Babi na talatin da hudu ( 34 )

920 97 4
                                    

Kaduna, Nigeria.

Wasa wasa karamin ciwo na so ya zamo babba. Tun daga ranar Fadila kusan kullum sai ta ji jirin nan kuma duk lokacin da ya zo mata sai ta zauna da Yan mintuna tukunna ya sarara. Najib kwata kwata bai cika zama ba a kwanakin saboda wani aiki da su keyi, yau shine Lagos gobe Abuja, portharcourt, Adamawa haka dai ta kasance.

Monday, yaran sun tafi school ita kuma tunda ta gama exams ta ke gida. Tsaye ta ke a tsakar gidan tana faman shanyan kayan yaran da ta wanke a washing machine. Wani irin jiri ne ya kwashe ta ba shiri ta yi kasa saukin abin karfen shanyen da ta rike ne. nan ta ke ba kuma sai ta ji kirjin ta ya rike ba ta kasa fidda numfashi, nan da nan idanun ta su kayi ja tana faman neman mafita. Sama sama ta ke jin muryan mutum a kanta daga nan kuma ba ta kara fahimtan komai ba.

Dawowan Zahra kenan daga kasuwa ita da sister in ta a mota tace ta sauke ta zata dubo Fadila tunowan da tayi tun ranar da suka rabu ba ta jin Dadi. Suman tsaye tayi ganin yanda ta iske fadilan, da kyar ta tattaro dukkan natsuwan ta jiki na rawa ta danno namban Antyn ta tana fadin "please help me kizo gidan da na shiga its urgent." Jin yanayin muryan kanwan na ta kadai ya tabbatar mata da ba lafiya. A guje ta shiga gidan ta iske abinda ke faruwa, ita ce tayi karfin halin yayyafa wa Fadila ruwa, da ke doctor nan da nan ta sa aka kawo mata first aid kit inta ta Mata emergency treatment zahran na taimaka mata. Sannan fa su ka nufi asibitin da ta ke aiki, gwaje gwaje aka hau yi mata inda aka gano blood pressure in ta ne yayi low sosai.  Nan ta ke aka sa mata drips hade da allurori ta samu bacci sai a sannan su ka fara tunanin gayawa mijin ta.

A gajiye likis Najib ya iso kaduna straight ya nufi gidan shi. Ga mamakin shi yana ta sallama bai ji an amsa ba, sai da ya karasa ciki sannan ya tabbatar Fadilan ba ta gida ga kuma wayan ta a nan falo. Karar horn in mota ne ya katse mishi tunanin ina fadilan, ga mamakin shi sumayya ce da kanta ta kawo su Arif. Sama sama su ka gaisa sannan ta fara gaya mishi "an maida pumpkins a kace min ba kowa a gidan shine nace dai bara in zo da kaina inji lafiya? Daman su kadai ke zama a gidan ne?"

"Ya za ayi su zauna a gida su kadai? Am also wondering ina ta shiga nima ga kuma phone in ta a gida"

Tabe sumayya tayi tace "this shows that this is not the first time Najib, ka fa san ni ban San ana min wasa da rayuwar Yara. In ba zai yiwu ba i will just pack their belongings and go with them"

Da sauri yace mata "No, Fadila is not that careless nasan akasi aka samu but i will warn her because i don't want it to happen again, tasan ba zan yi tolerating ba ai"

"Whatever, kasan Wanda bai San ciwon da ba ba zai taba treating insu right ba" harara ya bita dashi sannan yace ma ta "its okay please sumayya, ke da kika San ciwon su me ye sa ba ki hakura kin zauna dasu ba?"

Ba tare da wani gargada ba ta kalle shi tace "I have to save my own life, I mean i have a life to live and enjoy ba zan iya tauye shi ba" ba wani takaici ne gabadaya ya mamaye shi. He thought sumayya ta canja ganin yanda kwana biyu su ka dan daidai ta har ta ke ce mishi she will get married for some months and get back to him ko Dan saboda yaran da ke tsakanin su tunda ta fahimci ba mai iya kula da yaran ta kaman ita kanta. Abinda Najib ya kasa fahimta shine sumayya kokari ta ke at any cost ta bata image in Fadila wurin Najib gabadaya, domin a ganin ta cin amana ne gabadaya dangin Najib su ka hadu su ka mata da kuma tozarci, to tabbas ita ma fa sai ta rama.

Mota ta shiga ta fiddo IV a hannun tana mika mishi "I hope you will be there?" Kallon yake yana kara kallon IV in da ke hannun shi. Sunan ta ya gani a jiki da kuma sunan wani babban ambassadorn Nigeria da ke kasan Canada. Tabbas yanzu ya kara tabbatar wa kanshi Sumayya kudi ta ke wa bakomai Dan ya San banda kudi ba fa abinda zai sa ta auren mutumin. Zufa ya share mai zafi yace mata "all the best" shakiyin murmushi ta saki sannan ta ce "as you can see, I have enough money to sponsor my children if she can't do it zan zo na dauki kaya na." Da sauri ya dakatar da ita da tafin hanun shi "Ya isa Sumayya, naji please" murmushi ta yi sannan ta ja motan ta ta bar shi a nan tsaye.

Wani irin matsanan ci hali Najib ya shiga. Wannan wani irin soyayya ce? Shiyasan har abada ba zai taba iya manta Sumayya ba, ta riga ta mishi illa. Yaran su kadai ya gani sai ya tuno ta barin ma Ilham da komai na ta ta dauka. Sai dai kuma ya sa wa zuciyar shi salama, ya fita daga rayuwar ta. Tsabagen tunanin da ya shiga bai ji Kiran da ke ta shigowa wayan shi ba. Da kyar ya gabatar da sallah domin bai iya fita ba ganin yaran ne kadai a gida. Har aka idar da isha'i shiru bai ga Fadila ba sai lokacin ya fara tunanin shin ina ta je?

Sai karfe 8:30 na dare ta farfado, Dr Safiyya yayar Zahra ta sa ta ci abinci sannan ta gabatar da salloli ganin ta warware tace wa Zahra ta kamo ta kawai su tafi gida. Rungumo tayi har mota sannan su ka tafi gidan. Sai da Safiyya ta kira mijin ta Engr Usman su ka hadu a kofan gidan Fadilan sannan su ka shiga. Najib na zaune a falo ya ga an riko Fadilan an shigo da ita. Da mamaki ya ke binsu da kallo, Engr Usman in kadai ya iya ganewa saboda suna gaisawa a masallaci.

Sai bayan ta zauna sannan Engr in ya warware masa halin da ake ciki sannan ya kara da sanar mishi sun ta kiran shi bai daga call in ba. Sai a time in ya duba ya ga missed calls in. Sannu Najib ya Mata ta daga Kai kawai yawa Engr in godiya sannan ya tmby shi halin da ake ciki a yanzu. Nan kuma Dr Safiyya ce ta warware mishi komai ta kara da fadin "am sorry to intrude but Dan Allah a daina barin ta ita kadai because she is at risk sosai musamman ma saboda abinda ke cikin ta" ganin reaction in Najib in yasa Dr Safiyya murmushi tace "sorry i didn't mention that she is a month pregnant, i thought you are aware. So please cikin bai riga da yayi kwari ba you need to be very cautious, i will be checking on her also" fara'a sosai Najib yayi sannan ya musu godiya. Ko da ya bukaci jin fee in asibitin dagewa Dr Safiyya ta yi akan ya bar shi kawai domin a matsayin kanwa ta dauki Fadila har ta na kwantan tawa da Zahra.

Har gate ya taka musu yana mai kara musu godiya sannan ya dawo wurin Fadilan ya na mata sannu. Lokacin su Arif sun riga da sun yi bacci ita ma kuma ta Sha magani kafin su baro asibiti, wanka kawai tayi ta bi lafiyan gado.

Cikin yan kwana biyun nan zamu iya cewa Fadila ta dan ga canji daga gun Najib sosai domin ko yana kokarin taimaka mata. In ya fita kullum Zahra na shigo mata, har sunyi sabo sosai don zahran akan za ta koma Gombe ne gidan su bayan Exams in su Amma fir ta ki tace sai Fadila ta warke. Dr Safiyya kullum sai ta shigo ta duba ta har sau biyu haka Anty meena ma ta na zuwa daga gidan su Faisal ma haka. Don da maman Faisal in so tayi ma a kawo mata Fadilan sai ta warware tukunna, baban ne yace ta bar ta kawai tunda tana da doctor in da ke zuwa duba ta.

Ranar da Yan ABU su ka fara gama Exams Najib ya ma su Asmau magana akan su su Dan zauna da yar uwar ta su saboda akwai tafiya da ya taso mai gadan gadan. Lokacin Suhaila ce kadai ta gama sa ke ita faculty of social sciences ta ke yawanci suna riga gamawa. Duk da ba Wai tana son zuwa bane hakanan ta hau shiri tayi kadunan domin kuwa duk tabarancin ta banda Najib a ciki. Ran da ta je bai riga da ya wuce ba sun Sha hira da Dan uwan na ta sosai. Fadila har mamaki tayi domin ba tayi tunanin Shirin na su ya Kai har nan ba.

ABINDA KAKE SOKde žijí příběhy. Začni objevovat