Babi na ashirin da hudu ( 24 )

1K 98 8
                                    

Washegari, Safiyya da Yusuf su ka fara tafiya wurin 11:30 am. Train za su bi daga kadunan zuwa Abuja, Mukhtar zai kai su Train station in da ke iyayen su sun wuce tun jiya.  Godiya sosai Fadila ta mata hade da bata abubuwa na musamman, ta ko ji dadi sosai sai dai har lokacin Asmau ba ta sake ba. Da za su wuce har cikin gidan Mukhtar ya shigo. Ko da ya nemi Asmau ta raka shi ce mishi tayi ita kanta na ciwo.

Yan katsina bayan azahar gabadayan su suka koma har da su zainab. Su meema  ma train in 2 su ka bi zuwa Abuja ita da mummy sai Faisal. Sauran siblings inta jigawa su ka wuce hutu wurin paternal relatives inta. Asmau ce kadai ta rage a gidan Amarya ita da Amarya, Suhaila ta fi ta a cewar ta daga can za ta wuce gidan su Faisal.

Tare su ka wuni cur Asmau na ta sake lallaba ta tana mata nasiha. An kawo su abinci daga gidan su Faisal har da Anty meena ma ta aiko nata shi kanshi angon sai da yayi aiken kaji da yoghurt. 9:30 pm na dare Mukhtar ya kira Fadila akan tace ma Asmau zai so ya dauke ta yanzu. Da tsokana tace mata "Saurayinki ya ce zai ya dauki wai" harara ta zabga mata tace "Ki bar ganin ke Amarya ce Ya Najib zai kasa gane fuskan ki Allah"
"Daga fadin gaskiya, Gwara ma a fito fili ya isa haka ana so ana kai wa kasuwa" kaman jira ta ke nan da nan ta ji abun ya bata mata rai, ba ta San lokacin da ta ja tsaki mai karfi "Ba laifinki bane ganina da kika yi ne yasa kike fadin haka next time in kin ganni ki fada"
"Da ga magana ke sarkin zuciya sai ki hau fushi" Fadila ta fada cike da mamaki. "Malama ba ruwanki dani"  kaman mai aljanu haka ta tashi tana hada duk abubuwan ta. Fadila dai bin ta ta ke kawai da kallo har ta gama ko kala ba ta ce mata ta dauki kayan tayi waje gefen veranda ta samu ta zauna ta ajiye kayan a gefe tana huci kaman Wanda tayi dambe. A haka Mukhtar ya shigo ya same ta "ah ah had kin fito?" Nodding kanta kawai tayi hade da mikewa tana shirin daukan bag inta. "No mu shiga ciki mana, zanyi magana da Fadila" komawa tayi ta zauna tace "Shknn tou zan jira ka a nan ko ma kaban keyn motan sai in jira ka waje" kallon yayi yana dan nazari kafin ya kira sunan ta. "Fada kuka yi da kawarta ki koh" shiru tayi ba ta bashi amsa ba hakan yasa shi gasgata abinda ya ke tunani. Murmushi yayi yace "Tashi mi shiga sai ayi magana gabaday"

"Ya Mk ni ba zan shiga ba" hararanta yayi yace "kinsan Allah ki tashi muje da kafan ki ko kuma in sa hannu in daga ki" gani tayi yana nade hannun rigan shi, sanin halin shi sarai zai iya abinda ya fadan ya sa ta mike tana turo baki. Girgiza kai yayi a hankali yana fadin "Asmau rigima" shi dai komai yarinyar tayi burge shi ta ke.

A falo su iske Fadila tayi jugum ta zubawa TV ido ba wai don tana fahimtan abinda ake ba. Sallaman Mk ne ya sa ta dagowa ta gansu a tare, shiyasa daman ta kyale tasan da yazo zai lallaba ta. Kusa da Fadilan ya nuna wa Asmau ta zauna sannan ya zauna yana fuskantar su. "Meye sa kuke haka ne wai Ku? Ba Ku San kun girma bane. For God sake ku rasa lokacin Fada sai time in da kuke shirin rabuwa" kallon su yake kowacce ta sa kai a kasa. Ko ba a fada mishi ba yasan wacce ba ta da gsky ganin yanda ta ke zaro idanu yasan da bata da laifi ba haka za tayi ba. "Kayi hakuri Ya mukhtar ni ban San meya bata mata rai ba daga wasa ta hau fushi"

"Naji ku dai ba kananan yara bane yanzu don haka yakamata kusan abinda ya kamace ki back to you Fadila. Ban samu lokacin tattaunawa da ke shiyasa nayi using wannan Dakar kina jina" gyade kai tayi tana sauraron shi.

Wa'azi ne ya mata sosai Wanda ya ke ganin a matsayin shi na yayanta ya kamata ya sauke wannan nauyin. A haka Najib ya iso gidan ya same su, shima gefe ya zauna yana sauraron su bayan sun gaisa. Duk da Mukhtar in kanin shi amma sai ya kasance bai son su cika zama wuri daya tunda aka fara bikin saboda irin kallon da ya ke aika mishi na in har ka cutar min da kanwa to fa dole za a samu matsala. Mukhtar in har samun shi yayi mishi magana na musamman Wanda yafi kama da gargadi. Yanzun ma daya gama da Fadila sai da ya juyo ya kalle shi alamun har da kai nake, sannan yace "Brother ka Sani cewa Fadila Amana ce a gare ka in har ka kuntata mata to fa Allah zai tmby ka" Mikewa yayi yana fadin "mun barku lfy, Asmau tashi mu tafi." Murmushi Najib in yayi ganin yanda mukhtar in ya koma kaman shine gaba a kanshi. ya ko burge shi don yasan shima zai yi fiye da haka akan Suhaila. Kai ba ma suhaila yau da Fadila wani ta aura bashi ba to fah dole ya gargade shi domin tun asali itan mutuniyar shi ce "Nagode Malam Mukhtar" ya fada yana murmushi sannan ya juyawa ga Asmau "Sannu fa kanwata mungode sosai" murmushi kawai tayi. Har mota ya raka su ya ciro rafar 500 yana mikawa Mukhtar "Gashi a ba Asmau don na lura gajiyan bikin gabadaya a kanta ya kare"

" tou shknn mun gode Ya Najib"

hararan shi Najib yayi sannan yace "kaine Asmau?"

"To ai duk abu daya ne ko Asmy?"

dariya sosai Najib yayi yana fadin "kaifa ba ka da kunya in da gaske ne mu gani a kasa"

"Soon" ya amsa sannan ya tada motan.

"Gimbiya yaya dai?" Ya fada yana kallon ta ta gefen ido bayan sun fara tafiya.

A hankali ya ji tana motsa baki "Gimbiyar ka tana Abuja" bata yi tsamman yaji ba sai ji tayi yana fadin "to ai kinga ita ta tafi don haka yanzu dole na kece a gaba" yana dariya ya karashe maganan. Asmau dai kaman daman jira ta ke sai ji tayi wani siririn kwalla na zubo mata a fuska, da sauri ta sa mayafinta ta goge ta yanda ba zai fahimta ba. Amma me? Sai ji tayi wani na fito bayan wani tun tana gogewa har abin yafi karfin ta. Yana son ya mata magana ya ga abinda ke faruwa da sauri ya ja burki yana fadin "Subhanallah ba ki da lafiya ne?" Kallon shi tayi ta watsar nan da nan ya fahimto ta "wait! Is it about the talk?" Hanky ya Ciro ya mika mata ba musu ta amsa ta shara hawayen gabadaya sannan ya mika mata ruwa a gora ta dauraye fuskanta sannan ya tada motan su ka cigaba da tafiya. "Kice ina da aiki you are so sensitive" tabe baki tayi tace "Wanda dai ke da aikin zai yishi"

"Ehmm Asmau kishi na kike?"

A hankali ta ke fadin "kishin me zanyi?"

"So why are you worried about Safiyyah"

"Ni ina ruwana daku? Damuwata ma ya ishe ni"

Siririn murmushi yayi yace "I have no connection with her, I mean not in the way you are thinking"

"Ehmm ai naga alama"

"Believe me mana Allah we are discussing something shiyasa kika ga ina neman ta"

"She loves you" ta fadi a hankali.

Nodding kan shi yayi yace "ni dai ban Sani ba koma hakan ne tou yanzu kam ta daina, Yarinyar da a ka kusa sa mata rana. Dan yayan mum insu ke sonta, infact kowa ya san da maganan. Though she is not comfortable about the issue and that's what we have been talking about. Kinji ma na bude miki sirrin wata." Shiru yayi yana kallon ta jin ba ta yi magana ba yasa ya cigaba "Ni Asmau ban San ya kike so inyi ba, har yanzu ban San matsayina a gunki ba balle in San miye next step in da zan bi kinsan dai am not willing to give up ko?"

"To ni me kake so inyi? I can't tell him am no more interested"

"Ni zan iya fada ai, yanzu tukunna daga gunki na ke son ji. I mean i need your support before proceeding. In 3 weeks time mu ke sa ran komawa Florida, Yakama ta mu San abinyi kafin nan. In kin bani dama na San Wanda zan ma magana in sha Allah ko mai zai zo cikin sauki."

"Me kika CE?"

A hankali ya ji tana fadin "Ehmm" da mamaki ya juyo yana kallon ta, Ashe dai da gaske tana son nashi? Bai yi tunanin za ta amsa mishi da wuri haka ba.

"Eh? You mean yes i can go ahead?" Daga kanta tayi cike da kunya ko kafin ya kara magana har ta bude mota ta fita daman sun riga da sun iso.

  Shin Wai ya take ne a gidan Amarya Fadila? Yakama ta musan wainar da ake toya wa...

Am publishing my English novel titled: Falling into infinity today. Please do check it, Thank you.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now