Babi na ashirin da takwas ( 28 )

904 84 8
                                    

Zaune su ke da Umar a dakin shi. Breakfast ne a gaban su, Umar in kadai ke ci shi ko sai juya spoon ya ke cikin bakin shayin da ke gaban shi.

"Wai Mk lfy kuwa tunda na zo garin nan na lura kaman kana da matsala"

huci Mukhtar in yayi a ranshi yana fadin waya ja min ban da kai? A fili ko cewa yayi "ina cikin matsala Umar matsalan da ba mai fidda ni sai Allah"

ajiyar zuciya Umar in ya saki sannan yace "Subhanallah!  Allah ya raba mu da matsala. Wannan wani irin abu ne Mk? Nasan dai ba rashin lfy bane kuma ba family issues haka kuma ban tunanin financial stuffs ne ko dai matsala ne daga wurin aikin ka"

Girgiza kai yayi sannan yace "ba ko daya wlh, sharrin ya' mace ne kawai"

Cike da rudu Umar in ke kallon shi "ban gane ba? Sharri ta maka ko kuma me?"

"I've been in love with her all my life and she is getting married soon"

Girgiza kai yayi cike da tausayawa sannan yace "to ba ta San kana son na ta bane?"

"She knows" ya fadi a takaice

"Then what is the problem? Is she not feeling the same?"

"Ita ma tana sona sosai Umar sai dai tana claiming ba ta so taci amanar wancan saboda shi ta fara dating kafin inyi proposing to her"

Girgiza kai yayi cikin alhini sannan ya ce "kar ka damu in har matarka ce to fa ba makawa sai ka aure ta. Ka mikawa wa Allah lamuranka. Ban San halin waccan ba Amma tabbas da nine I will understand in barta ta auri Wanda ta ke so"

Kallon shi Mk yayi sannan yace "kai Umar are you sure za ka iya wannan sadaukarwar kuwa yanzu ace akan Asmau hakan ya faru" dan Jim Umar yayi da alamar ya sha jinin jikin shi a sanyaye yace "why not? In har na gano hankalin ta ya fi karkata wurin shi"

"I hopes so" Mukhtar ya fadi hade da mikewa ya nufi cikin gida.

.....

Bai kara shiga wani hali ba sai da labari ya isko shi cewar an sa ka rana amma shekara daya. Gabadaya cikin dare ya fita hayyacin shi, a yanda ya ke jin shi da kuka ya samu da ya samu kwanciyar hankali. Yana cikin wani mawuyacin hali mai wiyan fasaltawa, kana ganin shi kasan yana da damuwa, har wani rama yayi ya canja kama bai da kuzari ko kadan. Tsakanin shi da Asmau kuma ba mai neman juna, abinda ke kara ba ta mishi rai kenan. Gani ya ke kaman shi kadai ke haukan shi.

Tabbas Abinda kake so shi ke wahalar da kai. Hakan ne ya faru wurin Mukhtar. Suna zaune da Ummi ta na mishi nasiha ganin halin da ya shiga sai gani tayi ya rike kirjin shi yana nishi kafin ta ankara sai gani tayi bai numfashi. A tsorace tayi kan shi tana watsa mai ruwa... A takaice ranar dai a asibiti ya kwana.

Zaria, Nigeria.

Zaune ta ke akan reading table in da ke cikin dakin da ear piece makale a kunnen ta, idanuwan ta ko naga system in da ke gabanta tana kallon wani music video na Rihannah. Fadan irin annashuwan da ke zuciyan ta bata baki ne sai dai kuma ko fa wasa ba za ki iya ganin hakan a fuskan ta ba. Tapping inta da friend inta tayi ya sa ta juyowa. Fatima ce dai kawarta tun a kano "You phone has been ringing" ta fadi tana nuna mata wayan. Wayan ta bi da kallo yana ta faman haske, siririn tsaki ta ja sannan ta jawo wayan ta dauka "Any problem?" Abinda ta fara furtawa kenan bayan ta dau wayan.

Ajiyar zuciya aka saki daga dayan bangaren yace "Haba shona ya zaki min haka?"

Cikin kwanciyar hankali ta fara magana "Ya kake so in maka ne Prince? Kalla ni fa ban son damuwa. Face your wedding please"

"Haba shona to ba za kizo event in ba?"

"Kasan ba kowani events na ke attending ba but i will try and attend tomorrow's dinner for the sake of our relationship"

"Tou shona zan iya ganin ki Yau?"

A hankali tace "ur wish" sannan ta katse wayan. She can't tolerate abubuwan da prince ke mata, ita baa ita tasa shi auren dole ba hasalima daga sama taji. To na miye ne zai dameta bayan itan ma fama ta ke da kanta. She can't believe abinda ta raina na neman  fin karfinta. A ganin ta ta wuce da ajin shi sai gashi kuma zuciyan ta na son ba da ita. Gashi shi ma ya dage akan maganan are kwanan nan. Ita kam baa ta san ya za tayi ba. She have been rejecting the feeling its seems like ba zai yiwu ba. Of all people na duniya, duk cikin samarin ta ta rasa na zaba sai muhsin. Ita kam soyayya bai mata adalci ba, kwata kwata.

"Yanzu dagaske suhaila za ki dinner in prince?"

Arzikin kallo ba ta samu balle tayi tunanin za ta tanka "gani nayi wai Amaryar yar history. Kusan tare mu ke lectures ba ki tunanin za a samu matsala" tabe baki suhaila tayi tace "INA ruwa na da ita, wurinta zani?"

Murmushi Fatima sanin halin kawarta tace "Ban baki labari ba, dazu na ga Budurwar Ya Muhsin"

Dum! Suhaila ta ji kirjin ta ya buga. Saurin fuskesa tayi don ba ta son ta bada fuskan da za a ga alamun soyayyan shi da ke dankare a zuciyan ta. "Rahma, tasha farin kayan ta na nurses in gaya miki, khadija ke nuna min ita kinsan layin su daya. Ba laifi yarinyar na da kyau amma ba ta kamo kafan Muhsin ba wlh" da Fatima za ta san halin da kawar ta ta tashiga da tun tuni tayi shiru.

  Dan karamin veil in da yayi marching da fitted gown in da atamfan da ke jikin ta fatiman ta dauka ta sa akai ko dankwali babu akan. "Ina ga bae ya iso yana kira na, sai Monday zan dawo wannan karon" kala suhaila ba tace mata ba har ta fita ta bi saurayin nata.

Daman dai aikin kenan, hostel ta ke sai dai Rabin kayan ta na dakin Suhaila while the rest na dakin saurayin ta da take weekend a wurin shi. Fitsaran ta take yi kaman ba wacce ta zo makaranta ba.

....

Wasa wasa MK jiki ya ki dadi, tun suna sa ran sallama har su ka fidda domin ko kullum abin kara rikicewa ya ke. A asibitin Dr dara aka kwantar dashi, gabadya ya zama wani abun kaman ba MK in da ka sani ba. Bp kullum karuwa ya ke abu yaki ci yaki cinyewa, drip ya sha har ba adadi.

Duk abun nan Asmau ba ta da labari, itan ma dai ba dadi jikin yayi ba don sai da ta je pharmacy ta sha alurori tukunna. Sai dai tayi kokarin sa wa zuciyan ta sallama don kwanan nan sosai ta sakewa Umar jiki amma fa ruhin ta na ga malam mukhtar.

Waya su ke da Maman ta ta ke sanar mata zata asibiti dubiya. "Mah wa ye ba lafiya?"

"Yayan Ku man's baki da labari ne, kar dai ba ki kira kin gaishe shi ba?"

Cike da rudu tace "mama Wanne daga cikin yayyin"

"Au da gaske ba ki sanin ba kenan. Tou mukhtar ne kuma yana jin jiki sosai. Kin kira ki gaishe shi yanzu ba sai Anjima ba" kafin Maman ta cigaba da fadan ta, tayi saurin cewa "Mama in zo katsinan in gaishe shi mana kawai"

"In kinzo za ki bashi lfy ne Asmau? Kiyi zamanki ki mishi addu'a kawai" sai dai kafin maman ta kara cewa komai sai ji tayi Asmaun ta saki kuka tana rokon ta ta bar ta.

Ba ranar mama Aisha ta fara zargin tsakanin su ba amma action in Asmaun ya tabbatar mata. Sai dai a tunanin ta Asmaun ce kawai ke son shi banda shi. Addu'a tayi wa iyar tata sannan tace "kukan me kike, Faisal zai so gobe zan mishi magana sai ki biyo shi, kinji" kaman karamar yarinya haka ta amsa, sai dai ji ta ke kaman ta jawo washegarin yazo.




ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now