Babi na talatin da shidda ( 36 )

1K 113 8
                                    

Wasa wasa har bikin Muhsin ya gabato, shiri ake gadan gadan ba Kama hannun yaro. Duk da Mami ba Wai maraba ta ke da bikin ba hakan bai hana ta yin hidima ba da kuma gayya kala kala. A cewarta ko su kadai ne dole su shana, shi dai Muhsin fir ya ki yarda da yin wani sha'ani, Mami ko cewa tayi ita kam sai tayi sai dai daga shi har amaryar nashi kar su halarta ba damuwan ta bane Amma ita kam ba za ta tafka abin kunya ba. Haka nan Muhsin ya zuba mata idanu domin ko mahaifiya ta fi gaban wasa.

Two days yo bikin mutanen Gombe da katsina su ka fara sauka Kano. Gida ya debi mutanen biki kam kala kala. har Yusuf da ke Lagos ma ya iso Amma ango bai gari yana can Abuja aiki ya rike shi dole sai ana gobe daurin aure zai samu dawowa. Don haka Faroukh abokin shi da su Najib da Faisal ya bari da aiki.

Su meema, Asmau da Fadila gabadaya suna kanon ana gobe auren. Wata yar karamar liyafa Mami ta hada a nan cikin gidan, kida ke ta faman tashi ba kaukautawa. Sai dai abin mamaki duk abin nan da ake Suhaila ba ta na. A cewarta akwai wani test in da aka musu fixing sai tayi za taho. Ba yanda Mami ta iya hakanan ta bar ta ba dan ta so ba.

4:30 na yamma Mami ta Kira ta a waya "hello yar Mami an gama test in ko?" Sanin in tayi karya mamin za ta gano ya sa tace "eh Mami mun gama"

"Then get ready za a zo a dauke ki, kin San no way a na biki ba diya ta"

Mami na kashe wayan ta Danna wa Muhsin Kira. A lokacin yana jaji zai karaso kanon. Gaban shi ne ya fadi jin irin kidan da ke tashi da ya dau wayan Mamin. "Haba Mami wannan kidan fa daga ina? Mami shi fa aure albarka..."

Tsaki ta ja sannan ta je "dakata min malam in dai ba Kai ka haife ni ba please, sannan ba wa'azi na Kira ka kamin ba. Kaje maza ka dauko min diyata a Zaria yanzun nan"

Nan ta ke yaji ranshi ya baci. Duk abinda ya ke ji akan Suhaila kwana biyu ta sane mai, tsab yana sane da irin party in da ta ke attending kwana biyun nan. Ya so ya ganar da ita sai dai hakan ya faskara shiyasa ma gabadaya ya fita sha'anin ta.

Samun kansa yayi da shararo karyan da ba halin shi "Mami na wuce Zaria since"

"Muhsin ka fita ido na kar ka sake ka dawo Kano ba Suhaila" tana gama magana ta kashe wayan. Dafe kanshi yayi cike da bakin ciki, Allah ya sani yana gudun abinda zai hada shi da yarinyar nan kwana biyu.

Ya ja tsaki har ba adadi kafin ya isa Samarun. A kofan apartment insu yayi parking sannan ya Kira Mami ya sanar mata yana kofan gidan su suhailan. As expected fada ta hau mishi tana fadin tsabagen girman Kai ne ya hana shi Kiran suhailan a way kenan, kala bai ce ba illa ma kashe wayan da yayi saurin yi. Abinda Mami ba ta sani ba shine shi gabadaya ma bai da numbanta a wayan shi ne kwata kwata.

Ta gama shiryawa daman so Mami na Kiran ta taja traveling bag inta da handbag ta nufi wajen. Motan shi kadai ta hango ta ji gaban ta na dukan uku uku, ba ta San cewa shi zai dauke ta ba saboda mamin ba ta sanar ma ta ba. Da kyar ta tattaro dukkan natsuwan ta ta karasa wurin. Ta cikin madubi Muhsin ya hango ta, hade rai ya sake yi ba alamin murmushi a fuskan ma. Sanye ta ke da kimono navy blue, ash jeans ne a ciki ta yafa karamin ash veil. Tabe baki yayi a cikin ranshi ya ke fadin ba laifi domin ko she is somehow modest, kimonon ya rufe mata shape in jikin ta gabadaya. Ganin tana dab da karasowa ya sa ya bude mata booth, ita ma tana gani ta saka akwatin ta rufe sannan ta karasa ta bude motan ta shiga tana kokarin controlling kanta. Ta gefen ido ta dan kalle shi haka kurum ta ji yau in ya Mata wani kyau na daban. Yayi kyau da ka ganshi kaga ango, shigan bakin jeans da shirt yayi da ke farin mutum ne sai ya karbe shi sosai. Ga yayi aski da gyaran fuskan, gashin kan nan ya kara kwantawa haka sajen shi da ke shan gyara kusan ko yaushe. Duk a tunanin ta Muhsin bai acting kaman wayaye to fa ta tabbatar da cewa shi din dan gaye ne. Samin kanta tayi da gaishe shi "ina wuni?" Kaman daga sama ya ji siririn muryan ta na fadi, banbarakwai ya ji abun. Fuskewa yayi yace ma ta "lafiya, ki saka seat belt" ga mamakin shi ba tare da wani musu ba ta yi yanda yace in. Ya ja mota su ka bar layin. Hakanan ya ji kawai bai ji dadin yanda ya ganta ba gabadaya tayi wani sukuku kaman ba ita ba. Sam Sam bai Saba ganin ta haka ba, to kodai ba ta da lafiya ne? Suhaila kam yau gabadaya kasa fiddo wayan tayi ta dai durkusan da kanta kawai tana wasa da yatsun ta. A yanda ta ke ji abinda ke damun ta a ranar yafi gaban waya, kaman ta kurma ihu haka ta ke ji. Shin wannan wani irin jaraba ne?

"Baki da lafiya ne?" Kaman daga sama taji tmbyn. Shi ko Muhsin ka sa jurewa yayi ya tmby ta, domin ko bakomai yar uwar shi tun can daman halin ta ke hada su ba Wai don ya tsane ta ba.

Dum! Gaban ta ya buga, kar dai Muhsin ya fuskanci halin da ta ke ciki... In ko haka ne lallai ta shiga uku. Muryar shi ne ya kara katse mata tunanin nata "Ehmm tell me mana are you sick?" Mamaki ya fara bata, tunanin ta why does he cares, a sanin ta iya tsawon rayuwar su irin haka bai taba shiga tsakanin su ba.

"Kai na ke ciwo?"

"Kinci abinci?" Tambayan da ya wurgo Mata kenan. Sai a lokacin ta tuno kwata kwata ranar banda ruwan Lipton ba abinda ta Sha.

Girgiza mishi Kai kawai tayi Amma still ya kara tmbyn ta "why?"

"Lack of appetite"

Dan juyo yayi ya kalle ta sannan yace "that means you are sick kenan ko kuma akwai abinda ke damun ki ko stress, ai kinsan headache symptoms in illness ne right?"

A hankali tayi nodding kawai, tunowa da tayi shi in doctor ne.

"Me kike ganin zaki iya ci sai ki Sha magani?

Dan jim tayi kafin tace "am okay in nayi bacci ciwon kan zai warware"

"I disagree, you have to eat something ko da ko ba solid food bane" lallai Muhsin da gaske ya ke, haka kurum ta samu kanta da farin cikin kulawan da ya nuna a gare ta.

"Maltina is okay" ta fadi a hankali, nodding kawai yayi sannan yayi Parking a wani suya spot ya fita.

Nylon biyu taga ya fito dasu a hannu. Sai da ya fara driving ya mika mata yace "ki daure ki sa wani abu cikin ki ba kyau zama da yunwa" godiya ta mai a hankali ko amsa ta bai yi ba. Haka Muhsin ya sa ta a gaba dole sai da ta shanye gwangwanin maltina daya da kuma hadadden balango da ya siyo mai romo. Sanin ta tun tana karama in bata da lafiya nama kawai ta ke iya ci cikin dadin rai ya sa ya siyo mata. Sai da ya gamsu cikin ya dauka sannan ya mika mata magani, kaman ta yi amai haka ta hadiyi maganin tana bata fuska. Dariya ma ta bashi, don ko ita gwara a mata allura akan a hada ta da magani, Sam ba sa jituwa.

Dan kulawan da Suhaila ta samu gun Muhsin ya sa ta samu relief, daga baya tana ji Rahman shi ta Kira shi tana tmbyn har yansu bai iso ba? Ya sanar mata sun kusa isowa, yanda kadai ya ke ba Rahman kulawa ya isa ya tabbatar Mata da ba karamin so ya ke ma amaryar ta shi ba. Tabbas ta na cikin wani mawuyacin hali, yanzu kam ta fara saukowa daga tunanin ta na cewa zubda aji ne ma a ji har tana da wani feelings akan Muhsin saboda shi ba wayayye bane. Muhsin is civilized and exposed fiye da tunanin ta sai dai shi in yana kokarin kiyaye dokokin Allah ne sannan kuma yana da na shi tsare tsaren da ya Sha ban ban da na ta. Abu daya za ta iya yima zuciyan ta ta samu sassauci, shine kuma amincewa da abinda ke addabar ta. To tabbas ta amince Sai dai kuma tana mai haramta faruwan hakan. Ko bakomai ba za ta so ayi mata dariya ba.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now