Babi na talatin da tara ( 39 )

918 94 9
                                    

Abuja, Nigeria.

Sake baki mummy tayi tana kallon meema da ke ta faman balbale brother inta da masifa. "Kar ka sake min irin haka bana so"

"Sorry Adda Amma please ki daina wulakanta maza wlh ba kyau" za ta cigaba da fada mummy tayi saurin dakatar dasu. "Wuce abin ka ke kuma zo zauna ina da magana da ke" ba musu kowa yayi abinda mahaifiyar na su ta bukata.

"Halima shin kina da Wanda kika ajiye wa kanki ne ko kuma kunyi alkawarin aure" girgiza Kai tayi sannan tace "babu mummy"

"So now tell me your reasons na wulakanta kowa yayi approaching inki" shiru tayi ta kasa cewa uffan, tsaki mummyn ta ja sannan tace "seriously, this have to stop, am feed up with all your act, ce miki aka yi a gidan nan za ki dawwama ne? Final year fa zaki shiga bayan karatu me kike so kiyi" kallon maman nata tayi sannan tace "sorry mummy but ina da dreams in da na ke son inyi accomplishing before getting married. It can't be fulfil in har nayi aure"

"You are very stupid halima kuma ki kiyaye ne kina ji na" nodding kanta tayi "dreams in ki na banza an ce miki akwai abinda ya fi aure ne? Allah na baki within 3-5 months ki fidda miji in ba haka ko zan baki duk Wanda na ga dama." Dam! Dam! Gaban ta ya buga, da sauri ta tashi ta bar falon zufa na keto ma ta ta ko ina. She is done a tunanin ta kenan fa.

Gabadaya kwana biyun nan ta zama wani sukuku kullum tunani. Mummy na fahimtan halin da ta ke ciki da gam gam ta kyale ta. Brothers inta kuwa gabadaya ta hade musu rai don tana ganin duk su ke ja mata komai ma da su ke ba wa wasu numban ta har mummy ta ji suna case.

  Daddy in ta ne ya fahimci halin da ta ke ciki don haka ranar yana gama dinner ya aika a kirata. "Mamana lafiya me ke taba min ke ne kwana biyu?" Kaman jira ta ke ta saki kuka mai karfi. Girgiza Mata Kai yaya yace "Aa mamana ban ce kiyi kuka" hanky ya mika Mata ta share hawaye, sai da ya jira ta yi calming down yace mata "to yanzu yi min bayanin abinda ke faruwa"

Ajiyar zuciya ta saki "Daddy daman mummy ce ta ce Wai ta bani 3-5 months, I shall find a suitor" Dan dariya ne ya so ya kufce Amma ya danne.

"Ita mummyn tace haka?" Gyade Kai kawai tayi kaman za ta fashe da wani kukan.

A hankali ya shafa kan ta ya ce "don't worry kinji mama na, ki kyale mummy za muyi maganin ta" Dan sanyi taji. a zuciyan ta ke fadin "Daman na San Daddy ba zai goyi bayan mummy ba" Amma abinda ya fada next ne ya sa ta shock "tou Amma Mamana when are you thinking is the right time for you to settle down?"

Murmushi tayi alamun jin dadi tace "Daddy ka San me?" Ba tare da ta jira amsan shi ba ta cigaba da magana cikin zakwadi "I have plans and dream to be accomplished ne kafin nayi aure, in har nayi auren I don't think it will be possible kuma. I just don't want to loose the chances, I need to makes them alive" kallon mamaki ya bita dashi sannan yace "can you mention your dreams?"

"Yauwa Daddy ka ga Ina da plans sosai Eminent_delicacies, Ina son yafi haka sosai sannan I want to join Fashion designing da make up. Ina son Eminent_delicacies ya zamana the best in everything ne with different branches a countries ne, I want to even change the name ne saboda zai zama broad. Akwai bangaren make up, fashioned designing, A wide kitchen specialized in different kinds of international and traditional foods, snacks, drinks and everything ma. If possible har Interior decoration sai ayi establishing" attention ya bata sosai yana sauraron ta. He is so proud of her, yarinyar akwai basira ga entrepreneurship set of mind.

"Mamana kenan lallai kina da dream babba, Allah ya bada ikon cikawa."

Godiya ta mai sosai cike da murna ta wuce dakin ta ranar.

•••

Zaria, Nigeria.

Two weeks kenan da gama bikin Muhsin. tun dawowan Suhaila Zaria ba ta kara jin duriyar shi saboda haka sai tayi kokarin sa wa kanta salama, ta tattara hankalin ta ga karatu.

Fitowan ta Kenan library ta ga numba na Kiran ta. Kaman ba zata dauka Amma ta ji hankalin ta ya ki kwanciya kawai sai ta dau wayan. "Kina Ina ne?" Tmbyn da ya mata kenan bayan sallama, bai ma tsaya jiran su gaisa ba.

Ba ta needing wasi wasi domin kuwa ko sheshekan mutuwa ta ke ba tayi tsamman za ta mance mamalakin muryan ba. "Wurin KIL" ta bashi amsa.

"Bani 2 minutes zan iso please" kashe wayan yayi. Ai ko Two minutes bai wuce ba ya iso. Da ke sabon mota ne ya sa bata gane ba sai da ya kirata. Tun kafin ta karasa ya bude mata motan don haka tana shiga ya bar wurin.

"Ina wuni" kallon ta ya dan yi na sakwanni sannan yace "Ina zuwa tukunna, zamu isa wannan wurin but for now am hungry, suggest a best restaurant Amma ba cikin school inku ba" ita ma ta gefen ido ta kalle shi tace "Ban sani ba ko za ka iya cin abinci na, I have food at home"

"What do you cook?"

"Does it matter? Don't you trust my hand"

Murmushi yayi a ranshi yana dan mamakin yanda ta yi kokarin sakewa dashi haka. "You are a great cook i know, so mu je gidan" ba wanda ya kara magana har su ka isa. Fita tayi ta hado mi shi abincin, hadadden Dambun shinkafa ne da ya Sha kayan lambu da hanta a ciki ta hado da zabon ta mai sanyi. Sosai ya ci abincin Dan ko Suhaila ba karamar gwana bace a wannan fannin. Ba kasafai ta ke cin abinci a waje domin ko ta fi gane ta zauna ta sarrafa abinda ta ke so taci, yawancin ka ganta eatery toh drinks za taci sai ko su shawarama da yogurt ko ice cream.

"Allah ya saka ma Mami" abinda ya fada kenan bayan ya gama kwasan girkin.
Siririyar dariya tayi tace "yau kuma? Lallai ya kamata in ma Mami albishir"
hararan ta yayi "duk ba ke ke hada mu fadan ba"
"Ba ruwana"

kauda zancen yayi "Suhaila ba zan boye miki ba naga canji kuma naji canji ko da yake ma kafin nan why don't you call da zaki dawo school? Sai dai ji nayi kawai ba kya nan"

"You were no longer at home remember?"

"And so? You should have called me, like i really wanna talk to you"

Kallo ta bishi cike da mamaki sai kuma tayi saurin basarwa, for real Muhsin gabadaya ya canja.

Lokaci daya ta ga gabadaya ya canja ya shiga serious mood, sunan ta ya Kira ta dago ta amsa mai sannan ya ja numfashi ya fara magana. "Ina so ki wa zance na kyakyawan fahimta sannan kuma ki natsu ki saurare ni" ba ta amsa shi ba ya cigaba da magana.

"Kaman yanda na yi fata tabbas na ga canji daga gare ki kuma na ji dadin haka. sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, Sam ba a wa addini shigan sauri. Abu ne da ake zama a koya a San yanda za ayi shi domin bautawa ubangiji so dole ne sai ka nemi ilimi akan shi. Ke kuwa a iya sani na rabon ki da islamiyya yafi shekara goma, Kai duka duka ma ba ki wuce shekara biyu zuwa uku a cikin ta ba. Malamin da ke zuwa ko ba ku tsaya wa balle kuma Mami da ba ta da lokacin kanta. Ina miki sha'awar lada Suhaila sai dai kuma ba a addini cikin rashin sani. Wajibi ne cikin busy schedules inki ki ware wani time dan sanin addini ki, musamman weekend. Zan so in samu wannan ladan domin in ceto ki daga halaka a matsayin ki ta yar uwa ta, ya kike gani"

In tace ba taji wani iri ba to tabbas tayi karya don ko wani zuciyan na son fada ma ta tozarci ne Muhsin ya ke son mata sai dai mafi rinjaye na karya ta hakan. Musamman yanda ta ke ji akan shi, ko bakomai wani chance ne ta samu na ba wa zuciyan Abinda ta ke so.

A hankali tace "Kai kana Kano ni Ina zaria, can it be possible?"

"Kar ki damu da wannan, ai kina da waya. Za ma dai a samu solution kawai don yanzu in nace islamiyya na tabbatar ba wani attention za ki bada a wurin ba"

A hankali ta dago ta kalle shi.  yace "I know you Suhaila, so ki duba timetable inki ki turo min sai muyi fixing time tare ko"

"Ba zan takura ka ba?"

"Ina ruwan ki wai, June do what i say" murmushi tayi tace "in Sha Allah"

Yace "tou nagode da girki ko a fitan min mota" dan tabe baki tayi tace "mu ma Allah ya bamu"

"Ameen" ya amsa mata.

ABINDA KAKE SODonde viven las historias. Descúbrelo ahora