Tana Isa dakin su ita da Fadila ta tarar da wayan ta na ta faman ringing Bata daga ba har sai da ya katse sannan ta duba ta ga 5 missed calls from Umar, yanzu haka ji take kaman ta ci amanar shi don haka ta tura wayan gefe ta cigaba da kukanta a hakan har Fadila ta shigo ta same ta. Zaro ido tayi tana kallon ta cike da mamaki, if she can remember ce Mata tayi ta tafi hira wurin Ya Mukhtar ita Kuma ta wuce falo kallo. "Asmau lfy? Why are you crying? Meya same ki? Ki min magana please" ba abinda Asmau ta ce Mata illa kukan da ta ke ta faman yi "Haba Asmeey miye haka Wai wani Abu ya faru ne? Ko ke da Umar ne Naga ya Kira ni Wai in baki" girgiza Mata Kai kawai ta yi. Haka Fadila ta yi yin duniya Asmau ta fada Mata me ke damun ta taki illa iyaka ta sanar Mata ba abinda ya samu kowa daga karshe Fadila cewa tayi zata fadawa Ummi Nan dai Asmaun tace ma ta kar ta fada za ta bar kukan, bayi ta je ta wanko fuskan ta ta dawo kan gado tana ta ajiyar zuciya Fadila kuluwa tayi ta kyale ta, ita dai Asmau kasa bacci tayi ranar sai juye juye ta ke tana tuna abinda ya Mukhtar ke nufi hade da jimami, what does that mean? Me ye sa Ya Mukhtar zai ce yana son ta why her? Ai ko Dan Ya Umar bai kyauta ba abinda ya Mata.
Washegari, tana tashi da kyar ta jira breakfast tace wa Ummi za ta tafi gida, Ummin ta dauka fada su kayi da Fadila ganin yanda Asmau ke acting weirdly Amma ta tabbatar ma ta ba wani matsala. Ba ta wani ci abinci kirki ba ta gudu gidan su duk don gudun haduwa da MK. Ita dai Fadila ta kulu sosai a cewarta da ita ne ba za ta iya boyewa Asmaun me ke damun ta ba. Shiru shiru MK yaji Bata kawo mishi breakfast kaman yanda ta Saba don Haka yayi dialling numban ta switch up Nan ta ke ya Kira Fadila ya ce ta turo mishi ita ta fada mishi ta wuce gida a Dole ya sa Fadilan kawo mishi ruwan tea kawai don bai da appetite.
Asmau dai haka ta wuni ranar sukuku har wani zazzabi zazzabi ta dinga ji daga karshe ma kashe wayan ta tayi da Ya Umar ya ishe ta da Kira, ita ko Fadila da taga ya kirata ya tambaye ta Asmaun saboda ya Kira ta a kashe sai tayi tunanin dashi ne su ka Samu matsala. Mukhtar ma haka ya wuni ranar ko lekowa daga side in shi bai yi ba Banda Sallah ba a abinda ya tsinana a ranar shi dai gashi Nan ne kawai. Asmau ko tana samun labarin mamanta za ta bikin Yar kawarta a Daura ta nace sai ta bita domin yanda ta ke gani in ba garin ta bari ba akwai matsala.
Kano
Yau Asabar Mami ta yi tafiya domin dubo iyayen ta a gombe, abin mamakin shi ne yanda ta ke iya barin Suhaila cikin maza ita daya ko a jikin ta, shin ba ta tsoro wani abu ne? Barin ma irin masu halin Yusuf na gidan gashi yawancin kullum da Abokanan shi su ke Wuni gidan.
Zaune su ke a falo suna kallo though dai rabin shi hira ne, mutuniyar ko wando ne three quarter a jikin ta sai wani Dan karamin riga Mai hannun vest da kadan ya dan rufe Mata cibi, gashin ko ya zubo baya an dan kama shi da karamin ribbon. Yusuf ma sanye yake da three quarter in sai shirt in su na maza da Abokanan shi biyu a Fallon daya da doguwan jallabiya daya Kuma da shirt and boxers kawai, yawanci ma a gidan su ke kwana ita ko ko a jikin ta tayi zaman ta suna Hira da su Suraj, saleem da sabir.
"Baby kin lura kuwa" Yusuf ya fada Yana kashe Mata ido hade da nuna Mata kayan shi da nata.
"Kin gani munyi anko" tabe baki tayi hade da kallon shi ta gefen ido "Ya Y Kai Kuma matsalan ka kenan ni wlh yunwa na ke ji"
Saleem ne yayi saurin sako Baki "Yeah Wlh Nima Wai who is supposed to cook today"
"Suhaila Mana Kai ma kasan halin ta bayi za tayi ba Kuma Amma mu mun iya yi taci" Suraj ya fada Yana hararan ta ko kallon shi ba ta yi ba illa iyaka chocolate cake in da Ameer ya Miko Mata ta amsa ta Fara ci. Ameer shi ne shirt and boxers in daya daga cikin abokan Ya Y ne tuni ta gane abinda ya ke nufi Amma Ina ita a ganin ta tafi class in shi besides ma he is Casanova.
Dai dai wurin Muhsin ya shigo falon, kallon su yayi daya bayan daya sannan ya sauke idon shi akan Suhaila, harara ya aika Mata ta ko dauke Kai sannan ta tashi a hankali ta nufi dakin ta domin ba ta bukatar jarabar shi ta San halin shi yanzu zai Fara Mata nasiha ko ma yace zai Kai Mata hannu ita ko ba zata ta dauki embarrassment ma barin ma a gaban abokan sadiq, haba no ta fi karfin Nan, lokaci kawai ta ke ba Muhsin don in yazo wlh shi ko kallo bai ishe ta ba balle Kuma yayi tunanin sa Mata ido, its obvious shi ba class in ta bane Dan dai kawai Allah ya hada su gida daya ne.
Tsaki Muhsin ya ja sannan ya nufi cikin falon ya jawo hannun Sabir da alama yunwa ta gama cinye shi su ka nufi kitchen Yana jin Yusuf na Kiran "Bro please ka sa abincin da ni" kala ba ce Mai ba ya nufi kitchen in. Sai da ya dawo bayan Sallan la'asar ya aika Saleem ya Kira mishi Suhaila. Sukuku ta biyo shi har zuwa inda Muhsin in ke zaune a falon Abba, bakan riga ne a jikin ta wannan karon don Bata son matsala. Tana zuwa ta samu wuri ta zauna, Tayi five minutes tana jiran yace wani abu Amma yayi Banza da ita ganin haka yasa ta Fara kokarin mikewa za ta tafi "Keh, Ina Zaki ba Kiran ki nayi ba?" A hankali ta juyo da niyyan fada mishi magana sai dai sun hada ido ta ji want kwarjinin shi ya cika mata ido komawa tayi ta zauna sannan tace "Ina jinka"
"Abba bai fada miki ki hada kayan ki ki tafi gidan Baffa bane" shiru ta yi kaman ba za tayi magan ba sai can tace "Ya fada min I don't like it there ne""Saboda ba Kya sakewa ki yi abinda kike so a can ko?"da sauri ta dago ido tana kallon shi ai ko ido hudu su kayi Yana binta da wani kallon kiyaya kururu sauri dauke idanuwan ta tayi sannan tace "ina son in wuce" harara ya zabga Mata "Bismillah" ba kunya ta tashi za ta wuce "in baki dawo ba sai na balla Miki kafa" sukuku ta dawo ta zauna tana jin want irin zafi a ran ta "Wai shin Muhsin in Nan da me yake takama ne Amma ai Mami zata dawo zai sani" ta fada a zuciyan ta. "Ke baki jin tsoron Allah ne? Wait, kin ma San Allah n kuwa? Ba kunya ji yanda kike Zama cikin maza wadanda ba muharamman ki bane, jikin ki duk a bude a ganin ki burgewa ne? Kina zubawar wa kanki da mutunci kina tunanin wayewa ne Koh? Tou na rantse da Allah ki tattara kayan ki ki bar gidan Nan yanzu ba anjima ba, in kina ganin kinfi karfin kowa ai baki fi Abba ba Koh? Zanje gidan Baffan Anjima kar in same ki a can ki gani" tashi yayi ya bar Mata falon ta Kai minti goma a wurin sannan ta Mike, ba ta San meyesa Muhsin ke mata katsalanda a rayuwa ba Kuma ta ke kyaleshi, shi din me? Wadanda su ka fishia ta taka su ta zauna lfy Amma shi yazo ya sa ta a gaba, Yana dai cin darajan wani dalili nata ne ta ke kyaleshi Amma soon za ta yi maganin shi sai ta mishi abinda ko kallonta ba zai Kara marmarin yi ba. A Dole ta tafi gidan Baffan, ba Wai Bata son Anty nata bane matar babanta As sai dai ba ta da sakewa kaman Mami Abu kadan ta Fara Mata fada ko wa'azi ita Kuma ba iya tolerating za tayi ba gwara ma kar taje a samu matsala saboda haka yaran gidan gabadaya ba su son zuwa ko Ina in ba gidan su ba ko katsina su kaje ko gombe an dinga musu fada kenan da sunyi Abu kadan ba su Kuma ba su Saba ba domin ba haka Mami ta tafiyar da su ba kenan.
Ko da ta Isa gidan a dardare ta gaida Anty nata ba ta wani Dade ta nufi dakin da ta ke Zama in tazo gidan, kallo ta Fara yi abin ta don ko ba zata fito ba a Raina Mata wayau Baffah ya Zo ya mata fada, ita ko a ganin ta ta wuce wannan phase in, karfe 8:00 pm ta fito daga dakin da wani fitted gown in plain material a jikin sai veil in da tayi dauri dashi ba ta wa kowa magana ba ta fita already Daman wata friend inta Fatima na jiran ta a waje suka luluka shagalinsu.
Ba ta dade da isowa ba Muhsin ya iso gidan, ko da ya tambaye ta a sanar mishi ta fita Nan ta ke ya Fara dialling numban ta yayi ta ringing ba ta dauka ba. A takaice dai ba ita ta koma gidan ba sai 11:00 pm. Ko Ina su kaje? Oho.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...