A hankali Najib ke Kara warkewa sai da yayi three weeks a katsina kafin ya koma kaduna bakin aikin shi. Kasa zama a tsohon gidan shi yayi ya koma gidan su faisal saboda ganin komai ya wuce. Daga baya ma Saida gidan yayi ya siya fila ya tada wani ginin da Faisal ya zana ya mishi tsarin komai da komai.
2 months later
Katsina
Manya manyan gidan Baffah na gani zaune a falon shi, da dukkan alamu meeting su ke yi saboda yanda na ga kowa na tofa albarkacin bakin shi. Yayin da mutane dayawa su ka yanda da shawaran da aka tsaida. Alh Abdulrahman malumfashi mahaifin su Muhsin ne ya Fara magana "Baffah ban tari numfashin ku ba Amma zai fi kyau a ce an Fara tambayan yaran Nan an ji ta bakin su kafin a gama zartar da hukunci saboda kar azo ayi Abu ba dadi azo ana samun matsala" murmushi baffah yayi sannan ya kalli Abban "Banda a binka wannan ai aikin ku ne sai kusa iyayen su Mata su ji ra'ayoyin nasu Ina ga hakan zai fi" kowa ya amince da shawaran kafin aka rufe taro da addu'a. Kowa da fara'a a fuskan shi ya fito falon da alamun dukkan su hukuncin ya musu.
A tsaye ta ke a bakin titi tana faman neman napep in da zai sauke ta unguwan su Goruba road. Har ta tsaida napep in ta ji horn a bayan ta, tana juya su kayi four eyes da MK Yana ta faman jera Mata horn. A tare su ka sakar wa juna murmushi ya Mata alaman ta Zo ta shiga. Da hannu ta Mai alaman ta Riga ta tari Mai napep, da idon shi ya Mata alaman ta sallame shi da dukkan alamu suna jin dadin yaren kuraman nasu. Ganin haka Mai napep in yace "hajiya bara kawai in tafi tunda na ga alamun ana jiranki" ko kafin ta amsa shi ya tada mashin in shi ya Kara gaba. Motan ta nufa ko kafin ta Isa har ya bude Mata passenger seat in. Sai da ta shiga sannan ta gaishe ya amsa. "Ina zuwa?"
"Gida" ta amsa
"Shine ko sallama babu ko?" Shiru tayi Yana jin haka ya gane dalili "Hala fada kuka yi da Fadila" shiru tayi don haka ya tabbatar da zargin nashi ganin irin kallon da ya ke jefan ta dashi ya sa tayi saurin bude Baki "Ya Mk ba haka bane"
"Hey don't lie to me I know you more than you know yourself" tsit tayi jin abinda yace.
"Kin fadawa Ummi?"
"Ba ta gida Amma nace mata Zan tafi dama"
"Me ya sa har yanzu ba za ku daina fada ba, you guys are matured fa yanzu haba"
"Ya MK ita ke ja fa"
"Common shut up ita ma haka za ta ce" tsit tayi Bata Kara magana ba har ya gama fadan shi sai can tace "Wai Ya Mukhtar yaushe za ka koma Florida" rage gudun motan shi yayi sannan ya Dan juyo Yana facing inta "kina so in tafi ne" girgiza kanta tayi innocently "kawai na ga ba ka ce ka dawo gabadaya bane Kuma ka Dade a gida"
"Zan koma sai nayi aure Amma tunda ke kin ki ki bini" da sauri ta juyo tana kallon shi "yauwa Ya MK remember kace za ka nuna min pic in girlfriend inka Kuma za ka fada min sunan ta"
"Ina sane na dauka baki son sani ne Kuma"
"Kaiiii Ina so sosai ma"
"Then sai ran da kika dawo daga gida"
"Mu koma na fasa tafiyan ma"
"Kin Isa bayan mun iso unguwan" magiya ta dinga mishi yayi Banza da ita daga karshe ta Bata rai har su ka Isa bakin gidan ta fita. Har cikin gida ya bita su ka gaisa da mama Aysha da sauran Yan uwanta sannan ya tafi.
Da dare Yana zaune cikin dakin shi ya samu kanshi da kiranta. Suna zaune da kanwar ta Maijidda tana jiran Umar ya Kira ta as usual call in nashi ya shigo. Kaman ba za ta dauko ba sai Kuma ta kasa. "Hello" ta fadi a hankali.
"Asmauuu" ya Kira a hankali daga ita har shi sai da su kayi feeling yanda ya Kira sunan.
"Naam" ta amsa

YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...