Musamman ya dawo gidan karfe daya ya duba tana nan ko bata Nan. Tsaf ya duba gidan ba alamun ta sannan ya sauko ya samu mai gadi ya tmby shi. Nan ya ke sanar mai yana fita ta fita. Shiru yayi hade da citse dan yatsa, mai gadin na tmbyn shi lfy? Ya girigiza Kai ya shiga mota ya koma wurin aiki.
Sai bayan Sallan magrib ya dawo gidan Amma still ba ta dawo ba. Rasa abin yi yayi tsaban takaici, dawowan shi daga Sallan isha'i kenan ya ji shigowan motan ta. Wuri ya samu ya zauna a parlon yana jiran shigowan ta.
Da sallama a bakin ta tashiga Falon. A hankali ya amsa. Ganin yanda ya hade rai fuska a hade yasa ba ta ce mai kanzil ba ta bi hanyan upstairs.
"A ina kika tsaya?" Ta ji tmbyn sanda ta ke Shirin hawa stairs. Aniya ta dauka na yau za ayi ta ta kare. Ba ta son abinda ya ke Mata kuma dole yau ta kawo karshen shi.
"Ina na saba zuwa?"
"Bance Kar ki fita ba?"
"I also make it clear kowa yayi harkan shi" ta fada hade da karasa hawa stairs in. Kaman Wanda aka ingizo a zuciye ya bita saman. Tana ajiye veil inta da bag ya bugo kofan. A tsorace ta ke kallon shi ganin yanda idanuwan shi su ka rikida su kayi ja. Ganin gadan gadan yayi yo ya kanta ya sa ta fara ja da baya. Daman da gaske ya ke bai iya fushi ba? Wuf yayi ya cafko ta kafin ta samu Daman ba wa kanta amsan tmbyn da ta ma kanta.
Kafada ya rike da duk hannun "za ki fada min inda kika tsaya ko kuwa?"
Wai! Zo ka meema, idanuwa sun ciciko da hawaye ta zaro su rudu rudu ga kirjin ta sai bugawa yake. Nema ta ke ta kwace kanta Amma ko motsin arziki ta kasa.
"Zaki Fada min ko kuwa"
Da sauri tace "gab da magrib mu ka fito meetings shi ne na tsaya gidan Anty Ummi nayi Sallah"
Shiru yayi yana tuno tabbas ya San Anty Ummin, cousin in Daddy ce. Gidan ta na kusa da ma'aikatar ne.
"I can ask her"
"You can, please ka sake Ni am tired" ta bashi amsa, gabadaya jikin ta wani iri ta keji. Gashi Daman yau ba karamin gajiya tayi ba. Wuni tayi tana aiki rabon ta da abinci ko tun breakfast in da ta dan tsakura gashi shi kuma ya zo ya Mata wannan rikon.
Sassauta rikon yayi yace "Amma ban ce Miki Kar ki fita ba?"
Shiru tayi bata bashi amsa ba fuskan ta a yamutse kaman Wanda za ta fashe da kuka.
"Wato ki nuna min ban isa ba ko? Then let me show you who is in control. Gobe ba za ki kara ba"
Ko kafin tace wani abu ya fara kokarin wulli da kayan jikin ta. Ganin tana kokarin ture shine ya sa ya sake ta yace "okay Fight me in kina tunanin kin fini karfi ne" kaman jira ta ke ta fara ture shi daga kan gadon. Ganin ko motsi bai yi yasa ta fara dukkan arms in shi da dukkan karfin ta Amma ko gezau gashi gabadaya ta gama exhausting sauran energy inta. Gajiya tayi ta kwanta kan gadon hade da sakin kuka mai karfi. Shi ko opportunity in yayi using ya gama seducing inta gabadaya jikin ta yayi weak ko daga hannu da kyar ta ke ga shi she is feeling him everywhere on her body. Hakanan ta hakura ta bada Kai bori ya hau. One thing is for sure he didn't rape her nor force her instead ya San dai ba tayi reciprocating ba due to the weakness but she allowed him access.
Wani irin baccin Wahala ne ya kwashe ta bayan ya kyale ta. Jawo ta yayi jikin shi ya Mata bargo yana jin yanda ta ke ajiyan zuciya da kaji kasan na gajiya ne. Yanda jikin ya dau zafi da wuya in ba ta tashi da zazzabi ba ma. aikin da ta ke daurawa kanta yafi karfin ta Amma ya San abinda zai yi.
Sai wurin 3 na dare ta farka. Yana ganin ta bude idanu ya cincibeta yayi bayi da ita bayan ya hada ruwan zafi. Sai da ya tabbatar she will be okay sannan ya barta tayi wanka. Yana shafa'i sannan ta samu tayi Sallan isha'i.
Da ta gama ne ya ja su Sallah ya samu yayi musu addu'oi da aka umurce dukkan musulmi yi bayan yayi sabon aure. Komawa tayi ta kwanta shi ko kasa baccin yayi ya cigaba da azkar kawai. Sai da ya dawo Sallan asuba sannan ya tashe ta tayi. Bai yi wani bacci ba ya sauka kasa. Around 7:30 ya dawo falon saman ya zauna yana jiran yaga fitowan ta. Ilai kuwa fitowa tayi cikin shiga na wacce ke Shirin fita.Kallon ta yayi ya saki murmushi yanda ta ke yi da fuskan ta kaman mara gsky yasa ya tabbatar da taurin Kai a al'amarin ta. "Zo Nan" ya fada hade da daura kafa daya kan daya. Kaman ba zata ta zo ba sai kuma ta taho a hankali. Gefen shi ya nuna Mata ta zauna, ba musu ta zauna tana kallon kasa.
"Cutie ba gaisuwa" kallon gefen ido ta mai "Ina kwana"
Riko hannuwan ta yayi yana wasa da tafin hannun ta yace "wa yace Miki haka ake gaida miji?" Jawo ta jikin shi yayi hugging inta sannan yayi peckish goshin ta da lips inta. "Don't be a Village girl daga yau haka za ki dinga gaida mijinki"
Ba ta amsa shi ba haka kumaba ta dago daga kirjin shi ba.
"Ina zaki?" Ya fada bayan ya dago ta don yana son kallon idanuwan ta.
"Office"
Girgiza Kai yayi yace "You are not going" ganin yanda tayi rau rau da idanun ta yasa yace "ba Wai na hana ki zuwa gabadaya bane Amma not today infact throughout this week ma ba inda zaki"
"Please"
"Don't" ya saurin fada "ban son musu meema. Now ki fada min me za kici in hada Miki kinsan ke amarya ce. Ki je ki kwanta ke wai ba kiji jikin da zafi ma? Ba ki tsoron zazzabi ne ya rufe ki"
"Shiyasa na ke son fitan in na kwanta zai rufe ni"
"Aa stress ne so just rest a little. I will get you medicine. Mai za ki ci?"
"Komai ma" nodding yayi sannan ya tashi ya riko hannun ta sai da ya kaita daki sannan ya sauka kasa.
Golden Yam ya soya da farfesun kayan ciki sannan yayi frying egg ya daura ruwan zafi. Har daki ya same ta da breakfast in ya sa ta sauko su kaci abincin tare. Kusan gabadaya ma a baki ya bata.
"Ko zamuje asibiti ne?" girgiza Kai tayi tace "am feeling better kaman yanda ka fada gajiyan ne." Nodding yayi sannan yace "bara in Kai kayan nan kasa In dawo, Kar ki kwanta fa Ina zuwa"
Tana zaune tana jiran shi. Shi ko da ya je kasan kayan gabadaya ya hada ya wanke tas. Sannan ya tattare kitchen in. Ya mugun jinjina wa mata, ashe aikin nasu ba Wai sauki bane dashi har haka.
Da ya koma a zaune ya same ta sa system a gaba. Hararan ta yayi "au aikin kike daga zaune kenan koh? To a bari ban so" dan jim tayi sannan ta kashe system in ta ajiye a gefe. Kana ganin fuskan ta kasan gabadaya ta saduda. Ko dan gani ta ke kaman yanzu aikin gama ya riga da ya gama. Bayan hakan ma yanzu har wani irin shakkan shi ta ke yi da nauyi. Sai ta tsinci kanta da mamakin yanda da har ya ke hana ta abu ta mai gardama ta kiyi. Duniya kenan juyi juyi.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...