Tun da safe su ka ga Suhaila ta hau hada kayan ta "lfy?" Meema ta bukata.
"Zaria zan koma"
"Me ya faru?"
"Bakomai akwai abinda zanyi ne"
"Dawa zaki tafi toh"
"Ya Yusuf zai kai ni"
"Allah ya kiyaye" meema ta fada cike da mamaki. Asmau dai kala ba ta ce ba don ta daina damuwa da harkan Suhaila gabadaya. Ita ba da ban Ummi tace ta tsaya ta ma Ya Mukhtar breakfast ba ai da yanzu haka ba ganin ta zata yi ba.
Breakfast ta shirya mai kyau dai dai na Mara lafiya ta hada da kunu, meema ta dan taya ta su ka hada. Da Baba Kabir su ka tafi don Ummi tuni ta wuce sai dai kuma abin mamaki da su kaje ba ta nan.
Umar yayi mamakin yanda Mukhtar yaci abincin sosai don sai anyi dagaske ya ke yadda yaci. Shi ma kam Abincin ya mai dadi, tuni ya fara tsokanan Asmau yana fadin "iyyeh ashe Amaryar nawa ta iya girka, Ashe zan more" daman tun can shi mutum ne mai raha da son nishadi. Unknown to him kara cusawa Mukhtar bakin ciki ya ke. Allah Allah ya ke a kauda zancen kafin wani abun ya same shi yanzun nan.
Ummi kam tana fita gidan mama Aisha ta nufa. Sun dan jima suna hira kafin ta gangaro kan abinda ya kawo ta. "Kiyi hakuri na San cewa kin fahimci akwai soyayya mai karfi tsakanin Mukhtar da Asmau" shiru tayi ba tace komai ba, ita ma daman Ummin ta San ba fadan za tayi ba.
Dalla dalla ta mata bayanin abinda ake ciki ta kara da fadin "Mukhtar in kusan shi ya ja komai da bai Sanar mata ba tuntuni har ya ja ta fara son dan uwansa. In har kin yadda dani ba zan cutar da Asmau ba don Allah ki barni in yi hukunci na a Kansu.
Murmushin alkunya mama tayi tace " Ai Mukhtar in ne abin ji, wannan irin ciwo"
"Shiyasa na zo nan muyi magana kenan, Mukhtar in sha Allah zai samu lfy, ban son tausayin shi ya rinjaye ki. In har kin yarda dani to ki min wannan alfarmar"
"To ni me zance daman Ummi? Allah ya zaban musu mafi alkhairi shi kuma Mukhtar Allah ya bashi lfy"
"Ameen, nagode"
Tare su ka tafi asibitin ga mamakin su har yafi jiya warwarewa sai hira su ke abinsu. Ummi na lura da yanda su ke Satan kallo da Asmaun.
Dr na shigo da mamaki ya bi Mukhtar da kallo "ma sha Allahu Lallai ka warke mukhtar, sai sallama ko? Ko in barka a nan?"
Da sauri mukhtar yayi saurin girgiza Kai "wlh na gaji, I needs to go home" murmusawa dukkan su su kayi sannan Dr in yace a bari zuwa anjima a ga yanayin jikin tukunna. Kira yayi daga lab aka debi jinin shi domin yin test a ga ya jikin.
Kwatsam su ka ga Yusuf ya shigo. Kallo mukhtar ya bishi dashi yana gaida su Ummi "kai bance maka kar kazo ba" harara ya aikawa mukhtar in yace "maganan ka zanbi ba ka da lfy in zan yi zamana?"
Murmushi Ummi tayi saboda ta san Amintar ka nasu tace "gsky dai Yusuf tun daga Florida ai yayi nisa"
"Bakomai Ummi mukhtar ne fa"
.....
Shin ina Fadila ne? A hankali ta ke fitowa daga lectures in da ba abinda ta fahimta a cikin ranar gabadaya. Satin ta hudu da aure amma za ta iya cewa a cikin sati hudun nan ta fuskanci abubuwa dayawa da ma'aurata ba su kai ga fara fuskan ta ba tukun.
Wuri ta samu ta zauna a gaban lecture theater in ta ba jin wani bakin ciki na turnike ta, A lokacin ta ji wani irin kewan Asmau na damun ta don tabbas da ta na kusa da ita abubuwa za su zo mata da sauki. Kullum za su yi waya amma ta kasa furta ma ta komai don ba ta so ta ji daga auren na ta har ta fara shiga matsaloli. Numban Ya Najib ta yi dialling ta na jiran ya dauka, bai dauka ba in har ya katse har ta fara tunanin tafiya ta hau napep ta wuce gidan ta ga call in shi na shigowa. "Hello sorry na barki ko? Na shigo school yanzun nan"
"Okay" kawai ta iya cewa.
Jigum ta yi tana ta kallo mutane kala kala na ta shawagi wasu na raha da annashuwa wasu kuma gasu nan ne kawai. Har lokacin ba ta da kawa guda daya Wanda su ke mu'amala kasancewarta mai wuyar sabo. Bayan mintuna kadan ta hango motan na shi, sai da ta jira yayi parking sannan ta karasa ta Shiga. Gaishe shi tayi hade da tambayan shi aiki shi ma ya tmby ta makaranta. Bayan wannan ba abinda ya kara shiga tsakanin su har su ka isa gida. Suna zuwa ya fita sallah, abinci ta fara niyyan daurawa kasancewar tana fashi ranar. Ta San ba zai dawo ba sai bayan Isha'i kusan 8:30 sannan za su dawo gabadaya da yaran ta San kuma za su nemi abinci. Abinda ke faruwa kenan tun bayan sati daya da auren su. A cikin sati dayan nan ta ga gatan rayuwa da kula gurin Ya Najib kaman zai hadiye ta duk da ba za ta iya cewa ya so ta a lokacin amma tabbas ya damu da al'amuran ta hakan ya kai ta ga fara fadawa tarkon shi ba tare da sanin shi ba.
Sati daya da auren su suna karyawa da safe wayan shi ta yi kara. Ta San bai picking call in har yana cin abinci to fa sai ya gama amma ranar yana ganin sunan da ke kan screen in jiki na rawa ya dauka.
"Lfy Sumayya wani abu ya faru ne?" Abinda ta ji ya fada kenan. Ba taji mai aka fada daga dayan bangaren ba ta dai ji yana fadin "tou shknn ba damuwa in sha Allah Anjima zan zo in dauke su"
Ba ta tmby shi komai shima kuma bai mata wani bayani ba ila iyaka da yamma ya shigo ma ta da Arif da sister in shi Ilham yana rungume da yarinyar a jikin shi tana bacci. Da sauri Fadila ta amshe ta, Arif da gudu ya biyo ta shima ya shige jikin ta yana fadin "Oyoyo Anty kin dawo gidan Daddyn mu ne?" Murmushi tayi, yaron akwai wayau da alamun har yanzu bai manta ta ba.
Boxes in su da ke booth in motan shi ya je yana shigo da su ta na amsa tana sawa a dayan dakin da ke kusa da nata. Bai ce mata kala ba ita ma ba ta tanka ba sai ma Areef ne ke ta faman fada mata "suma sun dawo gidan Daddyn"
Tun daga ranar routine in su ya canja, Da safe dukkan su su ke fita bayan ta shirya yaran. Ita ya ke fara saukewa a school sannan ya ajiye Arif a school insu da ke nan kusa da gidan su Sumayyan sannan ya kai baby ilham gidan su sai ya wuce aiki. In ko an tashi daga school, Sumayyan ke sawa a dauko mata Arif sai bayan magrib zai je ya dauko su. Weekend ko gabadaya a can wurin mahaifiyar su ke.
Tunda daga lokacin sabon su ya ragu, yanzu kam in kaga doguwan magana ta shiga tsakanin su to fa akan yaran shi ne. "Suna son kaza, ki dinga musu kaza, ba sai son kaza, a dinga kula da su sosai da assignment in su" haka hira kullum su zai sa a gaba su yi tayi. Ba wai ta na kishi da yaran bane Aa rashin daukan ta da mahimmanci ne ke bata mata rai. Bai ganin abinda ta ke ma yaran ko kadan balle ya yaba a ganin shi dolen ta ne yi, kuma abu kadan zai nemi yi mata gyara akan su. Ba abinda ke ba ta haushi sai yana fadin "ki dinga lura da su sosai Dan Allah kin ga in abu ya same su mahaifiyar su ba za ta ji dadi ba" don ma yaran na rage mata kewa sosai ne. Balle ma karamar gabadaya ta gama shiga jikin ta don wata rana da kuka su ke rabuwa.
Abinda ta lura dashi dadewan da ya ke kafin ya dauko yaran da dare hira ya ke tsayawa gun mahaifiyar su. Hakanan kuma ba sai su ka tsari yin wayan dare ba. Kai sai ya zamo hatta Sallan Asuba shi ya ke tada ta. Ba ta sake da lamarin ba sai da ta ji ranar suna maganan auren kisan wuta. Lallai abin Ya Najib yayi nisa, shin wannan wani irin soyayya ne Wanda ba ji ba gani?
Ba irin rokon da Fadila ba ta mai ba ya kai ta taje ta dubo Ya Mk amma fir ya ki, wai yaran fa. Ba tare da wani tunani ba tace "ba sai ka kaisu gidansu Anty Sumayya ba" kaman jira ya ke ya hau masifa yana fadin ba ita za ta fada mai abinda yayi niyya ba. Tsabagen takaici suna waya da Ummi ta ke jin labarin ya je katsina duba mukhtar in daga workshop in da yaje Abuja ya karasa can.
Da ta nuna ma Ummin tana son ta zo, ce mata ta yi tai zamanta tunda ba lfy za ta bashi ba. Shi ma mukhtar in bai goyi bayan zuwan na ta ba.
BINABASA MO ANG
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...