Babi na hamsin da bakwai ( 57 )

1.1K 100 11
                                    

Zaune su ke a falon Abbahn suna hiran siyasa da kuma halin da kasan ta ke ciki. A hankali su ka gangaro wurin Yusuf. "Toh Alhmdlh Abbah Yusuf yace min ya samu transfer in zai dawo Kaduna sannan kuma Allah ya amshi addu'anku ya samu matar da zai aura banda waccan da Mami taki.

Murmushi Abbah yayi yace "Toh mun gode Allah. Waccan in banda Mami ku ba shi zai zauna da abin shi ba"

"Eh toh akwai kamshin gsky cikin hujojin Mamin. Kuma wannan in yar Nan Kano ce, kanwar Abokina in Nan Kabir ne Wanda mu kayi service tare. Ba laifi Abbah na yaba da tarbiyyan gidan su"

"Toh ma Sha Allahu, an tsaida magana"

"Eh Abbah sun ce ya turo iyayen su shine yace Toh in maka magana"

"Toh shknn zan Kira Baffanin ka muyi magana in an sa rana sai na fada maka"

"Tou shknn Abbah" Dan Sosa Kai yayi kaman yana son magana Amma sai yayi shiru.

Shakuwar da ke tsakanin Muhsin da mahaifin shi ya samo asali ne tun yana karami. Hakan ya sa duk wani motsi nashi mahaifin ya gama fahimta. Kaman abokai haka su ke zama suyi hira.

"Muhsin akwai magana ne?"

Nodding kan shi yayi yace "Eh Abbah da ma zan tmby ka ne shin Wai yaushe za ku aurar da Suhaila ne?" Kallon shi Abban yayi kaman yana son ya karanci wani abu yace "To banda abinka Muhsin yau Suhaila ta fiddo da miji mai zai hana mu aurar da ita? Son samu ma a hada da na Yusuf in kawai kowa ya huta. Akwai Wanda ka sani yana neman ta ne kuma ka amince dashi?"

Girgiza Kai yayi ya sunkuyar da kanshi kasa yana neman ta inda zai fara maganan.

"Muhsin wannan noke noken fa? Ko dai Kai ke so ne?" Dagowa yayi ya kallin Abbahn sannan yace "hakane Abbah"

"Shine kake boye min? Bayan kasan ba wannan tsakanin mu. Sai dai muhsin ba ka ganni yayi kusa ka kara aure, Kar ka jawo rigima a gidan ka tun yanzu."

"Abbah mun riga mun gama magana da Rahma"

"To Amma kana ganin za ka iya da halin Suhailan? Kusan zan iya cewa ka fini sanin ta Muhsin"

"Abbah Ina son Suhaila so duk halin da ta ke da ba zai hana Ni auran ta balle ma yanzu da nake da tabbacin akwai canji mai yawa daga gurin ta."

"Nima na fuskan ci hakan kuma Ina da tabbacin da sa hannun ka a ciki. Muhsin na dade Ina son inyi hadin Nan Amma sai na zabi in ba wa kowannen ku zabi. Tun farko na so a ce kaine mijin ta saboda irin su Suhaila suna bukatan mutum irin ku. Amma duk da haka dole na bata zabin ta don haka kaje ka nemi amincewan ta tukunna. Allah ya sa albarka"

Godiya yayi ma Abbahn sannan ya Kiran Yusuf ya sanar mishi yanda su kayi da Abbahn. Cike da farin ciki su kayi sallama. Yana farin ciki yanda shigowan Fatima rayuwan Yusuf in gabadaya ya canja. Abinda su ka gagara yi ita tayi shi cikin kankanin lokacin.

.....

Tunda ta gama girkin ta shiga daki ta ke jin wani zazzabi mai hade da ciwon Kai na son kama ta. Basarwa ta cigaba da al'amarin ta domin a tunanin in har ta kwanta to tabbas ciwon ne zai rufeta ruf sanin yawancin in za ta fara period inta haka ya ke Mata. Ba karamin wuya ta ke Sha ba.
Kallo ta ke a system sanda taji sallaman Mami na shigowa dakin ta. Da mamaki ta dago tana kallon mami. Gaban ta taji ya fada because its very rare Mami ta shigo dakin ta. In ko ta shigo always akwai magana mai mahimmanci da za ta fada mata.

"Kallon naki kike yi koh?" Murmushi tayi tace "Mami banda abun yi ne Allah"

"To ajiye muyi magana" kashe system in tayi gabadaya tayi focusing attention inta wurin Mami. Slowly ta matsa kusa da mamin ta daura kanta kan cinyan Mami. Dariya mamin tayi tace "Oh ni Suhaila in kika yi auren ya za ayi kenan" shiru tayi tana nazarin yanda Mami tace auren ba aure ba. Kenan sun yi magana akan auren ta Kenan?

"Mami auren zaku min?"

"Ai gatan ko wacce yarinya kenan Suhaila. Abbah ya aiko Ni yace in sanar Miki an zo an same shi ana neman izinin auren ki. Shi kuma ya turo shi wurin ki domin yace ba zai Miki auren dole ba dole sai da yardar. In ku daidai ta shknn. Yace in ce Miki yaron ne mai hankali da natsuwa matukar ku ka daidai ta zai so a ce shine ya kasance miji a gareki"

Da kyar ta iya danne hawayen da taji yana son zubo ma ta. Kenan abinda Ya Muhsin ya fadawa Mahmud gsky ne kenan? Gaban ta taji ya fadi. Shin ita Wai ya za tayi da ranta ne? Shknn za ta jure ta amincewa ko ma wanene Abbah ya turo mata kawai.

Jin shirun ta yayi yawa yasa mamin magana "Why are you silent Suhaila? Ko akwai Wanda kuka daidai ta ne?"

Girgiza Kai tayi tace "Aa Mami, ki cewa Abbahn na amince kawai ba ma said an turo shi wuri na ba tunda har shi Abbahn ya aminta dashi" Tausayi Mami taki ta bata. Ta kara tabbatar wa kanta Suhaila ta canja, ta yi hankali ba kaman da ba. Wai shin wani irin godiya za tayi wa Muhsin ne? Tabbas Muhsin baiwa ne a gare ta. Allah bai dubi halayen ta ba ya bata shi. Tana mai alfahari da kasancewar Muhsin da a gare ta. Abinda da ta kasa ganewa.

"Aa Suhaila ba za ayi haka ba. Ko sau daya ne kuyi magana dashi yana da kyau. Kar ki damu kinji. In Sha Allah alkhairi ne"

Kara shigewa tayi jikin mamin tana fadin "Mami ban son rabuwa da ke Allah"

"Toh banda abinki Suhaila wa isa ya raba ni da ke? Tabbas dole zan yi kewan ki sosai Amma ki sani aure ba za ta raba mu ba"

A karshe kuka ta sakan ma Mami sai da ta rarrashe ta tukun na ta bar dakin. Kasa komai tayi sai dimbin tunani da ta afka.

Abinci ma kasa fita tayi taci. Duk a tunanin Mami tunda ta ga abincin taci shiyasa ba ta mata magana ba. Zama tayi a daki ta rasa mai ke damun ta. Daga karshe kuka ta sa Wanda ita kanta ta rasa dalilin shi. A ganin ta halayen da ta dauka abun burgewa ne a da shi ya ke hunting inta duk da ta daina. Kukan ta tasha sosai har sai da ya saukan Mata ciwon Kai mai tsanani. Da kyar ta samu bacci ya kwashe ta Amma sai me? Tsakiyan dare ta farka a firgice, wani irin yunwa taji yana damun ta gabadaya ya rike Mata kirji. Bata da appetite in cin abinci hakan yasa ba tabi ta kan shi ba. Ai ko kirjin ya fada Mata kafin safiya don kasa koma wa bacci tayi ta tashi ta zauna tana fama.

To Daman tun tuni zazzabin ke son zuwa ga kuma kukan da tayi ya kara Mata ciwon Kai over sannan ga ciwon kirji abubuwa duk sun hade Mata. Da kyar ta samu ta je toilet ta kimtsa kanta ganin period in yazo. Wannan Karin ba karamin wuya ya Sha sai ta dangan ta hakan da ciwon kirjin da ya hade Mata.

Har Mami ta gama Shirin tafiya aiki ba taga fitowan suhailan ma. Dakin na ta ta nufa ga mamakin ta ta iske ta cikin bargo. Suhaila ba ma'abociyan baccin safe bace, its rare ka ganta tana yi saboda da wuri ta ke bacci da dare. Ko karatu tafi gane tayi da safe ko da Yamma Amma dare kam lokacin baccin ta ne.

Ganin yanda ta ke baccin ya sa Mami ta ayyana maybe kwana tayi tana kallon shiyasa ba ta farka ba. Kulle ma ta dakin tayi ta wuce wurin aiki kawai.

ABINDA KAKE SOTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon