Babi na hamsin da biyu ( 52 )

984 98 5
                                    

  Sallama yayi a falon gidan su. Ba kowa sai su Salim, suraj da Suleiman da ke zaune suna buga game. Sunan ganin shi su ka washe baki suna mishi sannu da zuwa.

Murmushi ya musu yana mai farin cikin yanda gidan nasu ya kimtsu cikin kankanin lokaci. Lallai Abbah yayi namijin kokari.

"Ina mami?" Tana falon ta su ka bashi amsa.

Can ya nufa sai dai maimakon Mami Suhaila ya iske tana kokarin kunna burner. Kusan a tare gaban su ya buga Amma sai kowa yayi kokarin basarwa da ke yan miskilancin na Kai. "Ina wuni" kawai tace mishi ya amsa da lfy ya nemi wuri ya zauna. A kanshi ya ke kirga kusan wata daya kenan rabon shi da ita.

"Dan yi Mami magana" ya fada yana danna wayan shi. Kala bata ce ba ta shiga wurin mamin su ka dawo tare.tana jin mamin na tmbyn shi "Aa Muhsin har kazo Ina ka baro Rahman da jiki"

Fita tayi daga falon gabadaya ta nufi dakin ta.

Maganan Yusuf Mami ta ke wa Muhsin akan Yarinyar da ya kawo zai aure Sam ba ta Mata ba saboda ba ta da tarbiyya ga rashin kamun Kai. Shi dai Muhsin ba ki ya dinga ba ta yana mamakin yau mamin ke kushe wata haka Wanda a da ta dauki hakan a matsayin wayewa. Maganan kadai da take dashi ya is ma tabbatar mishi an samu canji la'akari da da banda fada ba abinda ya ke shiga tsakanin su.

"Yanzu ma yana wata hudu bai zo ba Ina ga ya yi auren gsky ni hankalina bai kwanta ba. Kayi wa Dan uwanka magana Muhsin"

"Kiyi hakuri Mami, aiki ne ke masa yawa shiyasa Amma ai yana neman transfer zuwa Kaduna"

"Haka dai yace, tun yaushe mai yasa bai canja ba"

Murmushi Muhsin yayi yace "Mami fa ke ma kinsan long process ne. Kina fa aikin gwamnatin nan"

"Tou Allah ya sauwake. Rahman dai lfy kalau ko?"

"Eh Mami Dan yau ma har ta fita gidan Yayar ta. Mami ba abinci a gidan ne?"

"Banda abinka Muhsin mai Mata ana mishi tayin abinci ne?" Dariya yayi yace "ni na ce kar tayi don dukkan mu wurin 11 mu ka fita gidan."

"To ai shknn bara na Kira Suhaila na San ba a rasa a kitchen ba" saurin mikewa yayi yace "barta kawai Mami i will serve myself"

Kitchen in ya nufa ya ko samu abincin. A Nan dining table in kitchen in ya zauna. Spoons daya ya Kai ya San cewa ita tayi girkin. Duk da cewa training in Mami ne itan in Amma ya kware wurin banbance abincin su.

Yana cikin cin abincin ta shigo kitchen. Mamakin ganin shi tayi a kitchen in Amma sai ta basar ta karasa wurin gas cooker tana kokarin daura ruwan shayi wanda kacokam shi ya taso daga dakin saboda sanyin da ake yi.

Tana tsaye har shayin ya tafasa ta tace ta juye a flask. Shi ko ya gama cin abincin yana zaune yana danna waya. Ba Wanda yace wa dan'uwan shi kanzil.

Tana gamawa ta dauki flask in da cup da spoon tana kokarin barin kitchen in "Rowa dai ba kyau" ya fada Amma ya fuske kaman ba shi yayi maganan ba.

Dawo tayi da baya tana fadin "sorry ban San za ka Sha bane"
Mug ta dauka ta tsiyaya mishi sannan ta ajiye kan table in.

Kallon ta yayi yace "sai da na roka? Kuma kinsan wannan ya min yawa"

Without saying anything ta dauki mug in ta rage ta maido mishi.

"Teaspoon" ya fadi Kai tsaye.

Ita Sam manta tayi, daukowa tayi ta dauraye ta sa a ciki.

"Kiyi tasting kiji in sugar is normal" zuwa yanzu abin ya fara daure Mata Kai. Ko sai ya dauka da rahma ya ke magana ne?

Yanda yace tayin sannan tace "I think its okay"

"Okay dauko min Ginger in sachet da lemon a fridge"

Ajiyar zuciya tayi sannan ta je ta kawo mai. "Zuba min mana" ya kara fadi. Zubawan tayi sannan ta nufi hanyar fita.

"Dawo ki zauna a Nan, ba a Nan kike shan shayi ba?" Girgiza Kai tayi tace "Ina abu a dakin ne"

"Okay yanzu ban ma isa in sa ki abu kiyi ba kenan kin daina daukan magana ta" shiru tayi tana mamakin Wai shin me ke damun shi ne. "Am i not talking?"

"Ni na isa" ta fada hade da dawo ta zauna.

"Aikin San Abba ma ya hana cin abinci a daki" kala ba tace ba. Ta zuba tana Sha. Da ke kadan ta zuba Nan da Nan ta gama da sauri ta tashi ta fita. Wurin Mami ta wuce.

Ba ta dade da shiga falon mamin ba ya biyo ta a baya. "Mami bara na je zamuyi magana da Yusuf"

"To shknn Muhsin, ka gaida Rahama da jiki. Ni Wai tsaya Muhsin ko dai karuwa za mu samu ne" murmushi yayi hade da sosai Kai zai yi magana Mami ta wuf tace "Lallai Muhsin nice ma surukar ta ka kenan, Toh Allah sa albarka"

"Ameen mami" ita dai Suhaila haka kurum ta ke jin wani iri. Ba ta San meyesa ta ke kishin Rahma ba don har wani sarawa ta ji kanta na Mata.

"Za ka je wani wuri ne?"

"Da wani abu ne Mami?"

"Daman Zoo road na ke son a amso min dinki so ba kowa a gida. Abba duk ya gudu da drivers in shi. Suraj kuma ya hana shi tuki"

"Ba matsala Mami bara na amso Miki"

"To kuje da Suhaila ita tasan shagon"

"To" ya fada hade da fita. Ba don suhailan na so ba ta tafi ta shirya. Ta samu har ya fita da mota waje. Yana hango ta ya bude kofan motan. Ita dai kanta a kasa har ta karasa ta shiga motan.

Suna barin layin ya dan kalle ta yace "Ko kin tmby jikin Mata na" ba tare da ta dago ba ta amsa "na kirata na gaishe ta"

"Allah ya soki Amma still baki min murna zan samu karuwa ba"

"Allah ya sauke ta lfy"

"Ameen"

"Mai kike so a sa Mata ko shi?"

"Ban iya shishigi ba ask the mother"

"Thank you tunda family Ina ne su ka zama shishigi a gare ki" kallon shi za tayi magana ta kasa. Taga alamun da bala'i so ya ke sai ya tsokano ta sun yi fada ita kuma she is not in the mood.

Shagon su ka fara zuwa ta amso dinkin. Yana jin wata da ta rako ta na tmbyn ta "Suhaila wancan ne zaki aura"
"Aa brother na ne " ta bata amsa sannan ta shiga motan.

Maimakon su nufi gida ta ga yayi parking a ShopRite. "Mu je ki raka ni shopping" ya fada yana bude motan. Dole ta fita ta bishi. Yana ta kwaso abubuwa da alamun stuffs in gidan shi ne.

"Muhsin" ta ji wani na Kiran shi. Yana ganin da murmushin ya bashi hannu su ka gaisa. Sun dan yi magana kafin ya gaisa da Suhaila yace "Muhsin wannan ce Amaryan?"

Kallon fuskan ta Muhsin yayi da alamun reaction ya ke son gani. Ganin yanda ta sunkuyar da Kai tana kallon wani abu yasa yace "The second dai"

"Ah haba Dan Allah Muhsin Kai fa ustaz ne"

"Sai kuma aka ce shi Ustaz kar yayi aure ko?"

"Wai na ga its early Amma serious ma you look alike" yanda ya ke maganan ya ga Suhaila na duba abubuwa duk a tunanin abokin ba ta ji shi ko Muhsin ya sani sarai tana ji.

"Kagani tun yanzu ma kenan" dariya yayi ya Musu sallama ya wuce.

Da su ka koma mota kasa shiru tayi tace "Ya Muhsin why do you lied to him? In yaje yana fada fa"

Shrugging shoulders in shi yayi yace "and who tell you i care. Infact what if am not lying. Its of benefits ma tunda gashi you finally talk"

"If you don't care i do Daman nasan you don't ai"

Kallon ta yayi yace "don't misunderstand me please. Infact me na Miki kike ta shan kamshi, are we fighting ne?"

Girgiza Kai tayi tace "am doing what you want me to"

"Kar ki min sharri"

"Daman i wanted to tell you. Mahmud yace yana so ya zo yaga Abbah on Friday i don't know if you will help me tell him" sake baki yayi yana kallon ta. Nan da nan ya hade rai sannan ya fisgi motan da gudu a kofar gidan yayi parking hade da mika Mata wani leda. "What for?" Bai tsaya amsa ta ba ya ja motar ya barta a wurin. Murmushi tayi tana fadin "habawa na fika iya duniyan ci"

ABINDA KAKE SOजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें