Babi na arba'in da daya ( 41 )

984 93 7
                                    

A Yan kwanaki Suhaila tayi gaining sosai a wurin Muhsin. Mostly ta WhatsApp su ke karatun, dalla dalla ya ke mata bayani sosai aiko ya fahimci tana da saurin fahimta duk da daman ya San mai kokarin ce Amma ya kara tabbatar wa. Daga tambayoyin da ta ke mishi kawai ma ya isa, hakanan zai ta mata tmby abin mamaki da wuya ya mata gyara. Qur'ani ne dai Asmau ke kar Mata, duk sanda ya shigo Zarian wurin Rahma to tabbas zai biyo wurin ta ta biyo mishi Qur'anin, ba dai zakin murya ba. Da ke yanzu visiting lecturer ne a KASU da FCE zuwa zarian ba ya mishi wuya, Dan soon ma may be ya fara na ABU.

Bayan karatu, akwai shakuwa da ke ta kokarin shiga tsakanin su domin ko ba tantama yanzu sun sake da juna. Yayi nasarar nesan ta ta daga dukkan friends inta duk da ba Wai gabadaya sannan ya na yawan Jan hankalin kan dressing, ga azumin litinin da Alhimis da shi ma ta ke yi yanzu. Sai a lokacin ya fahimci komai na duniya a hankali ake bin shi da lallashi ba Wai dole ba.

Katsina, Nigeria.

Zaune ta ke tayi jugum tana kallon Arif da ya sa ta gaba da tmby "Anty yaushe Daddy zai zo in koma school" tausayi yaron ya ba ta yanda aka datse mishi mkrnt duk yanda ya ke son ta. Karon yaran na farko kenan da su ka zo katsinan Amma nan da nan su ka Saba da kowa. Daga Najib har Fadila ba Wanda ya fada ma iyayen na su abinda ke faruwa, sai dai kallo daya za ka ma Fadilan kasan akwai matsala ga cikin jikin ta ya fara nuna wa, shiyasa ma ba inda ta ke zuwa ko gidan baffa see da kyar ta ke iya fita. Zuba musu ido kawai su kayi su ga me suke nufi, domin ko tun da ya kawon su duk weekend yana garin. Ya dinga siyayye kenan yana yan kame kame.

Wani weekend ne Asmau ta zo garin bikin Neighbors insu shiyasa ma ba ta samu xuwa wurin Aminiyar ta ta ba saboda haka ita Fadilan ta shirya zuwa.

Maroon arabian gown ta sa da ya Sha aikin stones, da ke abaya ne mai fadi sam bai kama jikin ta  ba shi yasa ma ta dauki veil kawai tayi rolling da bag inta. Ta riga ta sanarwa Ummin kuma ba daman ba ta gida da ke ita ma ta je bikin. Yaran ta ke nema ta Kai su gidan baffah sannan ta wuce. A falo ta ji hayaniyar su saboda haka Kai tsaye ta nufi can ga mamakin ta suna jin Daddyn nasu suna ta mishi surutu. Kallo ya bita dashi, a daddafe ta gaishe shi yace "Ina zuwa?"

"Gidan Mama Aisha" ta fadi tana kallon kasa

"Ba tmby?" Shiru tayi ba tace komai ba don haka yace mu je mu sauke ki, ba musu ta bi bayan shi ya dauki ilham ya riko hannun Arif da ke ta mishi surutun school. Surutun yaran ke ta tashi har su ka isa goruba road. Ganin gidan shima da jama'an yan bikin ya sa bai shiga ba. Ya dai ce Mata "anjima zan zo in dauke ki, zamu yi magana" nodding kawai tayi ya koma da yaran.

Ba ta iske Asmau a gidan ba sai da ta Kira ta. Da gudu ta shigo gidan tayi gun Fadilan, sai dai tana ganin kawarta ta tayi turus jikin ta yayi sanyi. A sanyaye ta ce "ke ba dai laulayin cikin bane ya sa kika koma haka?" Yanayin idon fadila kadai ya sa ta shakkun hakan. Rau rau tayi da idanu tace "haba Fadila me ye sa ba zaki fada mun damuwan ki ba?" Kaman ko an ingizo ta ta fashe da kukan. Tare su ka Sha kukan su su biyu sannan Asmaun ta samu courage in lallashin Fadila.

A hankali ta warware mata dukkanin damuwan ta unknown to them gabadaya a kunnen mama Aisha aka yi. Ba ta boye musu domin yanayin fuskan ta kadai ya tabbatar musu taji komai. Ta shigo daukan abu a falon Abban ta window taji komai da ke can dakin Mama da ke side in su ka nufa saboda mutane.

Dukkan su biyu mama ta hada ta ma wa'azi sannan ta juya da Fadila tace Mata "Najib na da lafiya Amma kema kina dashi sosai" da mamaki su ka bi maman da kallo "Tabbas ko za ki iya fada min wani mataki kika dauka a matsayin ki na mace domin karkato da hankalin mijin ki gare ki? Musamman yanda kika gane weakness in shine yaran shi, dasu sumayya ke amfani ta samo lagon shi. A siyasance za ki damko mijin ki gare ki kuma ba za muyi naki ba ko nashi gidan mijin ki za ki koma Fadila domin ko matsalar ku kadan ce. Da ace yau dukan ki yake ko yawan zagi musamman ga iyaye ko kuma ba ci ba Sha ko sutura duk zan fahimta Amma wanna dalilin to fa can in shine rufin asirin ki. Tunda har kika riga kika yi aure to fa kinfi karfin zaman gidan iyaye sai dai in ba yanda mu ka iya ne. Ki saurare ni da kyau domin ko ba kunya tsakanina da ke a yau." Hanyoyi da dama ta zauna ta fahimtar dasu sosai domin a cewarta ba ta cire Asmaun ba tunda ita ma auren za tayi. Kunya su ga dinga ji ita ko maman share su tayi domin a ganin ta hakan ne mafita gare su.

Sai bayan magreeb Najib ya dawo daukan ta. Har falo ya shiga gaida mama Aisha tace mishi "Yauwa daman ko ba kazo ba zan aika a Kira min Kai." Nan ta ke ya Sha jinin jikin shi.

Murmushi tayi tace "malaman Najibu kenan shin har yaushe za ka tsaya sha'anin aure na zame maka matsalar? Na ji abinda ke faruwa kuma bai min dadi ba. Saboda meyesa don kawai kun samu matsala za ka dauko ta ka maido ta gida kace ka hakura, shin dole fa sai ka kara wani auren kuma tabbas sai an samu wani matslan ko so kake a fara kirga ma ka aure?" Girgiza Kai yayi yana shafa gemu. Tace "to shi matsala in ya taso facing in shi ake a warware shi ba wai a gudu mishi ba, binka zai yi tayi. Sannan maganan yara, shin in ba ka gode wa Fadila ba bai kamata ka daina ganin kokarin ta ba. Wacce mace a zamanin nan za ta daukan maka Yara tun tana Amarya ba ta cika wata daya ba. Ko Dan kana gani yar uwar ka ce? To bara na fada maka, a zamanin nan da mu ke ciki ko kanwar sumayya ce Uwa daya Uba daya ka aure ace yau ba sumayyan tou wlh ba za ta rike maka Yara haka ba. Ka samu mace mai hakuri ka San yanda za ka tafiyar da ita kar ka sake ta kubce Mata. In ba ka sani ba iyayen naku gabadaya ido su ka sa maka su ga me kake nufi na kawo iyalan ka gida ka bar su, shiyasa ba Wanda ya maka magana. Ko kasan bakin cikin da mahaifin ka ya shiga akan abin nan balle kuma Baba kabeer sannan a gangaro zuwa ummi. Su na fa son yar su Suka dauka su ka baka. To wlh kar inji ko in gani" warware shi tayi ta tas, ko bakomai ya samu relief jin wani ya tanka a cikin iyayen nasu. Kusan makasudin zuwan shi Katsinan kenan daman ayi ta ta kare. "Nagode mama daman dalilin zuwa na kenan in koma dasu domin na zauna na yi ma kaina fada na gano gsky"

"Da dai yafi maka, sai kaje ka saku baffah domin daman shi ya hana kowa magana but let me warn you ka je a shiryan ka" Nan ta ke gaban shi ya fadi domin sanin rikicin tsohon. Ko ya zasu kare.

A hanya ya ke ta kallon Fadilan, can ya kasa shiru yace "Sannu ko ba abinda ke damun ki?" Da mamaki ta kalle shi sannan ta girgiza Kai. Yace "muna komawa kaduna za ki fara zuwa awo in Sha Allah"

Da mamaki ta kalle shi a hankali tace "kaduna kuma?" Gyade kanshi yayi yace "Yeah Fadila i need that favour from you, I promise you komai zai canja" saurin girgiza kanta tayi tace "Ah ah brother don't promise what you can't do"

Yace "i mean it this time around" wani kwalla taji yana kokarin zubo Mata sai dai suk son ta hanashi ta kasa tace "I Know You didn't love me and you will never do. So please let me have the baby and then move on with my life"

Ajiyan numfashi yayi yace "har na aure ki Fadila banji wani abu a kan ki bayan yan uwan taka haka farkon zaman auren mu but believe with time komai ya fara canjawa, i keep denying it banyi realizing abin babba bane sai da na maido ki gida. Please Fadila ki yi hakuri mu gyara zaman auren mu wlh yanzu ina son ki and i mean it" kallon shi ta ke tana mamaki gabadaya idon shi ya rikida yayi ja yayi wani kallon tausayi. Hanky ya dauko yana goge Mata kwallan idanuwan ta yace "stop crying over me in Sha Allah ya kare daga yau."

ABINDA KAKE SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora