Ko da ta tashi daga baccin maimakon taji dama dama sai ji tayi abin gabadaya yayi worst ne. Kirjin ya Mata nauyi gashi ya hade da baya. Ganin ta na Shan wuya sosai kuma ba zata iya mikewa ba yasa tayi kokarin jawo waya ta Kira Mami Amma har ya gama ringing ba a dauka ba. Haka tayi ta fama ba mai kawo dauki sai da Mami ta fito daga meeting ta ga missed calls inta. Da sauri ta Kira ta back Amma ba ta dauka ba. Suraj ta Kira akan yaje ya dubo suhailan, aiko yana zuwa ya iske ta tana ta mutsutsu. Da sauri ya Kira mamin ya fada Mata "Mami ko mu tafi asibiti ne? Tana fa jin jiki sosai"
"Aa bara in kira Muhsin" ta fadi.
Yana cikin asibiti suna round da student in shi da aka kawo asibitin ya ga Kiran Mami. Da sauri ya dauka. "Muhsin please kaje gida ka duba min Suhaila ba ta jin Dadi sosai, in ma za ku wuce asibiti ne Nima gani Nan dawowa gidan"
"Tou shknn Mami" ya amsa Mata. Jiki na rawa ya hada dukkan abinda zai bukata ya nufi gidan. Ganin ba kowa a falon ya sa ya nufi dakin ta. Ya samu tana kan gado tana ta fama rawan dari shi ko Suraj ya sa ta a gaba sai sannu ya ke Mata.
Fita yayi ya Kira house help in gidan da ya ga ta shigo lokacin. "Please ki taimaka ma Suhaila ku je falon Mami" da sauri ta nufi dakin bayan ya kira Suraj ya fito. Kayan jikin ta ta taimaka Mata ta canja tukunna ta dago ta suka nufi falon.
"Sannu" ya fada yana kallon ta gabadaya jikin shi yayi sanyi ganin yanayin da ta ke ciki.
"Kina jin zazzabi ne?"
Nodding Kai kawai ta mishi yace "akwai ciwon Kai?"
"Ehmm"
"Da mai kuma?"
Kirjin ta taba da hannu. Idon shi ne ya fada kan dayan hannun ta da ke kan mara.
Da bakin shi yayi pointing yace "is it also paining you?"
Nodding Kai tayi ta sunkuyar da Kai kasa.
"Are you on your period?" Kaman daga sama taji question in. Nodding tayi kawai a hankali.
"Kinyi breakfast?" Girgiza Kai tayi. Juyawa yayi yace "Please get her something to eat Amma yanzu hado Mata tea tukunna please" da sauri ya tashi ya nufi kitchen in.
"Yaushe ya fara"
"Jiya kafin in kwanta"
Bag in da ya so dashi ya bude ya dauko syringe, wool swap, spirit da tourniquet. "I will need some of your blood" hannun ta ta Miko mai ya daure tourniquet in. Tana kallon shi har ya nemo vein In ya goga spirit da cotton wool sannan yayi drawing blood in. Runtse ido tayi har sai da ya gama.
Lokacin Suraj ya shigo da tea in. Mika Mata yayi ta amsa. Sa that a gaba yayi sai da ta shanye. Yana Shirin Mata allura Mami ta shigo.
Bayan sun gaisa ne ta ma suhailan sannu ta kalli Muhsin "ba test kake Mata allura?"
"Its for Emergency Mami. Tana jin jiki ba a bar ta har sai results ya fito ba"
Bottle in urine ya fiddo ya mika wa mamin. "Yauwa Mami in ta Dan warware ya kamata aje asibiti ayi tests because Ina suspecting infection"
"Toh" kawai ta ce mishi.
Fita yayi ya koma asibitin. Ita ko yana fita ta samu bacci. Har ya dawo da results in baccin ta ke.
"Mami typhoid ne so na hado Mata allurori na jijiya na San baza ta Sha drugs ba"
Kura mishi idanu Mami tayi tana mamakin Wai yanzu Muhsin ke considering abinda suhaila ta ke so. Duniya kenan juyi juyi. "Kai ma ka fara biye matan kenan?" Murmushi yayi hade da so sa keya yace "tou Mami ya za ayi"
Dariya tayi tace "Muhsin kenan, Thank God you can stop blaming me now" dariya kawai yayi yace "tou Mami in ta tashi ki sa ta taci abinci Ni zan tafi sai anjima zan zo Mata allura" maganin ruwa na ulcer ya fiddo yace "ta dinga Shan wannan shi Ina ganin ba zai ba ta wani matsala ba"
Kullum allura biyu ya ke Mata a rana a jijiya. Yawancin yana gamawa ya ke tafiya, Alluran da ya ke Mata shi yake kara taso da ciwon so yawanci ba ta iya wani magana because she is weak. Ranar da zai Mata na karshe ne ya zo ya iske ta tana breakfast a parlor, ita kadai ce a gidan. Gaishe shi tayi ya amsa yana tmbyn ta jikin na ta.
"Na warke" murmushi yayi yace "okay Alhmdlh, now can you tell me damuwan mai na ke gani kullum kwance a fuskanki? Am very sure bana ciwo bane"
Dan yake tayi tace "Ni kuma? I have nothing to worry about"
"No na fa sanki Suhaila. May be dai you don't want to share ne kawai"
Kallon shi tayi sai tayi tunanin kauda zancen tace "Kai ma kaman da magana a bakin ka ai abinda na karanta kenan"
Siririn murmushi ya saki yace "kaman kin sani na kosa ki warke in fada Miki kuwa"
Kallon shi tayi alamun tana sauraron shi yanzu "yace its a deal in na fada Miki kema zaki fada min" nodding kawai tayi without any thinking.
"Ina so zan kara aure" duk yanda ta so boye halin da ta tsinci kanta abin ya faskara domin karara ya ke hango damuwa a fuskan ta. Gabadaya jikin ta taji maganan ya ratsa sannan ya sauka a tsakiyan kanta.
"Aure kuma Ya Muhsin?" Ta fadi a hankali kaman mai tsoron magana. Nodding kawai ya Mata tace "is it not early?"
"Not when i desperately need to be with the lady" bata San lokacin da ta tabe baki tana fadin "Allah ya sa albarka" dariya ta so bashi Amma sai ya daure yace "Ameen, Nagode. Now tell me yours"
"Ai na San ka ma sani. Mami ne tace min Abbah zai turo wani ya zo wurina"
Shiru yayi yana nazarin fuskan ta "Ba ki so ne?"
Girgiza Kai tayi "i don't even know him. Ni ko waye i already accepted because am done with relationship"
"Ba za ayi haka ba. In har za ki aure shi ya kamata ki bashi dama ki San waye ne sannan ku fahimci juna" shiru tayi ranta na zafin yanda har ya zauna ya na bata shawaran abinda za tayi ma wani. Yanzu ta tabbatar Muhsin bai son ta tunda har aure zai kara. Amma abin mamakin shine duk da hakan hira dashi yana sa ta samu natsuwa.
Ganin alaman ba ta sauraren shi yasa yayi shiru. Zuba Mata idanuwa yayi yana kallon reaction inta.
"Wa za ka aura?" Ta fadi ba tare da ankara da irin kallon da ya ke aika ma ta ba.
"Suhaila" ya fada still idanuwan shin na kanta, wani irin kallo ya ke aika ma ta kaman Wanda ke jin bacci. Gabadaya ji tayi ta tsargu ta kasa fahimtan Kiran sunan ta da yayi. Shin amsa ya bata ko kuma Kiran sunan ta ya ke.
"Ban sani ba if you can marry me" dum! Gaban ta ya buga, ware idanu tayi tana kallon shi jin ya tabbatar ma ta da rudanin da ta shiga. Abu ne da ta dade tana nema Amma yauwa da ya zamanto gaske ta rasa me ta ke ji gabadaya. Farin ciki ko akasin shi? Ita dai abu daya ta sani kawai a yanzu, she is shock.
Ya fuskanci halin da ta shiga don haka bai yi kokarin kara Mata wani magana ba. Abubuwan shi ya hau hada wa yace "I need to go back to work" ba dai tace komai ba, a sace ta ke kallon shi har ya je bakin kofa. Kaman zai bude sai ya fasa ya jingina bayan shi a jikin kofan.
"Suhaila" ya Kira sunan ta. Dagowa tayi tana kallon shi don har ga Allah har ta fara tunanin tsokanan ta ya ke kawai.
Murmushi ya sakan Mata yace "okay, am tired hakanan ina ga zan kawo karshen komai yau kawai ko zuciya will be at ease"
in a confused expression ta ke kallon shi. "Kin San Ina sonki Suhaila" saurin dauke idanuwan ta daga kanshi tayi ta mai da kasa tana jin kirjin ta ya Mata nauyi. Kwakwalwarta ta ka sa tantance abinda ya ke fada mata statement ne ko kuma tmby.
"I mean what am saying ki dago kanki muyi magana" kasa dagowan tayi gabadaya sai dai tayi attempting.
Shrugging shoulders in shi yayi yace "Whatever in ma baki sani in ba am telling you now. Ina son ki sosai" shiru ya danyi kafin yace "i can't claim knowing your interest about this even though i acknowledge all the signs. So i need to hear your opinion about it please, Zan dawo mu yi magana. Sai anjima" bai kara cewa komai ba ya bude kofan parlon ya fita ya barta a wurin kaman statue.
KAMU SEDANG MEMBACA
ABINDA KAKE SO
RomansaCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...