

"Okay, ki same ni a side in Abbah" ko kafin tayi magana har ya katse wayan.

Ba Wai dan ranta na so ba ta dauki zumbulelen hijabin da ta ke sallah dashi ta sa akan rigan bacci da ta afka a jikin ta tana shiga dakin. Ba ta son ganin shi ba don komai sai dai dan ta San zai soso Mata abinda ke Mata kaikayi, sai a lokacin ta tabbatar da ake cewa kuka ma Rahama ne.

Sai da ta dauraye fuskan ta sannan ta nufi side in Abbahn, wanda ta tabbatar ba kowa sai shi Muhsin in da ya Kira ta.

A hankali ta shiga falon ta same shi ya na zaune gafa daya kan daya yana danne danne a wayan shi. ya Sha kaftan navy blue, kayan ya matukar karban shi sai shekin angonci ya ke yi. Wuri ta samu ta zauna a can gefe kan one seaters in da ke kusa da two seaters in da yake zaune.

Ba Wanda yayi magana a cikin su har kusan minti biyar. Sai da ya ajiye wayan sannan ya dago ya kalle ta ya sakan Mata murmushi Wanda yayi mugun tafiya da imanin ta. Da kyar ta sassaito natsuwan ta ta yanda ba zai fuskance ta ba, anya ba da gayya Muhsin ke mata haka ba? Tambayan da ta ma kanta kenan. In ko haka ne lallai ya gano ta kenan? Tunanin kadai ya sa ta faduwar gaba, ai ko da ta shiga uku.

"Malama Suhaila" ya fada yana karantar fuskan ta, ai gabadaya ma ji tayi kaf duniya ba Wanda ya iya Kiran sunan ta kaman Muhsin.

"Zan so in miki tuni guda daya in kuma sani ba kiyi ba to zan sanar Miki. Wajibi ne ga musulmi in yaje wuri ya yi sallama sannan ya nemi izinin shiga wurin kafin ya kutsa Kai Amma ke kuma sai na ga akasin haka daga gare ki, ina fatan ganin gyara a wurin ki Dan Allah ba Dan ni ba" zuwa yanzu zufa ya fara keto Mata duk da AC in da ke kokarin aiki a falon. Shin da gaske Muhsin gyara ya ke son Mata ko kuma kawai ya neme ta ne ya tozarta ta?

"Bakomai ya sa na Kira ki have Daman ina son tmbyn ki ne, ya jikin naki kin warke?"

A hankali ta amsa da eh.

"Ma Sha Allah. Let me be straight forward Suhaila, you are not yourself kwanan nan, shin me ke damun ki haka?" Galala tayi tana kallon shi sannan ta kakalo murmushi tace "ni? Am okay fa me.."

Saurin katse ta yayi yace "ehm ehm you are not" kallon ta yake cikin ido ta yanda ba za ta samu Daman musa mishi ba. Kasa jure kallon cikin idanuwan shi tayi ta lumshe idanu. Tunani ya fado mata, shin me ye sa ma ya damu da halin da ta ke ciki? A sanin ta kwata kwata Muhsin bai shiga shirgin ta. So why the sudden change?

A hankali tace "and why do you care?" Ajiyan numfashi ya saki a ranshi ya ke fadin da na San amsan tmby da nima naji Dadi ai Amma fili ya ce Mata "i hate to see people in bad situations, kallo daya na miki nasan akwai abinda ke damun ki. Forget about our differences ko kuma wani rashin jituwan mu. I wants to change that Suhaila wlh in nace miki rayuwan da kike living bai damu na to tabbas na miki babban karya. Ke mace ce wacce ta fito daga gidan mutunci, ban zan so duniya ta zage ki ba a matsayin ki ta yar uwata. Na dade Ina son fahimtar da ke hatsarin rayuwar sai dai kash ban samu Daman hakan ba sai yanzu na ke ganin na samu opportunity in da bazan bari ya kufce min ba. Kinga damuwan da kike ciki? Duk da ban San miye ba ina da tabbacin da za ki maida al'amuran ki da Allah to da tabbas abun ba zai Kai haka ba." Nasiha ya Mata sosai mai ratsa jiki, abun mamaki nasihan ya shiga jikin ta sosai. A siyasance ya dinga nuna Mata mahimmancin ilimin addini da yi Mata tayin samun shi ko da a wurin shi ne in ta aminta da hakan.

Shawarwarin sun samu zama cikin zuciyan ta, ko ba dan komai sai dan yanda ya ke magana cikin natsuwa da lamana. Shin daman haka Muhsin yake? Tambayan da ta ke ta wa kanta kenan. Kenan Daman duk halayen da ya nuna Mata a baya misunderstanding in shi ta ke?

Smiling ta saki, hakan yayi matukar taimaka wa wurin karawa fuskan ta kyau musamman ma gare shi, sai dai shi ba Wai kyau in ya ke ma wa ba. A hankali ta fara magana "Thank you, I shall try and follow your advice"

Da sauri yace Mata "promise"

Murmushin nan dai kawai ta kara saki tace "kaina na ciwo sosai, I need to go and sleep"

"Okay then later, be sure to rest well"

A tare su ka mike kowa ya nufi inda za shi. Sai dai dukkan su jin su su ke wani iri, kasantuwar hakan bai taba faruwa tsakanin su ba. Dukkan su dai suna cikin farin ciki, shi Muhsin farin ciki saukowan da tayi kuma yana burin daura ta akan hanyar gsky. Ita ko ta dan samu sassaucin abinda ke damun ta.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now