Babi na talatin da takwas ( 38 )

1.2K 111 30
                                    

Dawowan Asmau kenan daga wurin Umar ta iske missed call in MK ta WhatsApp video call. Jiki na rawa ta yi calling back, don ko ita kanta tayi kewan shi sosai cikin yan kwanakin nan.  Call in na shiga yayi picking. Kasa furta komai su kayi sai Asmau da ta bishi da kallo tana lura da yanayin da fuskan shi ya canja gabadaya. Gane kallon shi ta ke yi yasa shima din ya kasa furta komai har sai da ta gama sannan yace "kin game kare min kallon?"

Bata rai tayi kaman za tayi kuka tace "Ba haka ake yi ba wlh Ya MK haka mu kayi da Kai?"

"Me ya faru? Me na ma kanwata?" Hararan shi tayi "Alkawari bai ce haka ba wlh, gsky ni nayi fushi ma" murmushin karfin hali ya saki yace "ba a fushi da mutum in har bai San abinda yayi ba, nayi kewan ki kwanaki, ina mararin in Kira in ganki ashe ke fushi ma kike Dani ko?"

"Hmm! Na dauka za ka zo bikin Ya Muhsin ai"

"Aiki ya min yawa ne Asmy gashi  Yusuf bai gari dole ni in zan tsaya Amma na so nazo"

"Bakomai Amma ka sake ciwo ne?"

"Mai kika gani?"

"Ba ma abinda ban gani ba, ji fuskan ka kadai abin kallo ne talkless of raman da na hango ka zuba"  shafa gemun da ya cika mai fuska yayi yana smiling, he can't remember when last ya je aski ballantana kuma gyaran fuska. Gabadaya gashi ya cika fuskan ta ko ina, wannan kwantaccen sajen duk yayi wani iri.

Karfin hali yayi yace "aiki ne ya min yawa, I don't have enough time na kaina kwata kwata. Kinga yanzu 3 hours ya rage mu tashi fa"

Murmushi kawai tayi domin ko she knows him too much for him to say such thing har kuma tayi believing. Komin tight schedules in shi he squeeze time to take care of himself. Da alamun dai alkawarin da ya dauka ya kasa cikuwa.

"Kuna shan yawo a sama"

"Kedai kika dauke shi yawan mu kam aiki muke"

"Pls shave this beard mana"

"Its makes me ugly"

"No, you looks somehow dai kawai please do shave it kaji?"

"But i don't want to"

Ba ta San sanda tace "can't you scarifice for me?"

Directly yace Mata "okay, I will do it for you"

"Promise?" Nodding kanshi kawai ya Mata yace "Trust me mana, Ya bikin?"

"Biki ya kare, its was epic. Gobe zamu koma school"

"Okay ki gaida kowa please, I have to go now"

  Da kyar ta iya fadin "okay bye bye" suna gama wayan ta zuba uban tagumi tana tunanin irin wannan rayuwar ta ta. She is so heart broken, ji ta ke kaman ta rushe da kuka. Azkar ta fara yi cikin zuciyan ta sannan ta ji saukin abinda ya taso Mata. Sai a lokacin ta lura da Suhaila da ke can karshen gadon ta kwanta da ear piece a kunne ta ta dukunkune cikin hijabi. A ranta ta ke fadin ita kuma wannan mai ya ke damun ta? Ba ta tsamman akwai abinda zai sa Suhaila ta shiga irin wannan situation in ba, jin yanda ta ke ta faman ajiyar zuciya ya sa ta yi tunanin ko dai ba lafiya bane.

A hankali tayi tapping inta ta dago, yanda idanun ta suka rikida su kayi ja ya tabbatar wa Asmaun zargin ta. "Suhaila are you normal?" Nodding kanta tayi tana Shirin juyawa. Asmau tace "I don't think you are saying the truth, let me call Mami" ta yi azaman fita Suhailan ta yi saurin riko hannun ta, hakan ya sa ta juyowa ta kalle ta. Girgiza ma ta Kai tayi sannan ta fara magana in a very low tone "Kar ki kirata pls, Mami ba za ta iya warkar min da ciwo na ba haka ma kuma likita. It's emotional issue." Nan ta ke Asmaun matsalar su iri daya ne, sai dai ba ta San takamemen reason ba.

"Although ban San matsalar ki kuma am not in the right spot to advice someone saboda ni kaina ban yi sorting nawa issue in ba. I will like to say this, ki maida lamuran ki ga Allah Suhaila domin shi kadai ne mafita a gare ki. Ki yawaita azkar, karatun qur'ani da nafiloli musamman ma cikin dare domin Allah na amsan addu'an mabukaci a wannan lokaci. Sannan ina mai shawartar ki da Kar ki ba wa Allah zabi ki nemi zabin a gare shi."
  Ajiyar zuciya ta saki tace "nagode sosai Asmau though we are not close may be due to misunderstandings and differences I will like to share this with you" kallon ta Asmau ta ke tana mamakin Wai yau ita ce Suhaila ki Shirin fadawa matsalan da ya shafi rayuwar ta. Mutuniyar da ba Wai wani magana ya cika shiga tsakanin su ba. Kaman suhailan ta gano zuciyar ta tace Mata "kina mamaki ko?" Nodding kai Asmau tayi. Kakkalo murmushi suhailan tayi tace "don't be, in kayi la'akari Asmau na fuskan ci matsalar mu iri daya ce sai dai ina ganin naki ya fi nawa sauki domin ke duk Wanda ya San ya mukhtar ya San yana kaunar ki" ita dai Asmau kallon ta kawai ta ke domin a tunanin ta Suhailan ba ta wani lura da abinda ke faruwa a family in gabadaya domin ko da wasa ba a ganin ta tasa baki.

"Na yaba da hankalin ki kuma ina tunanin zaki fi fahimtan matsala na because you have an experience. And also i will like to share it maybe my mind will be at ease, kila in dan samu wani sauki for letting it out. Kece ta farko a kaf fadin duniyan nan da zan fara fadawa abin ina fatan zaki min kyakyawan fahimta?" Dukkan wani hankalin ta da natsuwan ta ta tattara gun Suhaila domin jin wani matsala ne ke damun yar uwar ta ta haka.

"Asmau tunda na taso na tsinci kaina a cikin wani hali game da Ya Muhsin tun ban San kaina ba kuma ban San menene ba har nazo na fara fahimta. Da nazo na gane kuwa ba karamin yaki nayi da zuciya ta ba wurin ganin nayi yaki akan abinda na ke ji akan shi sai dai ko kadan bai ragu ba sai ma kara karuwa ko linkuwa da ya ke yi. Na dade da ciwon nan a zuciya ta ko ina ganin shi ko ban ganin shi abin mamakin kuwa shine yanda ko kadan ba ma jituwa dashi Amma duk da haka zuciyan tawa ta ki hakura dashi. Tun ina share abin har yazo yafi karfi na da kaina na zo na amince da cewa ina son nashi sai dai kuma na sa wa raina ba zan taba samun shi ba sanin halin da mu ke ciki na rashin jituwan. Abin mamaki tunda aka fara maganan auren shi na ke jin wani iri azzababen kishi da na kasa controlling, ni nasa ba ni na daurawa kaina ba Amma wlh ko son ganin Rahma bana yi duk da ita tana kokarin sakewa Dani. Ba karamin kishi na ke da ita. Na rasa dalili na rasa ya zanyi na cire soyayyan da kuma kishin gabadaya domin nayi imanin cewa muhsin bai so na kaman yanda na ke yi. Asali ma bai ma San Ina yi ba domin ko ba tani ya ke ba. Though tun ranar da ya dauko ni daga Zaria ya fara sassautowa yana tmby na damuwa ta bai San shine sillah ba" ta karshe maganan hade da daura hannu a Kai alamun rashin mafita. Yanayin yanda ta ke magana kadai ya tabbatar wa Asmaun da gaskiyan maganan na ta daga zuci ya ke fitowa. Girgiza Kai tayi sannan ta sauke ma ta hannuwan nata.

"Ki daina daura hannu a Kai Suhaila. Allah ya San matsalar ki kuma zai magance miki" waazi ta Mata sosai mai ratsa jiki har ta dan ji sauki a zuciyan ta. Sai dai duk da haka kukan da ke makale ya ki fitowa sai kukan zuci ta ke. For the first time tayi appearing weak a gaban wani mutum.

Wasu shawarwarin ta kara bata Wanda a ganin ta zai dan kawo wa Suhailan mafita... Ko menene? Ta matukar tausaya Mata domin ta yarda nata case in mai sauki ne. A ganin ta da mukhtar bai bayyana soyayyan shi a gareta ba to da ba ma zata fuskanci ita ma tan son nashi ba.

Haka dai biki ya watse kowa ya koma inda ya fito. Sai muce Allah ya bada zaman lfy.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now