Babi na arba'in da shidda ( 46 )

958 102 4
                                    

Katsina ta ma mukhtar zafi fiye da zaton shi, sukuku haka za ka ganshi kwata kwata ba wani annashuwa da farin ciki na ango, Wanda hakan yayi sanadiyyan da yasa baba kabeer Kiran shi yana tmbyn shi ko bai son auren ne? Sosa Kai yayi yace "Aa Baba ba haka bane kawai dai banji Dadi ne, Dan Allah ku min addu'a kuma ina mai neman alfarma ka roka min gafara wurin Ummi" cikin rashin fahimta mahaifin nashi ya zuba mishi ido yace "mai kamata" girgiza Kai yayi yana mai jin wani zafi na ratsa zuciyan shi "Dan Allah Baba kar ka tmby ni, domin ba zan iya fada ba Amma Dan Allah ka bata hakuri" kallo mahaifin shi ya bishi dashi, hakan ya bashi daman saurin tashi ya bar wurin. Key in motan shi kawai ya dauka yayi waje, motan ya shiga ya tada ba tare da wani tunani ba ya dauki hanyan barin garin. Sai da ya Kai Zaria ya samu wuri yayi parking, kan shi ya kife a sitiyari. Yafi 15 minutes a haka kafin ya zaro wayan shi ya turawa Asmau text kaman haka.

Assalam Alaiki, ina mai neman afuwa a gareki ga duk abinda ya faru, I couldn't even face you or even talk to you. God knows that i didn't have that courage but please bear with me. I know you need a space so am giving you that... On my way to Abuja, see you in two weeks time when we will be leaving for Florida. Thank you.

Kwance ta ke kan gado lokacin da sakon ya shigo wayan ta. Kusan za mu iya cewa Asmau ta fi shiga matsanancin hali akan Mukhtar saboda itan mace ce tafi shi rauni. Abun ne ya taru ya cunkushe Mata. Mama tun tana rarrashi tana consoling inta har ta gaji ta sa Mata ido. Haka mahaifin ta ba irin lallaba da wa'azin da bai mata Amma a banza. Sai su ka lakanta hakan a matsayin sauyin lamarin da aka samu duk da ita mama Aishan ta San tsakanin ta da Mukhtar in Amma ana ta tunanin Kila ta saduda ta so wancan in ne.

Ummi ce kadai ta San abinda ya faru and she can't talk to her tabbacin har yanzu fushi ta ke dasu. Fadila kuwa kwata kwata ba ta son takura mata saboda a ganin ta itan ma fama ta ke da kanta, tayi nauyi sosai yanzu. Ko yaushe ta kan Kira Asmaun a Kai Kai tana tmbyn ta ya ake ciki Amma sai ta nuna mata lfy kalau babu wani abu da ke faruwa. Gabadaya cikin yan kwanakin ta zabge kullum banda kuka bata da abokin aiki. Abinci ko sosai ta ke gaba dashi sai dai kayan ruwa ta kan Dan taba. To make matters worst tun ranar da abun ya faru bata kara ganin Kiran mukhtar ba balle kuma ya so wurin ta. Kai kwata kwata ba ta da lbrn shi. Hakan ya sa ta ke ganin kaman ta zubda mutuncin kanta ne tunda ta amince dashi. In ko haka ne ai ko ta shiga uku tun ma kafin aje ko Ina fa kenan.

Da sakon ya shigo Mata rasa mai za tayi ma tayi, shin farin ciki za tayi ko akasin shi. This the problem. She doesn't even know what to feel again. Tana jin ta kaman ba ita ba, like she doesn't belong in the world.

Satin shi biyu a Abujan yana fafutukar samo Mata Visa. Da ke yana da hanyoyi da dama sannan kuma abin nasu sai aka yi sa'an nasara.

A tsorace ya dawo katsinan duk da Daman an San visan ya je nema. Ya rasa wa zai tunkaro da maganan daukar matar tashi. Yusuf ne ya bashin shawaran samun baffah. Yana lazimi ya same shi a falon Hajjah Fati, bayan ya gama gaishe shi su dan yi raha ne ya ke ce mishi "lfy muntari naga kaman da magana a bakin ka" Sosa Kai yayi cike da kunya. Dakatar dashi baffah yayi yace "ka ga nifa ban son shakiyan ci, ni daya daga cikin iyayen kane da za ka dinga min noke noke. To Maza ban son shakiyan ci fada min abinda ke cikin ka" murmushin karfin hali ya saki sannan yace "Baffah Daman ina so na koma ne jibi in Allah ya kaimu"

"Ah to Ma Sha Allah, Allah ya nuna mana Amma ni muntari yaushe za ka dawo kasar ka ne?"

"Baffah sauran shekaru kadan su ka rage, na riga nayi signing contract da su Ina gamawa zan dawo In Sha Allah"

"Tou Allah ya nuna mana, ya sa hakan shi yafi alheri"

Ameen, ya amsa sannan ya tsaya yana kallon shi. "Akwai wani matsala ne?" Baffan ya bukata.

Nodding Kai yayi sannan ya fara magana "Baffah daman maganan Asmau ne Ina so in tafi da ita jibi tunda visan ya kammala" kallon rashin fahimta baffan ya mai yace "Bangane ba tou dama ba da matar ka za ka tafi bane? Mai za ta zauna tayi mana a Nan? Ashe ma ba auren ba kenan" murmushin nasara yayi. Ai ko nan ta ke Baffah ya ciro waya ya danna wa surukin shi waya da ke daman a matsayin da ya dauke shi. Yana bukatar ganin cikin yan mintuna ya saki abinda yake ya taho wurin Baffan. Sai dai yana ganin mukhtar ya san kwanan zancen, don shi ma har ya fara tunanin lfy ya ajiye ba ko waiwaye? Me hakan ke nufi, Dan Kar yayi gajen hakuri ya sa ya sama abun ido.

Bayan sun gaisa Baffah ya tmby shi "shin ma'u ta shirya bin mijin ta jibin nan" girgiza Kai yayi yace "Gsky ba mu san da maganan ba Amma ai ba wani abu bane yau in sai ta shirya"

Murmushin manya baffah yayi yace "tou Maza ta shirya ta bi Mijin ta shine rufin asirin ta"

"Ai ba wani matsala sai dai kuma inaso in tmby shi Mukhtar game da karatun ta"

Kanshi a kasa cike da girmamawa Mukhtar in ya fara bashi amsa "Baba Daman akwai school in da na fara nema mata online tunda Exam in second semester, 100 level su ka gama.

"Tou Shknn Allah ya bada saa"

Godiya sosai mukhtar yayi bayan baban ya tabbatar mishi koman ta zai zamana a shirye.

...

Tsugunne ta ke a gaban Ummi, idanun ta sun yi luhu luhu a sanadiyyan kukan da ta sha tun kafin ta baro gidan su. Musamman Baffah ya tura manyan yaran shi Mata su kaje dauko ta su ka kawo ta gidan Baba kabeer in. Rabon ta da gidan tun ranar da Ummin ta iske su da Mukhtar.

kamo hannun ta Ummi tayi ta jawo ta jikin "Asmau ban taba Miki kallon da ba na yata ba a rayuwan nan, haka kuma ban taba kin ki da Mukhtar ba. In akwai Wanda zai yi farin cikin kasancewar ki matar shi to tabbas baya na zai biyo domin ko ke tarbiyya ta ce da na Aisha, matar da na aminta da ita fiye da Yan uwa na da mu ka fito ciki daya. Komai nayi nayi shi ne saboda Umar, sanin kan ki ne ko musulunci ya hane mu da neman aure kan wani neman. Tunda ko Allah ya yi ke matar shi ce gashi ya tabbata sai dai Ina so in sanar Miki wautan da kika yi kika yi, wani dama kika ba mukhtar domin gano laggon ki Amma mai afkuwa ya riga da ya afkuwa, Allah ya riga ya rubuta ta hakan ne kadai za ku zamo karkashin inuwa daya. Sai dai ina mai gargadin ki da ki San irin zaman da za kiyi da Mukhtar. Na San yana son ki kaman yanda ke ma kike son nashi Amma me? Kar ki bari ya dinga using wannan son da kike mai as an advantage to him." Sai da ta gama wannan sannan a hankali ta fara nausar da ita zamantakewar aure. Kalaman kwantar da hankali ta dinga Mata.

A haka Mukhtar ya shigo dakin ya iske su. Hada ido su kayi,I a tare gabansu ya buga. Tun wannan ranar sai yau su ka karasa juna a ido. A hankali ya rarrafa gaban Ummin ya kamo hannayen ta ya daura akan shi. Wani irin kuka ya saki Wanda Asmau ba ta taba zaton Namiji kaman mukhtar zai zauna yana irin wannan kukan ba, abu daya da ta kasa fahimta shine Mijin na ta mutum ne mai rauni. To ita ma dai Ummin hawayen ta ke balle Asmau da ta rakube jikin gado.

Cikin sheshekar kuka kaman zai shide ya fara magana "ki yi hakuri na San na bata Miki haka kuma ban kyauta Miki ba. Tabbas ni in mai laifi ne a gareki dama Ubangiji na da na kasance mai son Kai a cikin lamarin Nan. Ban sani ba ko dan ba ki sa albarka a auren Nan ba shiyasa gabadaya zuciyana a firgice ta ke, hankali na yaki kwanciya balle in samu natsuwa da dukkan sabbin ma'aurata ke samu. Ina mai neman Afuwa a gareki Dan Allah Ummi ki yafe..." Saurin katse shi tayi ta ya fito Asmau da hannu.

Tana karaso wa ta kamo hannayen su ta hade "Allah ya mu ku albarka, Ya kuma sa we auren ku albarka. Shin ya za muyi da kaddaran Ubangiji? Tabbas ban bakin cikin kasancewar ki karkashin inuwa daya. Ga Amanar Yata na baka, ka sani in har ka cuce ta Allah na kallon ka. Ka dauke ta ku tafi na yafe muku dukkan ku"

ABINDA KAKE SOKde žijí příběhy. Začni objevovat