Babi na sittin da uku ( 63 )

1K 97 15
                                    

Florida.

Zuwa yanzu gabadaya ya fara gajiya da lamarin. Sai dayawa ya kan Kira Ummi akan ya bata hakuri kilan hakkin ta ke bibiyan shi Amma da ya kirata sai ya kasa. Kaman Kashi da rai haka ta koma. Yusuf ya fuskanci halin da ake ciki ko da Mukhtar ya warware mai komai gabadaya kan shi kullewa yayi. Gashi halimatu ta je gida haihu balle lamarin ya zo cikin sauki. Shi da kanshi ya Mata nasihan but it all seems futile. Hawaye ko har ya kare Mata yanzu sai kukan zuci. In ta dauko kayan babies in da ta siya ta sa a gaba. Duk mukhtar sai da ya tattara ya zubar. Ai ko ranar ya ballo wa kanshi don sabuwan rigima ta tada. Da yaji labarin sa auren Muhsin da Suhaila har tunani yayi ko shima kara auren zai yi maybe ya samu sauki. Da ya gayawa Yusuf ne yaki ba shi goyon baya domin ba maslaha bane.

Yau da ya shigo ya same ta kaman kullum. Zama yayi a gaban ta yana mai fuskan ta. "Please please Asmau Mai kike so in Miki ne Wai? Abin Nan da kike fa kaman butulci kike ma Ubangiji tunda shi ya baki kuma ya amshe abin shi"

"Ka maida Ni gida"

Da sauri ya dago yana kallon don ya tabbatar da abinda ta ke fadi.

"In da a can nake am very sure ba za a bar ni in jigata ba har nayi loosing baby na. Kazo ka ajiye ni inda ban da gata ban San kowa ba. At times sai kayi one week ba ka Nan"

"Asmau ta ya zan maida ki gida bayan ni Ina Nan? Remember we are married. It can't work that way."

"I can't leave here anymore Ni ka maida ni gida. Quit the job if you want to be with me in ba za ka iya ka maida ni gida i can cope even if you are coming once a year in Kai ba za ka iya then let it be over" a firgice ya dago yana kallon ta. Nodding kan tayi tace "I loose the baby so am not afraid to loose anything after that. You have to choose Ni dai in all the conditions i want to be at home" wani zufa yaji yana tsatsafo mishi. Da sauri ya tashi ya bar wurin yana tuna farkon auren su yanda Ummi tayi ta mai nasiha Kar ya ga Asmau tana son shi yayi using opportunity in ya cuce ta. Unknown to her ita yanzu ke using opportunity in tana wahalar dashi. He loves her to much for him to let her slide that easily.

Da yaga wa Yusuf yanda su kayi da ita ce mishi yayi "Ka maida ta gidan. In ba za ka iya rabuwa da ita ka lallabo ta daga baya Amma yanzu she needs fresh air." Tsaki Yusuf ya ja yace "Allah ya gani ba zan boye maka ba matar ka na bata min rai. Is it because you madly love her or what sannan Kai musamman kana bata min rai. Ta ya za ka bari mace na juya ka yanda ta ga dama. Kan ka aka fara so? You need to man up and find your self a solution please"

Ko da ya koma gidan ya iske ta tana hada kaya. Kasa ce mata kanzil yayi ya fita ya bata wuri. Zai mata abinda ta ke so since it her choice.

Da ke wahalan shi ya zo karshe. Yana planning musu tafiya Nigeria cikin week in Najib ya Kira shi zai shigo Florida shi da Fadila washegari. Ta rako shi wani trip New York so she insists tana son ta zo taga Kawarta. Bai ma iya fada Mata me ake ciki ba. Sai dai Kwatsam washegari ta ga Fadilah a gidan ta. Ya riga ya shirya zuwan su, ya sa an gyara falon da dakin da zai sauke Fadila because Najib zai barta for two days kafin ya dawo su wuce.

Shi ya tarbe su a falo ya amshi babyn yana murmushi sannan ya shiga dakin ya same ta tana abinda ta saba. "Fadila tazo" waro idanu tayi tana kallon shi because ba ta yarda ba. Babyn da ke hannun shi ta bi da kallo. Sai da taji Fadilan tana Ina matan gidan ta ke ne Wai? Da sauri Asmau ta Sa wani hijabin ta. In ka ganta tayi shiga mai Dan kyau tou school taje. Shima daga baya daina zuwa tayi.

Saurin karban babyn tayi tana kallon ta cike da so da kauna. Tuna cewa da yanzu it ma ta kusa samun nata yasa ta kwalla. A fakaice ta goge.
Faran faran su ka gaisa da Najib yana tsokanan. Bai wani dade ya tafi, Asmau tayi mamakin special sallaman da taga sunyi da Najib in har yana tsokanan ta ko za ta bar kawarta tane ta bishi. Ita dai Fadila tun tuni ta ke kallon Asmaun ta na kallon yanda ta rame sai kuma wani zuciyan yace Mata maybe ciki ne da ita. Sai da Najib ya tafi su ka shiga daki. Kuran da ke dakin kadai ya isa sanar da ita ba lfy. Kallon ta tayi tace "Kawata miye haka na ke gani? Ba dai In da kike kwana ba ne Nan?" Dakin Asmau tayi da kallo. Ita har ga Allah sai lokacin tayi realizing abin yayi worst haka. Kakalo murmushi tayi tace "long story bara nayi wanka" ai kallo bai tashi ba sai da ta cire hijab in. Sakin baki Fadila tayi tana kallon ta "ke baki da lfy ne? Wani cuta ke damun ki haka? Ina Ya Mk lfy ya barki haka?" Duk a rude tayi tmbyn don ta tabbatar yanzu ba wani ciki.

Saurin shiga wanka Asmau tayi to avoid the talks. Ko kafin ta fito Fadila ta fara tattara dakin don haka tana fitowa ta sa hannu su ka karasa. Sauran gidan Fadila tabi duk sai a hankali hakanan su ka karasa gyaran. Ita dai Fadilan jira ta ke Mukhtar ya dawo ya fada ma ta me ke faruwa domin kuwa Asmau ta kasa cewa komai da ta matsa Mata sai kuka. Kitchen kam Daman kwaleman shi daban su kayi.

Da ya dawo tun daga kofa ya gane yau an samu canji ko daga kamshin turaren wutan da yaji a falo. Bayan sun ci abinci. Fadila ta same shi tace "Ya Mukhtar we need to talk" da sauri ya amsa tunda Daman jira ya ke. Ita ko duk tayi la'asar. Kaman ta girme su haka ta zaunar da su a falo tace "Ya mukhtar me ke faruwa na ga Asmau duk ta kare haka. Akwai abinda ke damun ta ne kuke boyewa?" Girgiza kan shi yayi yace "ba abinda ke damun ta Fadila. Ba ta gaya Miki abinda ta daura wa kanta ba ne?"

Da sauri Asmaun ta kalle shi tace "daura ma kaina nayi ma ko?" Nan da Nan sai hawaye. Ita dai Fadila kara shiga confusion tayi tana kallon su both.

Tsaki MK ya ja yace "look Fadila you are her friend maybe ke in ki Mata magana ta dauka" Nan da nan ya warware mata duk abinda ke faruwa.

Rike baki Fadila tayi tana kallon su. Lallai a bar so. Daman yanda Ya Mk ya ke mace za ta iya mai abun Nan ya kyale? Kallon shi tayi tace "Haba Ya mukhtar shine ka kyale ta ta ke abinda taga dama?

"Au kema bayan shi zaki bi? Ko da yake Daman what am i expecting you are his blood sister dole ki nuna min..." Wani irin harara Fadila ta aika Mata Wanda ya sa ta yin shiru.

"Wai Asmau Daman ba ki da hankali? I thought you are the smartest one between us. I always looks up to you ashe zaki ban kunya haka"

Juyawa tayi ta kalle shi "Dan Allah Ya Mk kayi hakuri zamuyi magana" nodding Kai yayi sannan ya tashi ya nufi dakin shi.

Kallon ta Fadila tayi ta ja tsaki "in kiga dama ki tashi mu tafi daki"

Bayan sun tafi ne ta kalli Asmau tace "don tell me you don't have explanation for it"

Kwalla ta fara yi tace "sorry Fadila i couldn't get over it that easily. The cravings to hold the baby, feed him and feel him. I was so happy having the baby, it means the world to me. Wlh Fadila ban taba jin kwanar Dan Adam ma kaman baby na da na rasa, a kullum Ina jin soyayyan shi na kara ninkuwa min cikin zuciya ta. I had all my plans, the name and everything. Amma Ina ji Ina gani na rasa abu mafi soyuwa a gareni ba yanda zanyi, no neighbors to run to, Husband not around. Nayi kokarin a ko wani hali in your saving in shi Amma bai yiwu ba. I feel shattered, broken and alone. Da na farka nayi tunanin Ya Mk zai tayi ni mourning jaririnmu Amma unbelievable he is trying to convince it gone. I mean he is already over it kenan? It can't be that easy i thought. Hakan ya sa nayi tunanin he never wanted the baby at all he is just pretending. Looking for what to bent my anger on so it end up on him" ta karasa zancen tana kuka mai cin rai.

Fadila ta ji tausayin ta sosai don har ita ma sai da tayi kwalla. She knows the feeling of having a child so loosing it won't be that easy "Asmau this isn't an excuse you know? Yeah na San it not easy haka kuma na san zanyi Miki zafi Amma shin Asmau kin manta Allah ne ya hallice mu kuma dukkan mu za mu koma gare shi? Ko ba yanzu ba Allah zai amshi abin shi. Wannan alama ce fa ta rashin yarda da kaddara. Mu sa abinda ya same ki jarrabawa ce daga Ubangijin mu tunda ya San kina son abinda za ki haifa kuma ya amshi abin shi. Kenan kin fadi kenan? Me kika yi kenan kin butulce mishi? Koma ban Miki nasiha ba ya kamata ki zauna ki wa kanki fada ki natsu ki San me kike yi. Ubangijin da ya baki wancan shi zai baki wani Asmau." Baki ta dinga bata sannan tace "in kuma kin ki ji kin koma gida to Ina Miki albishirin Baffa, Abbah, Ummi da Mamah wlh har baban daura na rantse Miki Da Allah sai na sanar abinda ke faruwa su ai daidai su ke dake. An gaya Miki mace ta koma rayuwa gidan iyayen ta bayan ta dandani zaman aure da sauki ne? Meyesa kika zawara na saurin kara aure. To wlh in ka wuce zaman gidanku ka riga ka wuce shi. Balle ke da Allah ya azurta ki da miji mai matukar son ki kuma mai saukin kai a lamuran ki. Ke da labari aka ban ya mk yayi hakurin Nan Allah ba zan yadda ba. Kuma a haka kike so ya mai da ki gida kaman skeleton? Ki wa kanki fada" tatas dai Fadila ta Mata ranar sannan ta koma ba ta baki. Sai gashi ta dan fara dawo hankalin ta jikin ta baki daya yayi sanyi.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now