Ranar dai har Rahma sai da ta kasa gane kanshi duk koma yanda ya ke kokarin boye Mata duk matsalan da ta danganci tsakanin shi da Suhaila. Hakanan su na zaune sai ta ji ya ja tsaki, tun tana tmbyn lfy har tayi jugun tana kallon shi. Bacci wannan kasa yi yayi yana ta juye juye gabadaya ya rasa ina zai sa kanshi. Ita kam Rahma abin ya fara ba ta tsoro kasa jurewa tayi ta dinga tmbyn shi. Yanda ta sauya ne ya sa ya dan ji wani iri Amma ta ya zai kalli idanuwan ta yace Mata saboda soyayyan yar uwarta mace ya sa shi shiga wannan halin. Dole yayi karfin hali saboda ita. Sai da tayi bacci sannan ya tashi ya jero nafiloli game da yin istikhara.
Ana idar da sallan asubahi ya dannawa Faroukh Kira.
"Kai lfy?" Faroukh in ya fada bayan ya daga "Ina fa lfy?""Me ya faru?"
"In kana gida gani nan zuwa"
"Do asubahin nan?" Ba tsaya amsa wa ba ya kashen waya. Text ya tura wa Rahma akan za shi wani wuri. Ko da ya isa wurin Faroukh in har ya koma bacci. Duka ya daka mai a cinya yace "Kai tashi dallah duniya ba lfy kana bacci" tashi yayi yana mitsika ido yace "Amma ba ka kyauta min ba Muhsin, in mafarkin nayi aure na ke fa?"
"To Daman ku gauraye me kike yi banda wannan"
"Allah ki yaushe ma..."
Katse shi Muhsin yayi yace "dakata malam ba wannan nace maka fa duniya ba lfy?"
"Wai da gaske a Ina ake fada"
Nuna mishi saitin zuciyan shi Muhsin yayi yace "wlh a Nan ne Dan ya ma fi karfin a Kira shi sa fada yanzu sai dai yaki"
"Subhanallah Kar kace min matsala ku ka samu da uwargida?"
"Haba wannan ai tana hannu banda abinka ba ita ba"
"Waye toh"
"Amaryar mana"
Shiru Faroukh yayi yana tunani kafin ya kwashe da dariya yace "wlh Muhsin ba ka da kunya. Nan kazo ka gama cika min baki a kanta. Ba abinda ba ka fada ba, da dakin ma na magana da ya maimaita ma"
"Its all in the past Faroukh let face the present"
"Me ya faru? You can't confront her? You want me to tell her? Or what?" Tsaki Muhsin yayi sannan ya fada mishi yanda su kayi da ita game da Mahmud.
"Wonderful kaga ko maganan ka ta dauka"
"Faroukh let be serious mana"
Shiru Faroukh yayi yace "kasan mai? Karya za muyi Amma tunda am saving life Allah ya yafe mana" da idon rashin fahimta Muhsin ya bishi da kallo.
"Yanzu dai call her ka tmby is she serious? Inta nuna she is then ask her for the guy number sai muyi proceeding" kallon is this a good idea Muhsin ya bi Faroukh in dashi.
"If you are doubting me then leave it" jin haka yasa yayi saurin Kiran ta. Yasan if Faroukh is serious...
Ta koma bacci kenan bayan ta gama azkar ta ji wayan ta na ringing. Da mamaki ta bi sunan Muhsin da kallo. Tunanin ko ba lfy ba yasa tayi saurin daukan wayan.
"Sallamu Alaikum"
"Wa'alaiki Salam, kin yi sallah"
Ajiyan zuciya tayi tace "Tun dazu"
"Okay then i want to ask you akan Mahmud are you serious please?"
Dariya abin ya so ba ta Amma sai ta fuske tace "Eh mana that is why i told you"
"Okay then send me the guy number let us talk tukunna"
"Right now" ta fadi sannan ya kashe wayan.
Kallon Faroukh yayi sannan yace "its seems futile"
"Dadi na da Kai hanzari, ji yanda kake ta wani hade rai kana Mata magana kaman da gasken Nan"
"Ban son wulakanci"
Suna cikin magana numban ya shigo. Nuna ma Faroukh numban yayi an rubuta My prince a sama. Which means haka tayi saving numban shi.
Fada mishi yanad zai yi Faroukh yayi shi dai Muhsin fatan shi daya Allah yasa plan in yayi working.
.....
Zaune su ke gabadaya a parlon mummy suna kallo ita da kannen ta da mummyn. Daddy ne yayi sallama ya shigo daga gudu younger ones in su ka tashi suna mishi oyoyo. Da murmushi kwance a fuskan shi ya ke hugging insu sannan ya amsa gaisuwan su meema.
Kallon shi mummy tayi tace "Da alamun yau akwai kyakyawan labari daga ganin fuskan ka daddy" murmushi ya sake yi jin kalaman mummyn.
"Haka na ke Fata maman halimatu" dariya tayi saboda jin yanda ya ambaci sunan meema kadai ya tabbatar ma ta da maganan akan ta ne"
A hankali meema ta gama sauraron abinda mahaifin na ta ya ke fada mata bayan ya aika a kirata falon shi, daga ita sai shi su ke magana don ko mummy ba a gayyata ba. Idon ta ne yayi raurau yanda ta ke jin Daddyn ke fada mata "Ki yi hakuri ki amince da auren Nan meema nasan ba Wai kina kinshi bane, I know your dreams and i plan helping you with it. Duk wani burin ki zan cika miki, I will even give you the whole Eminent da capital in da za ki bunkasa shi according to your own taste. Amma buri na daya ki amince ko don saboda mahaifiyar ki"
Nazari ta ke a zuciyan ta. If Daddy can help her achieve her dreams then she is Willing to do anything for it. Sai dai she is very sure ba za ta iya auren Dr Aliyu ba saboda halayen shi da yanayin shi da ta fuskan ta.
Ajiyar zuciya ta yi tace "Nagode sosai Daddy sai dai ni ban turo Dr Aliyu ba hasalima hakuri na bashi but he is so persistent" ganin fuskan Daddy na kokarin canjawa tayi saurin cewa "Amma Daddy daman akwai Wanda mu ka gama magana dashi zai zo ya ganka" without much thought taji ta tana fadan hakan.
Shi ko Daddy da bai san abinda ake ciki murmushi ya zuba sosai yace "Ma Sha Allahu ki turo min shi gobe in ganshi da rana shi kuma likita zan same shi zamuyi maganan fahimta a tsakanin mu"
Kanta a kasa Dan ba ta so Daddyn ya fahimci wani abu tace "shknn zan mishi magana in Sha Allah"
Sallaman ta yayi ta tafi cikin wasi wasi. Ga dai burin ta na son cika Amma shin wa za ta iya gabatarwa Daddy? Tabbas ba za ta iya bari wannan dama ya wuce ta ba haka kuma ba za ta iya auren Dr Aliyu ba saboda ra'ayoyinshi da kuma tsanin shi.
Daren ranar ba tayi wani baccin kirki ba sai tunanin mafita ta ke Wanda ta kasa samowa ko ta wacce hanyan. Ta San ba Wanda ta isa ta tunkara da magana domin ba alamun goyon baya.
Haka gari ya waye ba tare da ta samo mafita ba kwata kwata. Kin fito dakin ma tayi gabadaya. Amma hakan duk bai hana Daddy yasa a Kira mi shi ita ba bayan ya gama lunch.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...