Babi na ashirin da bakwai ( 27 )

904 83 2
                                    

Kafin Mukhtar yayi wani yunkuri sai labari ne ya isko shi Asmaun ta tafi Zaria makaranta. Hakika yaji zafin kin sanar mai da tayi amma yanzu wannan mai sauki ne tukun. Abubuwa duk sun cakude mai ga shi har an tsaida ranar da za a zo tambayan na ta. Dan takaici ko iya kiranta bai kara yi ba bayan ya ta kira ta ki dagawa. Gabadaya ya rasa ta ina zai fara ga matsalan Ummi ga nata shiyasa yaji haushi ya share ta. Bai samu Karin takaici ba sai da maneman auren na ta za su zo musamman Ummi ta tura shi Daura ya tarbe da kanshi ya kai su Family house in baban Asmau in da za a nemi auren ta gun yayan babanta.

Alh Usman Bindawa, mahaifin Asmau Dan Asalin karamar hukumar Bindawa ne da ke katsinan. Sai dai Gabadaya yan gidansu girma da tashin Daura ne. Mahaifiyar tashi ma bafulatanar Daura ce. Sai dai tun suna kanana suna yawan ziyartar bindawan kasancewar dangin mahaifin su gabadaya na can. Da ke wurin yayan shi za a Neman auren shiyasa aka nufi Dauran kai tsaye amma yan uwan shi na bindawa ma sun hallara duk a cikin Dauran.

Da safiyar ranar Mukhtar ya isa Dauran. Kai tsaye Family house in ya isa da ke duk sun riga da sun San shi kaman dan gida ne. Gaisawa sosai su kayi da Kawu Abdallah Wanda shi ya kasance waliyyin Asmaun. Hira su ka fara yi sosai bayan an gabatar mishi da fura. "Kai kuma mukhtari ai na dauka kai ke neman diyan tawa sai naji sabanin haka" ji yayi gabadaya wuta ta dauke mai a lokacin. Murmushin karfin hali ya cigaba dashi kafin kawun ya cigaba da magana "ai nan ma'un su ka zo tare da mahaifin ta da za ta wuce maakaranta na ke tambayan ta. Ta tabbatar min da bakomai tsakanin Ku, ni da farko ma ban yarda da ita gani nake boye min za ta yi sai daga bays tukun" wani irin kulun bakin ciki ya ji ya taso mai nan ta ke yaji furar ya fita daga ranshi na bakin nashi ma daci yaji yana mai da kyar ya hadiye sannan ya kora da ruwa. Kawun ne ya cigaba da cewa "bakomai ai duk daya ne sai dai naso a ce kai ne. Allah dai ya tabbatar da alkhairi" yake Mukhtar ya dinga yi. Daga nan kau hirar ta tsaya. Lokacin ya tafi dauko maneman auren su ka karaso gidan. A gaban shi aka yi komai, sai dai gani ya ke kaman a mafarki abun ke faruwa. Ba tare da sallama ba ya fita ya shiga motan shi ya fara tuki. Anya Asmau na son shi kuwa? Tambayar da ya ta wa kanshi kenan. Koma dai miye dole ya fuskance ta ta tabbatar mishi da abinda ta fadawa kakan ta. A ganin shi is an opportunity da ta kwabar musu dukkan su biyun. Ba tare da wani tunani ba ya dau hanyar Kano daga Daura. Za mu iya cewa ikon Allah ne ya kai Mukhtar Zaria a ranar, wayar shi kawai ya dauko ya tura mata text.

I need to see you.
Currently in Zaria.
~Mk.

Kasancewar ranar Asabar tana gun meema suna hira tana nuna mata wani chemistry da aka musu lectures week in da ya mata wuya. Tana ganin mssg in shi reaction in ta ya canja ta daina fahimtar abinda meeman ke nuna mata. Gane hakan da meeman ta yi ne yasa ta tmby ta

"ya ya dai Asmau wani abu ya faru ne?"
Girgiza kai Asmau tayi a sanyaye. "Ko dai fargaban auren ne aka fara tun yanzu?" Ta fada hade da kashe mata ido.

Kakalo murmushi Asmau tayi hade da tabe baki "ina fa Ya MK ne wai yana son gani na yana Zaria"

"Anya Asmau ba kusa kika wa yayana ba" mikewa tayi hade da son canja zancen. "Bara na shiga wanka kafin ya karaso"

Text ya turo mata da ya karaso samarun.

Ina zan same ki?
~MK.

Kai tsaye ta tura mishi address in apartment in da meeman ta ke. Cikin 10 minutes ya iso wurin. Nan in ma text ya tura mata cewar ya iso.

Idanuwan shi na kanta tunda ta fito daga gidan har ta karaso, sai dai ita ba ta iya ganin shi saboda tent glass in dake motar shi. Material bubu gown ke jikin shi fari da sky blue sai black veil da tayi wrapping dashi. Kayan sun amshe ta sosai, a lokacin Mk ji yake kaman ya sace ta su gudu kawai kowa ya huta. Meema na bayan ta said da ta zo su ka gaisa da Mukhtar in su ka dan taba hira wannan ta koma ciki. Tana tsaye a waje yana kallon ta ta gefen ido. Kusan minti biyar su kayi a haka sannan ya daure ya ce mata "shigo mana" tana shiga ya tada motan ba tare da wata maganan ba.

Cikin makarantar ya shiga da ita ta area da ba mutane sosai ya samu yayi parking. "Na miki wani abu ne?" Abinda ya fara fitowa bakin shi kenan bayan ya tsaida motan. Girgiza kanta tayi "to meyesa kike min haka? Na kira ki kin ki dauka, na turo miki texts kin share, kin taho makaranta ba ki sanar min ba sannan kuma kin yi denying ina a gaban magabatan ki, don't you think that's its an opportunity to us? Ina tunanin ki ya tafi, Asmau anya kina sona kuwa kina tausayi na, abinda kika yi kinsman za a iya kiran shi da rashin imani..."

"Dakata!" Ta fada da sauri cikin fushi da tunzura "ni za ka kira da mara imani? An gaya maka kai kadai ke jin abinda kake ji ne? Ko an gaya maka ni ba mutum bace banda zuciya? Kasan halin da na shiga cikin yan kwanakin nan? Ko an gaya maka da ina da mafita bazan bita ba nima din?" Sai a lokacin ya karewa jikin ta kallo, tabbas ba ko tantama ta fada kuma ba ta kuzari "I can't be selfish that's it. Umar bai yi deserving haka daga wurin ba haka ma Ummi" harara ya bi ta dashi yace "what a lame excuse!" Ya fada karfi dai dai da sakin kukanta.

Cike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Kuma kin cuci kanki. Ina kike so in saka raina. Ba ki min adalci ba ba kuma kiwa kanki ba" ita kam kuka ta ke wiwi da kyar ta ke iya magana "Kayi hakuri Ya Mukhtar ba zan iya ba" share hawayen fuskan ta tayi da handky in da ya miko mata tace "Zan yi hakuri in zauna da Ya Umar, zan dawo da soyayyan shi cikin raina. Kai ma kuma zan maka addu'a Allah ya baka wacce ta fini..." Hararan ta yayi sannan ya ja tsaki mai karfi. Sannan ya fisge motan har sai da ta bugu, ko kallon ta bai yi ba balle kuma batun hakuri. Ita ma ta ji kadan daga abinda ya ke ji. Bakin titin da zai mai da ta gidan meeman ya tsaya cikin tsawa yace mata "Get out of my car" ba bakin musa ganin yanda gabadaya ya canja sai huci ya ke. Ita kam iya rayuwar ta ba ta taba ganin ya fusa ta irin haka ba. Jiki na rawa ta bude ta fita. Ya fige motan hade da badeta da kura. Tsoron ta days gudun da ya ke shararawa kar ya ja mishi accident.

Sai da ya dau hanyan kano sannan yayi parking gefe. Kife kanshi yayi kan sitiyari ya samu ya fitar da numfashi mai zafi. Addu'a ya dinga yi cikin ranshi sannan ya samu natsuwa. Ya fi mintuna 20 a wurin kafin ya cigaba da tuki. A ranar ya koma katsina cike da bakin ciki da takaici. Yana kallon kiran Asmau sai ma cillar da wayan yayi ya kwanta ba wai dan zan iya baccin ba.

Author note: Dukkaninku naga sakonin Ku kuma nima INA godiya da kauna da soyayyar da kuke nuna wa rubutu na. I have to update again for the love you have shown me. You guys really motivates. Unbelievable! One of you give an idea without even knowing... Wacce ta yi comment ta ce akwai cakwakiya tsakanin Umar da Mukhtar da Asmau kanta. Do you know that you just give an idea of my next chapter? The answer is No. I will love if you all continue like this, it really helpful. Nagode sosai, Allah ya bar kauna.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now