Kaduna, Nigeria.
A tsakanin zaman Fadila da Najib zamu iya cewa abubuwa dayawa sun canja sai dai ba duka ba. Domin kuwa yanzu ba Sumayya haka kuma ba yawan zuwa gidan su sai dai duk da haka Najib in har yanzu ya kam bata umurni akan yaran shi, kasantuwar ta mai hakuri sai hakan bai zama wani matsala ba tana bin shi yanda ya ke so haka kuma shi ma yana kokarin kwatantawa musamman ganin ajiyan shi a jikin ta. Haka kurum ya kan tsinci kan shi da tausayin yarinyar lokuta da dama.
Wannan karon satin shi daya a Lagos kafin ya dawo gida. Tsaraba dayawa ya kawo wa yaran suna ta murna, hadda unborn baby ma an siyo mishi Amma matan gidan kam banda kayan abinci ba abinda ta gani. Ta dan ji ba dadi Amma ba ta sa aka ba, ta ma godewa Allah dan shi kam a wurin abinci ba za a raina mishi ba haka sutura. Musamman ya ke ba ta kudi ta siya abinda ba ta dashi, sha'anin makarantar ta kuma bai taba gazawa ba shima. Sai dai hakan yafi Mata Kama da kyautatawa tsakanin Yan uwa akan ma'aurata. Anya Najib ya dauke ta a matsayin mata kuwa? Har yanzu ba wani hiran kirki da ke shiga tsakanin su, Kai yanzu shakuwar su ta baya ma duk ya tafi. Su dai kawai gasu nan ne, Amma ba wani effort na cigaba.
Zaune ta ke kan kujera a zahiri tana kallon yaran da ke gaban ta suna homework sai dai gabadaya hankalin ta bai kansu. A haka mahaifin yaran ya fito daga daki ya iske su "Ah ah Fadila ya kika kyale su su kadai suna Homework in ai da kin jawo su kunyi tare koh" kerere ta kalle shi sannan ta tashi a fusace ta yi daki ba tare da ta tsaya sauraren Abinda ya ke fada mata ba. Direct kan Gado ta nufa tana fidda wani hawaye mai zafi. Shin wannan wani irin rayuwa ce? Ta rasa wani irin zama ta ke a gidan Najib. Ita dai kam ta gaji dole ta nemi mafita.
Cikin da ke jikin ta Kai wa duba a hankali ta shafo sannan ta kara sakin kuka. Ko wani irin rayuwa zai yi? Shine abinda ya fara fado mata. Sheshekan kukan ta ya jiyo ga mamakin shi gani yayi arif ya ture assignment in shima zai fara kukan. "Lafiya" ya ce yana kallon shi.
"Daddy to ba Kai bane kake wa Anty mommy fada ka sa ta kuka" fashewa da kuka yayi ita ma ilham kamaj ta fahimci me ake fadi ita ma ta sa kukan. Rike Kai yayi yana kallon su sai dai hankalin shi ba akan su yake ba. Tun sanda Arif ya Kira Anty Mummy ya fada tunanin mahaifiyar shi. Hakika ko yaushe cikin kewan ta ya ke, irin shakuwar da ke tsakanin su da yanda ta tafi ta bar su bayan ta Sha fada mai ya kula da kanwar shi. Anya yana ma kula da Suhaila kuwa? Sannan ta Sha mai nasiha ya rike yan uwan shi, ya so su Kar ya kuma yanke zumunci. Amma duka wanne ne bai you ciki ba? Musamman ga Fadila da ya ke ganin yana kwarar ta. Yana tuna farkon komawan shi katsina. Da farko gun Hajja aka Kai shi amma a hankali ya sidado ya koma jikin Goggo Fulani da ya ke ta fi Jan yaron a jiki akan hajjan, akan hakan har so aka yi aji kan su da kyar baffa ya daidai ta al'amarin. Ya dauke shi ya Kai shi gidan Baba kabeer, lokacin mukhtar ne kawai. Soyayyan da tarbiyyan da Ummi ta mishi kadai bai ci ace jinin ta yau yana kuka dashi ba kwata kwata. A gaban idon shi aka haifi Fadila, domin ko dashi aka yi rainon cikin ta. Lokacin da aka haife ta shi ya ke rainon ta dan ta ma fi yards dashi akan mukhtar wanda dalilin haka ne ya sa shima ya samu Asmau. Ta gara wayau ya koma boarding Wanda yayi sanadiyan da ya koma gidan Baffan sai dai duk da haka rabin hutun shi a gidan ne sauran kuma a Kano.
Tafin da ya ji akan fuskan shi ne ya sa ya dawo daga dogon tunanin da ya tafi. "Me ke damun ka Ya Najib?" Ka tasa Yara a gaba sai kuka su ke, lfy? Ina Fadilan?" Muhsin ne daman sunyi za su hadu sai dai shi gabadaya ya manta sanadiyan abinda ya faru. "Uncle Anty daki kuka" da mamaki Muhsin ya kalli Najib yace "talk mana lfy?"
Girgiza Kai yayi ya kalli Muhsin da ya dauki ilham yana lallashi, Arif ko sai kokarin Jan hannun shi ya ke su tafi dakin. Da sauri ya Mike yace wa Muhsin "Afuwan Bro bara nazo"
Har yanzu kukan ta ke. Ko da ta ganshi ba tayi yunkuri dainawa ba sai ma dauke Kai da tayi, ya ma kasa ta yanda zai fara mata magana sai dai kaman an tsikaro ta ya ganta ta mike ta nufe shi tana share hawayen da ke idanuwan ta. A gaban shi ta durkusa za ta fara magana yayi saurin girgiza kan shi, shima durkusa wan yayi yana kokarin dago ta sai dai ko kadan ba alamun za ta mike din. Da kyar ta fara magana duk da maganan da kyar ya ke fitowa "Ya Najib kayi hakuri in na maka wani abu ne kake min wannan horon Amma nikam na gaji hakanan Dan Allah ka taimake ni ka sallameni kawai, in dan su Arif ne na maka alkwarin zan kulan maka dasu ka maida katsinan gabadaya."
Wani tausayin ta yaji ya mamaye shi. Wato duk abinda ya Mata still tana da burin kula mishi da yaran shi? Bai ma San da wani kalma zai fara neman Afuwan ta ba. Kan ta ya dago yana kallon yanda idanuwan ta su ka kada su kayi ja, tabbas bai ma Fadila adalci ba a rayuwa. Kasan dauka. Wani kokaron action yayi sai rungumo ta yayi a jikin shi sosai yana sauraron sautin numfashin ta da ke sauka, tausayin ta na kara ratsa shi. Hakika yau da wani yayi wa Fadila abinda shi ya mata to fa da babu abinda zai hana ya dau mataki tsattsaura. In ko hakane to tabbas shi kanshi ya cancanci hukunci because she didn't deserve someone like him.
A hankali ya dago ta ya Ciro ta daga jikin shi, hanky ya Ciro ya share Mata hawayen da ke idanuwan ta. Jikin shi gabadaya rawa ya ke yi "katsina kike so ki koma?" Ba tare da wani tunani ba ta daga mishi kai.
"Hakan zai faran ta miki rai?" Ganin yanda tayi saurin daga mishi Kai ya sa shi kara tabbatar wa abinda ta ke son in kenan. Lallai kam yayi asaran nagartacciyar mace kaman Fadila. Wani kwalla yaji na neman zubo mishi yayi saurin goge wa.Daga ta yayi ya ajiye kan gado yace "am sorry kanwata nasan na cuce, tabbas i didn't deserve to have you. Zan miki abinda kike so, ki shirya kayan ku gabadaya gobe zan Kai ku katsinan in Sha Allah."
Ita dai kallon shi kawai ta ke ta kasa fahimtan abinda ya ke nufi har ya bar dakin. Ya na nufin ya yarda da bukatan ta Kenan ya hakura da auren ta? Ko da yake ba abin mamaki bane la'akari da tun can Daman a matsayin kanwa ya dauke ta, ba wani son ta ya ke ba. Kila Daman jira ya ke ta furta da kanta. Kwalla taji yana zubo Mata cike da tausayin kanta da kuma na abinda zata haifa.
Ko da Najib ya fita, fita su kayi da Muhsin bayan ya Kai yaran daki da ke duk sun yi bacci. Muhsin bai nemi jin wani ba'asin abinda ya faru tun da ya fuskanci tsakanin shi da matar shi. Sai ce mishi da yayi "please brother always know how to tackle your problems" murmushi kawai ya mai yace "nagode brother"
ČTEŠ
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...