Kwance ta ke a rigingine Kan gado fuskan ta na Kallon silin yayi da hankalin ta gabadaya Yana ga wakan hausan da ta ke saurare.Da gudu Asmau ta shiga dakin tana kwala Mata Kira "Fadeela Fadeela" Sai dai Kash ko dago kanta ba tayi sakammakon ear piece in da ke makale a kunne ta tsaki taja sannan ta fisge ear piece in kunnen nata. Abinda kake so shi ke wahalar da Kai, in da Kuma ka samu sai ka Tana dai... na so kaina na biye wa zuciya. wakan da ta ji Yana tashi a wayan kenan. girgiza Kai ta yi cike da tausayin Yar uwarta ta kafin ta kalle ta. "Fadee its high time you move on please shi fa so ba a mishi dole ka nayi ne da Wanda ya San mahimmancinta" shiru tayi tana tunanin abinda zata fada Mata next "Ya Najib sun rabu da matar sa Saki Uku" kwalalo ido tayi tana kallon Asmau cike da mamaki Nan da Nan ta ji na ta damuwan ya kau. "Daman duk irin son da Ya Najib ke ma Anty Sumayya zai iya rabuwa da ita?" Girgiza Kai tayi cike da takaici. "Yaushe abin ya faru?"
"Wai fa Yau three days ba wanda yaji lbr sai yau da Anty meena taje gidan Mimi tace su zo su je su ganshi tunda shi ba zai Zo inda su ke ba. To ma fa sanadiyyar fitowan lbrn kenan."Ikon Allah toh me ya hada su?" Shiru Asmau ta Mata sanin ba ta da amsan ta sai can take tanka "he refused to talk about it"
"Tabdi Allah ya kyauta, aure har da yara biyu Abu bai yi dadi ba"
Haka dai ko ta Ina aka cika da jimami. Duk da halin ta an ji abin ba dadi Barin Kuma yara sun hada ai an riga an zama daya.
•••
Sati daya da faruwan abin Ya Najib in yazo katsina a dalilin Kiran da baba Kabeer ya mishi bisa umurnin Baffah.
Yana isa side in Hajjah yayi sallah yaci abinci kafin ya Isa a parlourn Baffahn domin Yana da tabbacin baba Kabeer in na can tunda ya San da isowar sa.
Kamar kullum Yana zaune kan kujera da jarida a hannun sa dayan hannun Kuma da carbi a hannun sa. Tsoho Mai ran karfe kenan ka ganshi zaka rantse bai Kai shekarun shi ba, a tsaye yake kyam don wani saurayin ma ba zai nuna Mai karfi ba tun Yana tasowa bai wasa da motsa jiki har ko zuwa yanzu bai daina, gashi duk Abubuwan da suke Kara lafiya da ingarman jiki sune cimanshi. Faram faram ya amsa wa Najib gaisuwan shi kafin baba Kabeer ya iso. "An iso lfy Malam Najib?" Baba Kabeer ya tambaya bayan sun gama gaisawa" Kai a kasa ya amsa gabadaya yayi Baki ya rame sai ya basu tausayi ma, duk fadan da baba Kabeer ya yi niyyan mai kasawa yayi saboda a iya sanin shi ba karamin Abu bane zai sa Najib haka, mutum Mai fara'a da raha kullum ka ganshi da murmushi akan fuskan shi, tabbas mace ta gari ita ce mutum. Basu nemi jin ba'asin abinda ya raba su ba sai dai sun Mai fadan saki ukun da yayi lokaci daya Nan ya ke shaida musu ba wannan ne na farko ba sun Sha yi wannan ne dai na karshen ya rabu su gabadaya. Nasiha su ka Mai sosai akan hakuri da mace sannan su Kai fatan Allah ya bashi wacce ta fita ya Kuma raya Mai yaran shi.
Tare da Mukhtar su ka shiga wurin Ummi da dare. Suna falo suna Hira. Kaman kullum da murmushi kwance akan fuskar shi ya gaida Ummi sai dai fara'ar tashi ta yau tafi kama Dana karfin Hali. Su Asmau su ka gaishe shi ya amsa faran faran har da tsokanar Fadeela "Yar gidana ko a Aiko min abinci ko? Ko yanzu an daina yi Dani ne?" Girgiza Kai kawai ta yi sannan su ka bar falon ganin Alamun Suna bukatar kebewa da Ummi. Nasiha ita ma ummin ta Mai sosai sannan ta bashi shawaran fawwala wa Allah komai domin da ka ganshi ka San damuwa har ta Mai yawa, shi dai da toh kawai ya ke bin su amma shi kadai ya San irin abinda ya ke ji a zuciyan shi. A gidan ya kwana dakin Mukhtar ko zai dan rage kadaici wani abin ya ragu.
Sai dai me? Tun cikin daren Mukhtar ya fahimci da zazzabi ya kwana da ya tambaye shi me ke damun shi yace babu sai da Asuba ya Zo tada shi sannan ya ji jikin shi zafi rau haka ya tashe shi, da kyar su ka yi alwala su ka wuce masallaci shi ma da taimakon Mukhtar. Jiri na diban shi haka ya kabbara sallahn. Ana idarwa ya taso za su wuce jiri ya kwashe shi yayi kasa Allah ya so Mukhtar ya ankara ya riko shi sai dai gabadaya bai cikin hayyacin shi Nan take ya Suma. Saukin ma masallacin kofan gidan Baffah ne don haka straight ka sa shi a mota sai asibitin Dr Kabeer Dara.
Ba shi ya farfado ba sai after 24 hours gabadaya yayi wani iri ya fada kaman bashi ba. Ba ehm ba Aa ga gabadaya dangi sun taru akanshi sai sannu su ke Mai sai ma da Doctors in su ka Dan tsawatar sannan su ka ragu. Hatta mahaifin shi da ke fushi dashi sai da ya Zo Katsinan dubo shi tare da Muhsin da Suhaila. Da kyar aka Samu ya Dan Sha tea. Ummi da Hajjah ne ke kanshi sai ko Suhaila da ta ki yadda ta tafi. Duk da rashin kulawan ta akan komai tana ji da Yayan ta kwalli daya tak wato Ya Najib, ba Wai ta Kira shi a waya ba ko ta je gidan shi haka matan shi kwata kwata Bata shiga harkanta Amma ba ta son jin want Abu ya taba lafiyan shi yaran shi Kam kaman ta hadiye su don soyayya, musamman ta ke siyan abubuwa ta aika musu, uwar ko godiya ba tayi ko. Tare aka tura su gida donin hado abinci ita da su Asmau Amma fir taki zuwa tace ita xata zauna wurin shi gani ta ke kaman zai tafi ya barta yanda mahaifiyar su tayi. Ba ta kuka a fili Amma zuciyan ta tafasa ya ke ta gwammace ta bar shi a boye akan ya fito fili a gane weakness inta. Ita dai tayi zuruzuru da idanu tana kallon shi kawai, dole su Asmau su ka wuce su ka barta domin sun fahimci situation in da ta ke ciki.
Fadila na zaune a daki sai faman kuka ta ke Asmau ta sa ta a gaba tun tana rarrashi har ta gaji ta daina. Ba za tace ga takamaiman abinda ke damun ta ba, shin ciwon Yaya Najib ne ko Kuma ASLAM?
Tsaki Asmau ta ja da ta gaji da jin kukan ta, Fadila is so emotional Abu kadan ke taba zuciyan ta sai kaji tana kuka wholeheartedly. "In Kinga dama ki tashi mu koma asibitin kin San ana jiran mu, tunda dai kukan ki ba bashi lafiya zai ba in ma Kuma ba shine asalin dalilin ba to duk ma dai ke kika sani.
Kala Fadila ba ta ce Mata ba ta bita su ka koma asibitin. Yana a kwance ba ehm ba Aa, idanuwan shi na sama Yana kallon silin a yayinda hawaye Mai zafi ke bulla da idon shi. Ba wanda ya tanka balle ya ji nasihan da suke Mai to make matter worst har yanzu ba wanda ya fadawa Mai Sumayyan taa mishi Amma ga duk alamun A sanadiyyar ta ne ya shiga wannan halin. Yin duniya an yi yaci abinci ya ki har doctors sun yi ta magana Amma ina.
Sai ta Suhaila ta ga kowa ya bar dakin sannan ta matsa kusa dashi ta jawo hannun shi ta sa a nata. A hankali ya dago Yana kallon ta, duk da halin da yake ciki he is in shock for a bit. Suhaila never shown her concern about everything. "Ya Najibbbb" ta Kira a hankali still idon shi na kanta ta Nan ta gane Yana sauraron ta. "Ka Sha fada min yanda Anty mommy ke son ka da irin maganganun da ta ke maka a kaina tun Ina ciki, ka fada min cewa ta na yawan maka fada akan zumunci da hakuri da kauda Kai sannan da fawwala wa Allah komai. Ya Najib a ganin ka yanzu ka kyauta ma ta kenan ko za taji dadin halin da ka sa kanka a ciki. Ba Zan gan laifin ka a auren Anty Sumayya domin rabo ne ya rantse a tsakanin ku Amma yanzu haka halin da ka sa kanka bai kamata ba Ya Najib, Mai yiwuwa rabon ne ya Kare a tsakanin ku ko ma dai akwai a can gaba Allah ne mafi sani. Sai ka gode mishi a duk halin da ka tsinci kanka Amma right now halin da ka sa kanka bai dace ba kwata kwata Kai kanka ka sani. Jikina ya bani Anty mommy ba ta jin dadin halin da kake ciki Ya Najib I can feel it. I never talk about her but she run through my veins Ya Najib ban taba sanin ta in ba Labarin ta da nake ji ba mostly a wurinka. In Ina kallon ka ya ina yawan tunawa da ita har in Mata addu'a sosai. Yaya Najib please i don't want to loose you also Dan Allah you should let it go and move on... You have a life ahead probably better than the previous one." Murmushi yayi sosai Yana kallon ta, sai ka rantse Suhaila Bata magana Amma in tayi she said something reasonable and she talks maturedly "you don't want Anty mommy to be mad with you right?" Nodding kan shi yayi a hankali Yana kallon ta. Sosai ta ke kama da mahaifiyar su, da yanayin su komai na Suhaila na mahaifiyar su ce har ko da sunan. Yanzu haka Najib ji yake kaman mahaifiyar tashi CE gaban shi, he can't believe his baby sister grow matured like this. Smiling ya Mata sosai sannan yayi nodding kan shi in approval. "Za ka ci abinci" murmushin kawai ya Kara Mata Nan da Nan ta jawo abinci ta hada. Ita tayi feeding in shi har ya gama ci. Duk da bai ci sosai ba she is satisfied.
Muhsin da ke window Yana jinsu ya girgiza shi cike da bakin ciki. That is one of the things he likes about Suhaila. Amma sai dai kash akwai gyara a rayuwan ta sosai, he just hope yanda Ta wa Najib maganan Nan har ya sauko ya saurareta ita ma in aka mata za ta ji. Amma kullum abin ta da su Yusuf is getting worst.
Kowa yayi mamakin saukowan Najib but sun gode wa Allah sosai. Kwana Uku ya Kara yi a asibitin su kayi discharging in shi tare da bashi shawaran rage tunani da kadaici and Alhmdlh ya Fara dawo wa kaman da sai dai yayi Baki sosai ya rame kaman bashi ba.
Duk yan'uwan sai da su kazo duba shi. Areef ko har yanzu Yana hannun Uwar shi ta ki bada shi su ma ko ba wanda ya Kara bi ta kanta.
Finger crossed, toes crossed we are moving on to the next level. Expects more of me In Sha Allah. The story have just began!
BINABASA MO ANG
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...