Amarya ta sha kyau cikin Yellow Aso ke inta da ya sha farin stones kala kala, sai shining su ke. Half covers Fari ta sa shima mai shiny stones. Kwalliyan ya mata kyau sosai sai yabawa ake tayi. A haka su ka dawo gida friends inta ko Yellow and coffee brown Atamfa ne a jikin su. Sun sha kyau har sun gaji. Sai bayan magreeb sannan aka rankaya Star-event-arena da ke nan gaba da barhim estate. Decoration in wurin yayi kyau sosai ya bada ma'ana. Nan da nan Alameen_photography da majidpixels suka fara aikin shi na daukan portraits kala kala kafin aka fara sha'ani. An sha kidan kwarya da na zamani duka, Musamman aka kira performing artist masu tashe. Midway 2ru d event Ango ya iso da tawagar sa. Farin Shada ne a jikin da ya sha surfani. Gabadaya aikin ma fari ne yayi kyau sosai. Friends in shi na binshi a baya ya karasa wurin Amaryar tashi. "Fadila ya muka ji da hidima?" Ya fadi a hankali bayan ya zauna, da kyar ta jiyo shi ta dalilin sautin da ke tashi. Tunda fara bikin sai ranar ta sa shi a ido. Murmushin karfin hali tayi kana tace "lfy kalau, ya naka hidiman?"
"Lafiya, you looks beautiful""Thanks" ta amsa a takaice hankalinta na kan wayan da ta kan duba a kai kai. Har photographers in su ka iso ba ta Sani. "Let me get the phone" ya fadi yana kallon ta. Ba musu ta mika mishi saboda ba ta kawo komai a ranta ba. Shi ko Alijihu ya tura kafin aka fara snapping insu ta ko ina. Sunyi kala kala hadda friends da families. Har sai da ta gaji ta fara rufe idon ta tsaban yawan hasken flash har kanta juyawa ya fara yi. "Its okay please" Najib ya fadi yana jan hannun Amaryar ta sa zuwa seat insu. Ko da MC ya bukaci suyi rawa fir yaki, at the end ya tattara tawagar shi suka fita su ka bar mata da event insu. Ya kayatar gwanin sha'awa. Baba Useey kam ya sha fama da Amaryar sa da ko events ba ta yarda anyi organizing ba.
Mukhtar bai kara Neman mutuniyar sa ba. Ta ganin shi suna hira da Safiyyah da su ka zo kamun. Har photo kusa da ita ya tsaya sai wani iyayi ta ke mishi, duk inda yayi tana wurin tana kallon zee na hararan su abin ya kara kullar da ita. Shin da gayya ya ke mata hakan ko kuwa, ko da su ka hada ido wurin event in juyar da kai yayi abinshi ai ko ta shaka dayawa.
Da aka tashi event in, motar su Aliy ta bi su ka kaita can gidan su Gobarau road ta dauka Sako ta kai wa Mama nan gidan Baba kabeer kafin ta karasa. Da Umar su ka hadu zai rakata can gidan Amaren, suna tafe suna hira. A kofar gidan Baba Muhammadu ta hango Safiyyah da Mukhtar again suna hira. Kallo ta bisu dashi jiki a sanyaye don bakin ciki sai da su ka tsaya magana da Umar ka sa jurewa tayi ta tmby Safiyyah "Zamu wuce ne?" Ga mamakin ta girgiza kai Safiyyah tayi "INA jiran Yar uwa ne ta shiga gidan Baffah" tabe baki Asmau tayi ba tare da tace komai ba ta fara tafiya ko Umar ba ta jira ganin hakan yasa ya bita da Sauri. Har Gidan ya rakata ya so ya tsaya suyi hira amma bai ga fuskan ba ya sa ya wuce. Asmau na shiga gidan, kawayen da ke garin duk sunyi gida sai cousins da wadanda su ka zo daga wani gari su kuma suna zaune a falo suna hira. Ko da ta shiga dakin ba ta ga meema ba sai karan ruwa da taji alamun ana wanka a bayi. Kaman an giza ta da tuno Safiyyah da Mk na tare sai taji ta rasa mai ke mata dadi, ba zato ta ji wani kuka ya kufce mata hadda shesheka. Tun da Safiyyah tazo ya canja mata ko magana banda kiranta da yayi a waye shima zancen fita da Amaryar ne. Yau ko arzikin text in ma bata samu ba. Kukan ta taci ta godewa Allah bata Ankara ba sai ji tayi ana goge mata hawaye da hanky. Dago kanta tayi su kayi ido hudu da Faddi ashe ita ke wankan. "Kar kiyi kuka kawata nasan its hurt but believe me he loves you" dagowa tayi tana kallon ta, girgiza mata kai tayi sannan tace "stop it kinji, it won't solve Anything. Ba zan ce miki bakomai tsakanin su ba amma nasan ke din ta dabbance a rayuwarsa ki yards dani ko mai ya faru ina tare da ke" murmushi Asmau tayi sannan ta rungume Fadila. Wannan karon tare su ka fashe da kukan ko na tausayin kan shi da Dan uwansa. Asmau na lura da yanda Fadila ke damuwa da halin Najib amma tana kwantar mata da hankali. A haka Meema ta shiga ta iske su. "Kaga Aminnan juna kukan rabuwa ake, Allah sarki a yi hakuri yan kannena" sai a nan su kayi dariya, Asmau tace "Ya meema oh son girma na nan sai"
A tare Safiyyah da Suhaila su ka shigo "Amaryar Brother an bani aiki" Suhaila ta fadi tana ajiye ledojin da ke hannun ta "An ce inyi feeding inki inji Angon ki, you are so lucky you get to eat the chicken tun kafin a kai ki" kallon ta fadila ke yi ta kasa aiwatar da komai "come on sa kaya kizo kici kinga ma shi ke kira na"
Wayar Asmau ce tayi ringing ta na gani ta bata rai hade da kashe wayan gabadaya. Ba ayi 2 minute ba ya kira Safiyyah "Asmau Ya Mukhtar wai ki same shi gaban gidan nan yanzu nan" murtsuke ido Asmau tayi hade da hamman karya "please tell him am sleepy I can't go out" fada mishi Safiyyah tayi kafin ya bata amsa "to yace in ma baccin kika fara in tashe ki ki same shi yanzun nan" zata kara magana Suhaila ta akai mata da kallo mai cike da ma'anoni. Hijabin Fadilan ta dauka ta sa ya kaima ta har kasa da ke ta riga ta sa kayan bacci.
A gefen titi ta hango motan shi amma sai tayi kaman ba ta gani ba ta fara neme neman karya. Ganewa da yayi yasa ya mata horn. Ko kafin ta karasa har ya bude mata Motan. Rai a bace ta shiga ta rufo motan ba tayi aune ba ta ji ya ja motan, kasa jurewa tayi tace "INA za ka kaimu da Daren nan this is 11:30 pm"
"Abu zan amso a barhim you are accompanying me" ganin ba fuskan musu ya sa ta kame bakin ta. Kaman ba zai yi magana ba sai can yace "meyesa na kira ki baki dauka ba? Na kira yanzu kuma kin kashe wayan why?" A hankali ya fada ya kallon ta ta gefe. Wani kuka ta ji na cinta da kyar tayi kokarin dannewa kafin tace "You got a new Girlfriend ko labari" murmushin gefen baki yayi domin ko yasan za a rina "Nace miki? Why do you say so"
"Ina gani dazu da Rana you called 2 times kafin ka kira ni said m da kuka gama wayan Ku, since she came you guys are always together" INA zuwa yace mata ganin sun iso inda zashi. Ko 5 minutes bai yi ba ya fito ya koma mota ya ja. Sai da su ka fita gabadaya a Estate in sannan yace "Are you jealous?" Tabe baki tayi cike da takaici ta ce "me? Never" dariya ma ta bashi sai da ko ya murmusa tana ganin shi sannan yace "Yarinya na gano ki" banza tayi dashi shima bai kara cewa komai ba har ya kaita baking Gate "Toh Hajiya nagode da Rakiya ko, a gaishe min da new GF ita and please take a very Good care of her kinsan..." Bai gama maganan ba ta bude kofa ta fita, buga kofan tayi hade da Jan siririn tsaki ta shige. Shi kadai ya sauna ya sha dariya kafin ya kara kan motan shi zuwa inda su ke kwana.Har ya zo kwanciya ta fado mishi a rai shi kadai ya sha murmushin shi sannan ya tura mata text kaman haka "just remember Mukhtar will always loves his Queen (Asmau) kar ki takura min kanki please, you should sleep well" kaman ko ya Sani, ta na ganin SMS in ta samu relieve. Kaman shi daman ta ke jira nan da nan bacci yayi awon Baba da ita cike da nishadi da annashuwa.
Asuba ta gari Gimbiyar Mukhtar, nima nace mu kwana lafiya...
KAMU SEDANG MEMBACA
ABINDA KAKE SO
RomansaCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...