Babi na Ashirin ( 20 )

958 86 1
                                    

Gadan gadan aka fara bikin Fadila da Najib. Tun Asmau na dari dari da Ummi har ta saki jikin ta ganin ko kadan Ummin ba ta canja mata ba.

Tun ran Wednesday yan Kano, Kaduna da Abuja gabadaya su ka karaso sha'ani sosai ya kankama.

Amare ko dole nan gidajen da ke kallon layin gidan su su ka koma koma, inda gidaje kusan biyar ke jere a wurin sannan ta farkon layin ma akwai kusan Uku. Al'addan baffah ne tunda kan baba kabeer shi ke bawa yaran shi maza gida da sunyi aure said dai daga baya in basu zauna a garin ba suyi nasu, amma dukkansu kowa da nashi har ma ko da su khalipha, Aliyu da Abakar da ba su kai da auren ba akwai wurin su a ajiye. Mata ko kyautan mota da set in zinari ya ke ba ma kowacce, arziki kam akwai shi sai Sam barka.

Fadila ba taso barin gidan su ba amma haka Anties su ka sata a gaba dole ta koma nan gidan baba bello da matar shi ke amarya, ta na dai da tsohon ciki amma ba yara. A cewarsu za su fi walawa a nan in.

Kwatsam! Ba sai auren ya hade musu biyu ba. Neman aure baffah ya tura su baba kabeer neman wa Usman in dakin Goggo Fulani, wanda Anty meena ke bi ma wa. cewar shi gwara su je kafin biki saboda a samu daidai ta wa. Suna zuwa mahaifin yarinyar ya nemi da a daura auren kawai in na su Najib yazo, Abokin baba kabeer tun suna yara tare su kai taso shima Dan unguwan ne. Kwatakwata bai San Usman na neman yar shi ba, mita ya ke wa mahaifiyar ta kullum akan samari sun fara hure mata kunne daga shigan ta jami'a. Shi ma Usman lura da hakan ne ya sa ya matsa ya tura tun tana tirjewa har ta hakura amma da sharadin ba yanzu za ayi auren ba sai ta gama aji biyu. Sai ko ta sha mamaki saboda labarin da mahaifinta ke samu akan irin mazan da ta fara hulda da su, irin yara kanana ne masu hure wa mace kunne ba tare da tunanin aure ba kwata kwata. Usman na jin labarin shima ai ko hankalin shi ya tashi shi yasa ya matsa har aka je nan mahaifinta ya turje duk da su baba kabeer sun nemi ko wata a sa "zan iya siyan mata komai a kwana ukun da ya rage kuma nasan Allah ya wadata kam. Ba wani abun karya za ayi ba to miye na tashin hankalin, ni daku ai duk daya ne" a haka suka amince su kai tafi wa baffah da labarin. Usman ya ji dadi sosai, yana da aiki, gida da rufin asiri dai dai gwargwado to me yake nema da yafi nan? Sai dai yanda zai shawo kan Amaryar tashi ce domin ko yasan akwai daru amma wannan ba matsala bane a ganin shi in akayi auren shknn. Nan da nan aka hau shirin aure biyu, Dan ma na namiji ne so komai yazo da sauki.

Ranar Thursday su kayi scheduling cocktail party in Wanda za suyi a new katsina motel. Event in yan mata ne kawai ba maza kuma ba iyaye. Anyi decorating wurin yayi kyau sosai yayi matching da outfit in amarya da tayi in Burgundy and golden. Bride maids in kuma gabadayan su in mustard color straight gown su ka fito, sun yi kyau sosai.  Event in yayi amarshi, su suhaila anyi rawa son rai cikin natsuwa da kwanciyar hankali ta ke juya jikin ta, sai da ta burge kowa don dama gwanar rawan Ce.

Suna zaune a nan gidan Baffah gabadayan su samarin suna hira har da su khalipha, Abakar da Aliy. Usman ko gabadaya hankalin shi ba a jikin shi ya ke ba yana wurin Amaryar shi ta jibi da ko daukar wayar shi ba tayi, yana son ya je ganin ta amma ta ki bashi dama ko da yaje tilasta ma ta fitowa aka yi ko kallon shi ba tayi ba har ya gaji ya tafi.

Najib ne ya fahimci halin da ya ke ciki, da ke shi yasan miye auren "Calm down Baba Usy everything shall come to pass. Kar ka wani dagawa kanka hankali Allah da anyi auren ko mai zai zo da sauki" murmushi kawai yayi na yake sannan yace "Allah dai ya saukaka amma Humaira akwai taurin kai"

"Be a man my dear, kar ka ji tsoronta ko ka nuna you are weak about the whole thing kasan mata infact ma kun fahimci suna and she loves you so use that love even if its a little ka shawo kanta kar ka wani damu" Shi ke ba da shawara amma gabadaya tuno wahalan da ya sha a hannun Sumayya ya ke duk don kawai ya nuna mata tsantsar soyayya. Shi kam da nuna wa mace so ai an gama in sha Allah, he is done. Sumayya ta riga da taci Amanar soyayyan da yake mata ta yanke yards da ke tsakanin shi da duk wata ya' mace on earth.

"Oh! Ashe haka Fadila ke da kyau Ma sha Allah" Aliy ya fada yana kallon wayan shi. nan fa duk suka amsa suna ganin irin kyau in da tayi

"Wow! Ita kam dai Ma sha Allah kwalliyan ya karbe ta" 

"She looks elegant"

"Gorgeous"

"Cutee"

"And her dressing is modest"

Comments in da su ka dinga yi kenan kafin Najib ya amshi wayan domin ganin amaryan shi da ake ta kodawa. Aiko shi ma ya dara coz bai San sanda guntu murmushi yayi escaping lips in shi ba "Fine girl" ya fada a hankali ta yanda shi kadai zai ji but daman yasan Fadila akwai kyau don shi ta ma fi mishi kyau naturally akan da make up in. Haka kurum yaji yana tausayin ta. Shin wani irin zama zasu yi? Tmby da ya wa kanshi kenan dashi kan shi bai da amsa. Ya dai San kawai sai yanda yanayin rayuwa ta kasance.

Washegari, kusan 11 Asmau ta ga kiran Mukhtar suna cikin aiki. Ta dan yi mamaki ganin duk kwana biyun nan bai kirata ba sai dai SMS da su ke ta exchanging.

"Yanzu nan ki zo gida ki same ni" ya fada sannan ya kashe wayan. Dan jum tayi kafin ta mike ta sa hijabin ta. he sounds authoritative, Just like the senior brother he has always been. Ko ma dai miye ta San wannan Abu ne a matsayin ta na kanwar shi. A falon shi yace ta same shi nan ko ta ganshi da wata budurwa sai hira su ke, Nan ta ke gaban ta ya fadi tun kafin ta karasa. Kallo daya ta wa yarinyar ta ga shi looks  Familiar "sannu" kawai ta ce mata sannan ta dauke kai ba tare da ta lura yarinyar ta amsa ba ko Aa "Gani"tace wa mukhtar rai a hade. Siririn murmushi ya saki ganin yanda ta hade rai kaman za ta fashe. " Yarinya ashe ke ma kina kishi na" ya fadi a ranshi.

"Asmau ga Safiyyah sistern Yusuf da na hada Ku kawance years back kin tuno ta?" Sai a sannan Asmaun ta saki murmushi sannan tace "Yeah na gane ta mana" juyawa tayi ta kalli Sumayyan tana murmushi ta mika mata hannu su kayi musabaha "its has been a while" Asmaun ta fadi. Murmushi safiyyan ta mata sannan tace "Gaskiya kam"

"Muje ko inda muke "

"Okay" ta fadi tana mikewa.

"Ya Mk mun tafi"

"Asmy ku biyo ki gaida mum fa tare su ka zo, Yusuf ma na tmbyn ki"

"Tou Shknn" ta fadi sannan su ka tafi.

A hanya su ka hadu da Yusuf in bayan sun gaida mum in. Gaisawa musamman Asmau ta tsaya su kayi domin tana matukar ganin mutuncin shi, he is nice and considerate. Daga nan su ka wuce can gidan Amaren tare da Safiyyah, ba wani hira su ke ba amma kuma she looks nice sai smiling ta ke har su ka karasa.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now