Nannauyar Ajiyar zuciya Ummi ta saki bayan ta gama sauraron abinda Mukhtar ke fada ma abokin sa Yusuf a waya. Ba kowa a gidan tana son ta aike shi kasuwa shiyasa ta je side in nashi da kanta sai dai kafin ta kai da yin sallama ta ji bayanin da ya ke ta faman korowa a waya. Zufa ta share tana mai Neman mafita. Tabbas ba zata bari mukhtar ya jawo mata magana ba. Murmushin karfin hali tayi sannan ta mai sallama ta fada mai sakon NATA. Tana komawa falo ta fara neman numban Asmau sai dai kwata kwata ya ki shiga, ba tare da sake tunani ba ta danno numban Mama Aisha aiko nan da nan shi din ya shiga.
"Ina yata?" Ta bukata bayan sun gama gaisawa.
Dariya mama Aisha tayi tace "Ummin Yara yar nan naki fa ina ga sai kin zo biko, kinsan yanzu mutuniyar ta ba ta nan"
"Aa ba za muyi haka ba, INA kewar ta tayi hakuri tazo in ganta"
"Ina ruwan Asmau yau gabadaya ma ranta a bace ya ke don Fadila ta kirata ta sanar da ita Najib ya sa an mata transfer a KASU za tayi karatu"
"Allah sarki kinsan sabo barin ma irin na Fadila da Asmau ina ji nima ita ta fado min. Yanzu dai ki turo min ita yanzu Dan Allah zamu tattauna" siririn murmushi mama Aisha tayi tace. "Tou shknn Ummin Yara yanzun nan za ta taho."
...
Mukhtar sauri ya ke tayi ya gama da sakon Ummi ya samu ya biya ta wurin Asmau saboda akwai tattaunawar da ya ke so suyi da ita.
Asmau ko shiryawa ta ke a ranta tana tunanin dalilin da yasa Ummi ta ke son ganin ta. Tabbas tasan cewa ba irin kiran nan bane da ta ke mata saboda kawai tayi kewarta. Nan da nan ta gama shiri ta dauki Hijab inta. Dai dai sanda ta ke taran napep a bakin layin nasu taga wata mota ta Shiga Layin nasu kaman ta Mk. "Hajiya INA zamu?" Maganan me napep in ne yasa ta waiwayo daga kallon da ta ke. Napep in ta shiga ta sanar mishi layout za ta.
A kitchen ta iske ummi da kannen Fadila mata suna taya ummi girki. Faran faran su ka gaisa da Ummi har ta danji sanyi a ranta, ta bukaci ummin ta bar girki ta mata "Aa Asmau zo ke magana zamuyi ki bar su Amira su karasa girkin ai sun iya" wani faduwar gaban taji, da kyar ta samu ta dake bai nuna ba a fuskanta.
Jan ta tayi har falon Abbah da ke bai gari shiyasa ta jata can saboda ba ta bukatar wani ya jiyo su. "Asmau me ne ne matsayina a wurinki?" Tambayar da ummin ta mata ke nan da nan ta ji gumi ya fara tsatsafo ma ta. "Mahifiya" Asmau ta bata cikin rawan murya. "Kwantar da hankali ba wani abu bane sai ma alfarmar da na ke nema a wurinki" shiru ummin tayi tana kallon yanayin Asmaun. sai da shirun ya ratsa na sakwannin sannan ummi tace "Ban San miye sa kika canja ra'ayinki akan Umar ba Asmau sai dai ina ganin hakan yana da alaka da tsakanin ki da Mukhtar" kan Asmau a kasa tana sauraron kala ba ta iya cewa sai ma numfashin da ta ke fitarwa a hankali. "Hakika Asmau na dade ina miki sha'awar Mukhtar tun dukkanku ba Ku kai haka ba sai dai rashin faruwan komai a tsakanin ya sa na sare har Umar ya zo yane Neman ki. Na yi farin ciki sosai da hakan ganin Umar in ma da ya ke a wuri na kaman yanda da ke da Mukhtar in kuke sosai. Zan fi kowa farin cikin alakar ki da Mukhtar Asmau saboda dukkanku na san Ku cike da baiya haka kuma ban shakku akan tarbiyyan da na baku sai dai kash! Ba ki tunanin in aka yi haka ba ayi wa Umar adalci ba? Umar Dan dan'uwana ne da ya ke matukar girma Mani ya ke min kallon mahaifiya. Ya rasa mahaifiyar shi tun bai San waye shi ba, UMAR mutum ne mai juriya, hakuri, hankali da sanin yakamata. Ba tantama na San zai rike min ke amana fiye da Mukhtar ma saboda ya fishi hakuri da fahimta. Kiyi hakuri Asmau ki min alfarmar nan ki koma ga Umar Ku dai dai ta tsakanin Ku na miki alkawarin samun farin ciki a tattare dashi domin banda shakku akan sa shima tarbiyya tace kaman Ku. Bayan haka ma kowa yasan maganan ki dashi ba kya ganin in muka ta ke duniya za ta zage mu? Umar Amana ne a wurina Asmau ban zan so abinda zai taba shi ba. Za ki min wannan alfarmar?" Cikin muryarta mai yanayi da tana daf da sakin kuka ta furta "Ummi ko umurni kika bani zan bi dole balle kuma alfarma, kin fi karfi wannan a wuri na" da kyar ta iya kai karshen zancen saboda kukan da sarke ta. Jawo ta Ummi tayi tana goge mata hawaye "nagode Asmau tabbas da wani kika samu ba Mukhtar ba zan yi kokari in fahimtar da Umar in amma yanzu tabbas duniya za ta zage mu" gabaday jikin Asmaun yayi sanyi sai ma wani azababen ciwon kan da ya rike ta saboda kukan da tayi. Abinci ma ummin ta sa ta gaba taci tasha magani sannan tace ta kwanta ko zata samu bacci. Kwanciya kawai tayi amma batun bacci kam kwata kwata babu shi. Tana jin shigowar Mukhtar har ya ba Ummi sako. "Ummi Asmau ba ta zo bane?" Hade rai Ummin tayi tace "tana bacci" dole yayi shiru saboda ba bakin magana ganin yanda ta amsa shi.
Bangaren Asmau ko ba ta taba tabbatar da tana son mukhtar ba sai ranar. Gabadaya duniyan juya mata yake domin gabadaya bacci ya mata kaura a ranar. Kiri kiri Ummi ta ki su hadu ranar da kanta ta mai da Asmaun gida. Kirjin ta wani irin zafi ya ke mata, ranar dai da zazzabi ta kwana tana ganin kiran Umar da shi kanshi Urban gayyar Mukhtar amma ta kasa dauka. Sai dai ta dau aniyar cikawa Ummi burinta na auren Umar ko da ba ta so domin Ummin ta mata abinda mahaifiyar ta bata mata shi ba.
Kanshi sunkuye gaban Ummi yana sauraron ta har ta kai aya. Sai dai abinda ba ta Sani ba ya dade da daina fahimtar abinda ta ke fadi sakamakon halin da ya shiga na rudani da firgici "ban son cin Amana Mukhtar kar ka manta Umar fa dan uwanka ne" abinda ya sauka kunnen shi kenan. Dagowa yayi ya kalle ta ta yanda za ta fahimci halin da ya ke ciki "Ummi wallahi ba cin Amana ba ne, na dade ina son Asmau tun kafin ta san wacece ita kinga ko hakan ba cin Amana bane la'akari da na dade da abun a raina ta tun kafin ma ya San Asmau. Har ga Allah Ummi ban San akwai wani alaka tsakanin su ba sai dawowa ta lokacin bikin Meenah. Ummin ki min rai banji zan iya rabuwa da Asmau banjin zan iya bar ma wani ita" hararan shi ummin tayi sannan tace "an gaya maka ban son tsakanin Ku da ita ne mukhtar? Nauyin bakin ka ya ja maka. Yanzu so kake ince Umar ya janye ya bar maka? To ban iya son kai ba dukkanku biyun daya ne a wurina"
"Ummi ban ce ki mai magana ba ki barni kawai in wa baffah magana kaman yanda nayi niyya"
"Ban Amince ba mukhtar tunda ba ka jin lallashi wannan Umurni na baka in kuma za ka kauce bismillah" tana gama fadi ta tashi ta bar wurin. Dukkan su biyun sun bata tausayi sai dai kash a ganin ta Mukhtar bai da gaskiya domin kowa ya riga da yasan akwai magana tsakanin ta da Umar duk Wanda ya ji dole yayi tunanin ita ta hada abin.
Rasa mafita mukhtar yayi gashi Asmaun ba ta daukar wayan shi balle su tattauna yanda za su bullowa abin. A in takaici washegari sai ga Umar a katsina ya na mai sanar da Ummi mahaifin shi yace yana so a tsaida magana domin a basu daman zuwa neman aure.
Author note: dukkanku na ga sakonninku kuma nagode sosai, Allah ya yi albarka. Game da updates please am sorry abubuwa ne su ka taru su ka min yawa but in sha Allah I will be squeezing. Nagode sosai.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...