Babi na daya (01)

3.6K 177 0
                                    

Babban gida ne sosai da aka mishi ado irin na mutanen da. Amma Kuma a kayate ya ke da furanne ko ta Ina daga waje har cikin gidan. ya kunshi sashe Uku a jere in aka hada da na Mai gidan ya Kama hudu kenan sai Kuma sashe daya da aka ajiye musamman don Baki kawai.

Alhaji Abdullahi Malumfashi Babban mutum ne da aka mishi matukar sani a cikin jahar katsina da ma kewaye gabadaya, Kai ko kwatancen Unguwan da ya ke za ayi to tabbas da gidan shi ake yi. Ba komai ya jawo hakan ba sai dan kasancewar shi shaharraren Dan kasuwa da Allah yayi wa ruwar arziki tun yana Dan saurayin shi ya baro Malumfashi gun wan baban shi da ke Nan cikin katsina. yayi suna ba kadan ba.

Allah ya azurta da yara da dama har manyan su kayi aure su ka haihu ba a daina haihuwa cikin gidan Alh Abdullahi ba domin kasancewar shi Mai son zuri'a sosai. Har ma cikin jikokin nashi akwai wadanda su ka girme yaran nashi.

Duka gidajen Yara mazan a jere yake sannan wasu na Kallon wasu, duk da akwai Wanda ba garin su ke da Zama ba Amma duk da haka Alhaji Abdullahi sai da ya musu gini saboda su sauka in sun Zo garin. Ko kadan ba sa wasa da zumunci tun suna kanana su ka taso da hakan saboda tarbiyyan da mahaifin su ya daura su a Kai. Yawancin hutu a katsina su ke dawowa su yi ko basu so ba zasu turo yaran nasu.

A takaice da kullum gidan cike ya ke da mutane. Yaran, jikoki, Yan uwa da abokan arziki gabadaya. Hakan ne ta kasance a Rana irin ta yau sai dai wannan ma ya zarce na kullum. duk girman gidan Nan sai da aka yi occupying in shi a sanadiyar auren Yar shi mace da ake yi wato Aminatu. Biki ake na gani na fada irin na manyan mutane masu fada aji a kasa. Amarya dai sai dole gidan Babban yayansu Kabeer ta tare da kawayen ta saboda gidan nasu ya cika dam kuma yafi kusa da gidan su. Jikokin gidan ma yan Mata duk suna tare da ita don ko sun kasu kamo ta da kadan za ta girme musu.

••••

Sauri sauri gudu gudu Fadila diyar baba Kabeer in ta shigo tana kwalawa Asmau Kira wacce ta ke diya ita Kuma ga Mami Aisha babbar dakin Hajiya fulani. Suahila da ke kusa da Asmaun ne ta ja tsaki tana fadin "Deela Miye Haka sai kace ba Yan Mata ba?"
Gabadaya kwashewa da dariya su ka yi har da Amaryar, inda ta ke fadin "Yan ya'ya' na Kun girma"

Meema ce ta kalle ta cike da mamaki "Kai Anty meena sai dai kace Kinga yarintan mu, I think mommy cewa tayi da 2 years ki ka girme ni su Asmy kuwa 3 ko ba Haka bane"

Hararan ta Aminatu ta yi tana fadin "oho dai ko ma miye ku dai Ya'ya'n yayyina ne"

"Ku bar wannan maganan tukunna" Fadeela ta katse su "Asmy kinsan me? Ya MK ya dawo"

"What? Allah ya sa ba Wasa kike ba right? Shine ko ya fada min"

"Wlh am not lying a waje na gansu tare da su Ya Muhsin da Ya Faisal har ma mun gaisa" Ai Asmau ba ta jira karshen zancen ba ta figi takalmin ta da dankwali a hannu.

"Ke dawo dawo" Fadeela ta kwala Mata Kira "Ya Zaki fita Haka, Kinga mazan da ke waje har da Ya Umar fa" turus tayi Jin an ambaci ya Umar, ba lakka a jikin ta ta dawo ta zauna. Nan fa su ka hau Mata tsiya Wai Daga Kiran sunan Umar gabadaya jikin ta ya fara rawa.

Asmau da Umar da ya kasance da ga kanin Maman su Fadeela wato Matan baba Kabeer kenan. Soyayya ce tsaftataciya a tsakanin su, gabadaya iyaye duk sun sani Amma an bar maganan akan sai ta fara makaranta zuwa 200 level za ayi auren da ke shima Bai gama settling ba. Already ta gama secondary school tana jiran admission ne. Shakuwar ta da Mukhtar ko ya samo asali ne tun tana karama, yawancin hutu ta na gidansu da ke baban ta ma abokin baba Kabeer in ne don Haka zumuncin sai ya Kara kulluwa. Tun tana karama jinin su ya Zo Daya da Ya Mukhtar in nasu, ya matukar nuna Mata gata Wanda ya cigaba har zuwa yanzu hakan yasa ya samu babban wurin a zuciyan Asmaul Husna.

Tun bayan azahar aka fara Shirin kamu da za ayi a nan cikin gidan su Amaryar. Babban wuri ne sosai a ta gefen cikin gidan har ma yafi cikin asalin gidan girma. Wurin ya kayatu sosai yayi irin na al'ada yanda ya kamata sai ya saje da yanayin ginin gidan ya bada amazing colours sosai komai na gargajiya ne a wurin. Kawayen Amaryan ne su ka dauko ta zuwan wurin bayan an gama makeup su ko Ya'ya'n nata su ka biyo su a baya. Gabadaya Kan su a kasa su ka taho gudun kyara da ga gun yayyin su maza da ke waje, a cewar su zasu bada su gaban samari su dau kwalliya, gabadaya yayyin nasu miskilai ne Wanda da Basu daukan raini ko kadan, shi dama Ya Mukhtar Asmau kawai ya ke sakarwa fuska sosai, Ya Muhsin ko ustaz ne tuni ya tsare ka da wa'azi, Ya Faisal ko in za ka cinye kanka ko kallo ba Ka ishe shi ba, miskili ne sosai don ko cikin Yan uwan shi maza ba magana ya ke sosai ba ba uhmm ba Aa, Meema dai ta ce gidadanci ke damun shi. Sai Ya Najib shi ko fada gare shi sosai shiyasa su ke tsoron sa, Amma Kuma Yana da kirki over ma ga kyauta sai dai shi ko bikin ma bai Kai da zuwa shiru dai ake jin shi har yanzu. Su ne kadai Daman mazan babba cikin jikokin sauran duk Yara ne.

ABINDA KAKE SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang