Doctor Aliyu ya sako meema a gaba. Dan dole ta bari yazo ya ganta. Shiru tayi tana sauraron shi har ya gama koro bayanin shi.
"So ya kika gani? Nidai na yaba da hankalin ki, tarbiyyan ki da kuma natsuwan ki duka. Sannan kuma ni ba wasa nazo yi gun ki ba. Na ganki kuma kin kwanta min a rai so Ina bukatan ki bani dama in gana da iyayen ki in har kin amince"Shiru tayi kanta a kasa na yan minutuna kafin tace "Naji bukatan ka kuma nagode sosai sai dai kuma Ina mai baka hakuri domin akwai Wanda mu ka daidai ta dashi har na tura shi wurin iyaye na"
Kallon ta yayi na yan sakwanni yayi murmushi yace "Haleematu kenan, ki sani kafin nazo gun ki sai da nayi dukkan binciken da yakama ta tukunna. Kuma Ni iya bincike na ban gano akwai wamda ya je neman auren ki gun iyayen ki ba. Ki yi hakuri ki bani dama and i assure you, you will never regret it. Ko ban fada Miki ba kinsan ban yi kallan mazan da za su zo neman aure a hana su ba. Zan tafi Amma ki yi shawara, sai na kara zuwa."
A kufule ta shiga daki, Suhaila na ganin ta ta kwashe da dariya. "Wannan hade ran fa Anty meema? Sai kace dole aka Miki ki fita?"
Tsaki ta ja tace "dole ne mana, to in ba dole ai yasan shi lecturer dole ya sani abu in yi don't rabu lfy"
"To Wai ke miye matsalan shi fisabillilahi?" Hararan ta tayi tace "ba matsala ba matsaloli dai. Kinga na farko, yana da aure da Yara biyu sannan na biyu ba wai soyayya ta ya ke nema ba burin shi kawai in amince mu yi aure. Like he don't even sure an ounce of care on my interest and lastly, he is proud of himself. ai mutum ya bari a yabe shi ko?"
Dariya Suhaila tayi tace "wlh kina da ra'ayi mai tsauri sosai. Kinsan Allah a zamanin nan ba a wani tsayawa zabe. Fatan alkhairi kawai ake yi a shafa fatiha, ke kin sani."
"Kowa ma alkahirin ya ke nema Amma Ni ba zan auri Wanda bai damu da ra'ayi na ba sai nashi kawai za abi. Ina ba zai yiwu ba, I have a lot of plans for my life ai sai yayi shattering in su gabadaya. Na fi so na auri namijin da in nace Ina son zan yi abu kaza zai bani go ahead kawai. Ban son mai tsauri da ra'ayi, ba zai yi wu ba. I need a free life"
"Tabdijam, Allah ya zabo mafi alkhairi dai"
...
To haka dai rayuwan ta cigaba da tafiya. Yau Dadi gobe rashin ta. Bangaren meema Dr Aliyu ya sako ta a gaba sosai sai dai ita ma ta ki bada fuska duk nacin shi haka shima din yaki hakura. Gashi ba daman guje mishi Amma ita burin ta ta samu ta gama year in lafiya tasan yanda za tayi ta tsige shi cikin sauki.
In muka juya bangaren ma'auratan to fa sai dai muyi hamdalah domin dukkan su suna zaune lafiya sai dai dan abinda ba a rasa ba. Anyi auren zahra. Najib har gomben ya Kai Su fadilah, daga ita har babyn ta gata su ke gani ta kowani fanni. So kan su dangi yanzu hankalin kowa a kwance don a ganin su yanzu ne Najib yayi aure. Kowa zai shiga gidan shi ya fita sanda ya so cikin karamci da mutuntawa.
Yan Uk kuwa, zamu iya cewa Karen su suke ci kawai babu babbaka. Soyayya sai abinda yayi gaba, zuwa yanzu sun riga sun tabbatar they are meant for each other. Ya kan yi tafiya yayi 2 days watarana har week ma abinka da matukin jirgi Daman zaman zai yi wuya. Amma da ke akwai kyakyawan fahimta tsakanin su ba ta dauki hakan a matsayin wani matsala ba sai ma tattara hankalin ta da tayi ta maida kan karatu kocakam.
Bangaren Suhaila da malamin na ta kuwa shiru kake ji babu wani motsi. Ganin Exams da ke gaban ta ya sa ta zubda ta mai da attention kan school in sosai. Duk wani saurayi daman tuni ta watsar sai ko prince da ya zame Mata karfen kafa.
Zaune ta ke a class in su day yamma tana duba Exams in da za suyi washegarin ranar. kwata kwata ba ta maida hankali akan wadanda ke ajin. Hakan yasa ba taji sallaman da ake mata ba sai dai buga desk in da aka yi. Dagowa tayi ta kalla Wanda ke kokarin dauke Mata hankali. Kallo daya ta ma yarinyar ta sauke idon ta.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...