Kano
Zaune su ke a daya daga cikin joints in su da ke Lebanon club a Kano, kowacce da abinda ta sa a gaban ta tana yi. Fatima sai faman zukar shishan ta take, Khadija ko tuni tayi nisa a duniyan maye da ta shiga gabadaya idanun ta sun yi radau radau kaman zasu fashe Amma ita Kam ko a jikin ta sai Kara kurban wani ta ke faman yi, Amina da Zainab kuwa hannun su na cikin na juna a yayin da daya ta kwanto wa daya suna kallon show in da ake a TV Wanda bana komai bane sai na Divorce court date ake particularly na Same sex marriage da ake tayi, Suhaila ko hankalin ta na kan system in da ke gaban ta tana kallon wani video in Waka. Tsaki Fatima ta ja tana kallon su "Wai wannan wani irin iskanci ne, miye Haka za ku sa Mana wannan iskancin muna kallo, me za kayi da Yar uwarka mace? Tabdi Allah ya kyauta" Khadija ta yi saurin katse ta "Dan Allah dakata Malama Ina ruwanki damu ne in ba ki iya kallo sai ki maida hankalin ki kan abinda ke gabanki, ai a ganina gwara ka bi Yar uwarka mace da ta San ciwon ka akan Da Namiji mugun icce"
"Tabdi jam a tunanin ki ba toh bara na ma fada muku gsky in ma abinda ya faru tun a schl ne baku manta ba to its high time you let it go, kowa ya San a secondary School ana irin wannan abubuwan ayi ta tura letters but a Nan ake barin su, yours is getting worst gsky"
Sai a sannan suhaila ta dago ta sakarwa Fatima hararan da ya sa ta saurin yin shiru "Teey Wai miye matsalar ki dasu ne? Ke yansu hayakin da kike ta sa wa cikin ki an gaya Miki is safe never, you know abinda zai iya biyowa baya but you choose to do it to hakan yake su ma a wurin su, its a free world kowa yayi abinda ya ga Dama haka kuma yayi regretting abin shi shikadai, kowa ai yasan gsky sai dai yaki ta." Nan ta ke duk jikin su yayi sanyi, suhaila ba ta taba kwaban su akan abinda su ke ba sai dai sun lura yanzu magana ta fada musu. Karan wayan Fatiman ne ya katse musu hiran da suke dai ko aka yi sa'a wayan na kusa da zainab, daukan wayan tayi da karfi ta Kira Sunan da ta gani kan screen in wayan "Mutumin banza" a tare su ka kwashe da dariya gabadaya in ka cire suhaila da ta fuske sai ko Khadija da bata fuskanta duniyan ma gabadaya domin kuwa tuni ta tafi rayuwan sama. Fatiman ce ta cigaba da magana "cikin Maza dai wlh akwai banzaye masu shegen nacin bala'i ga budurwar zuciya in ba haka ba Ina tsoho ina yarinya fisabillilahi ka haifi kamata Anna kana nema na" wannan karon Amina ce ta katse ta "Kinga laifin shi, irin ku ke Basu fuska ai da Basu samu sa zo?. Dai dai Nan Suhaila ta tashi tana kokarin daukan handbag in da ke gaban ta "ya ya dai mutuniyar?" Amina ta tambaya ganin alamun tafiya za tayi, "I have something to do at home" kawai ta Fadi sannan ta mike Amma a zuciyan ta tsoron Muhsin ne fal a ranta Kar ya neme ta ya rasa ya nemi hada ta da Abbah.
Katsina.
Kwanan su biyu da dawo wa daga daura Amma still wayan ta a kashe, a ranar ummi ta Kira ta tana neman ta, a dole ta shirya ta tafi a kasan zuciyan ta tana ta addu'a Allah ya sa ba Ya mukhtar bane ya fada mata abinda ya faru tsakanin su. Fadila ta Fara haduwa da a falo, kicinkicin ta amsa mata sallaman ta kaman yau ta Fara ganin ta ita ma Asmau'n ba ta wani damu ba tace "ummi fa?"
"Duba dakin ta" ta Bata amsa Aiko Kai tsaye can in ta nufa.Ga mamakin ta gabadaya zancen akan Umar saboda Ummin ta fahimci wani abu tsakanin su, Umar ya zo Mata a rikice shi dai ayi auren yanzu kawai ba sai ta shiga schedule in ba saboda ya tsorata da lamarin ta. Dagewa Asmau tayi akan bakomai wani Dan sabani ne kuma za su daidai ta, "toh Asmau ki je dai kuyi magana in ma akwai wani matsalan ne gwara ku daidaita tun yanzu saboda shi aure ba zaman kankanin lokaci bane ba a gaggawan shi gwara ku fahimci juna yanda Yakama ta" amsawa tayi da toh sannan ta Mata godiya ta fito dakin.
Ga mamakin ta samun su tayi su biyun zaune a falo wannan karon sabanin Fadila da kenan, a daddafe ta gaishe su zata wuce, Umar yayi saurin Kiran ta "Asmau" Dan juyowa tayi tana kallon shi. "Let's talk mana" nodding kanta tayi alaman tana jiran shi "no zo ki zauna a Nan ayi gaban babban Yaya ya ma samin baki ai" Dan juyo tayi su kayi four eyes da Mukhtar saurin dauke ido tayi sakamakon kallon da yake ta kokarin aika Mata gashi a gaban umar kaman ta nutse Dan kunya sai dai Bata da tabbacin Umar in ya gani, in idanun ta ba gizau ya ke Mata ba taga mukhtar in ya Dan yi baki kuma Rama ya bayyana a jikin shi.
Sum sum ta dawo ta zauna a kasa tana fuskan tan Umar in. "Dawo Nan mana" ya nuna Mata kujera, girgiza kanta tayi "I can see that you are not even free with me now Asmau me ke faruwa, ko dai kin samu wani ne?" Kanta a kasa ba ta ce komai sai can ta jiyo Mukhtar na magana "in ko hakane Dan uwa hakuri fa za kayi kawai kana tare da ita ta hango wani..." Saurin katse shi Umar yayi "Kai babban Yaya Kai da zaka sa baki a shawo kanta kuma kana zancen hakuri" shiru yayi a zahiri a badini kuma tunani yake tabbas ya San ba Wanda zai iya bar wa Asmau a duniya, No yafi kowa bukatar ta. Nan ta ke wata dabara ya fado mishi "To Shknn tunda kace haka Ina ganin ka bar ta muyi magana ni da ita sai inji miye matsalan ka San ai mutuniya tace ko Asmau? Ya fada have da kashe Mata ido daya ita dai shiru tayi kawai tana ganin Umar ya Mike "To Shknn tunda kace haka bara naje wani gu na dawo please ka dai bita a hankali"
"Haba man trust me bro"
"I do so Captain" ya fada Yana jinjina mishi ita dai a zuciyan ta Fadi take "za kaga trust kuwa" tashi tayi za ta fita yayi.saurin katse ta "ki sameni a backyard" kafin ta amsa har ya fita ya nufi wurin a dolen ta tabi shi Kar yayi tunanin ta Fara raina shi.Daya daga cikin fararen kujerun da ke wurin ya samu ya zauna, iska sai busawa ya ke a sanadiyyar bishiyoyin da sukayi yawa a wurin ciki kuwa har da na mangoro,zai dabino, tsada, lemu da gwanda. the place looks so calm and serene, yayin da tsuntsaye ke ta shawagi a wurin. Ji yake daman zai zama cikin farin ciki Shima kaman yanda tsuntsayen Nan su ke, sai dai fa da kamar wuya domin ko shi kanshi yasan ba karamin yaki bane a gaban shi, domin bai ganin zai iya rasa Asmau a cikin kowani hali, da farko dai ya samu ya shawo kanta tukun komai ya biyo baya. Tun daga nesa ya hango ta tana nufo wurin, fuskan Nan a hade ta turo baki, bai San sanda ya saki wani murmushi ba, hakika tun tana karama ta Saba da turo bakin da alama har yanzu bai barta ba. Tun kafin ta karaso ya jawo kujera ya ajiye Mata kusa dashi. Ba musu ta je ta zauna kanta a kasa tana wasa Dan Yan yatsun ta da su ka ja da bakin lalle a sanadiyyar bikin da ta je daura. Hakika ana cewa lalle yafi wa farar mace kyau Amma a idanun shi yafi ganin kyaun nata fiya da duk wata farar mace da zai sa a ido.
"Ina wuni" ta Fadi a hankali.
"Ban bukatar gaisuwar ki Asmau, kin San abinda na ke bukata a wurin ki" shiru tayi Amma a zuciyan ta ji ta ke kaman ta tashi ta ruga da gudu.
"Amma Yaya Mukhtar kasan tsakanin mu da Ya Umar fa" girgiza Kai yayi "ban sani ba saboda baki taba fada min ba shi ma haka sai jiya dana ji wurin Mami suna magana dashi in, bazan baki laifin rashin fada min da baki yi ba saidai na dauka hakan saboda bai Kai matsayin a sanar dashi in bane, Asmau na San baki son Umar" saurin dago kanta tayi tana kallon shi cike da mamaki. Nodding kanshi yayi "ko Zaki Musa min ne?" Shiru tayi hakan ya bashi Daman cigaba da magana. "haba Asmau a tunani na ban cancanci hakan a wurin ki ba, Nayi tunanin komai na ke bukata a wurin ki in dai bai fi karfin ki ba zan samu" Yana maganan ne Yana kallon ta a yayin da ita kuma kanta a kasa ji take kaman ta tashi ta ruga don har yanzu ba ta Saba da sabon yanayin da Ya Mukhtar in yazo Mata dashi ba "can i please have my answer" ya katse Mata tunani, ganin ya kafe ta da ido duk ta tsargu ya sa ta saurin bude baki "Ya Umar fa Ya Mukhtar Dan uwanka ne" wani irin kallo ya bita dashi saboda yanda ya ki jinin ya ji an danganta ta da wani namijin "dakata dallah Malama nafi ki sanin Umar dan uwana ne, ko xaki fada min abinda na ke ciki" gabadaya jikin shi na rawa yake magana, har bai San sanda ya koma Yana lallashin ta ba, it's kanta ta tsoro ta da yanayin nashi, sosai ta ke iya hango soyayyan ta a shimfide a cikin idanuwan shi, there is no doubt Ya Mukhtar na son ta soyayyan ba na wasa ba, gabadaya wani tausayin shi taji ya lullubeta Nan da Nan jikin ta yayi sanyi "Asmau Wlh ba da namijin da zai kaini son ki dashi na girma nayi hankali na San wanene ni, wata Ya mace bata taba birge ni ba bayan ke, can't you help this soul?" Ba ta San sanda kwalla ya Fara fitowa daga idanuwan ta ba, hakika ba ta iya cin Amana ba Amma bayan haka ko Bata son Ya Mukhtar za ta iya hakura ta aure shi barin ma shi din ba Wanda za ace ana so bane. "Am sorry Ya Mukhtar, i can't cheat on him please" muryan ta na rawa ta Fadi magana tsabagen kukan da ta ke yi, saurin fiddo Hanky a cikin Pocket in jeans in shi yayi ya Mike Mata "its okay my dear you don't have to cry" shiru yayi har Saida ta yi calming kanta "Abu biyu kawai Zaki min. Na farko ki dawo gidan Nan a yau ba sai gobe ba na biyu kuma prove that you love him then ni kuma duk soyayyan da na ke Miki zan jure na hakura Amma fa ki San cewa that means ends of my happiness kenan" Yana gama fadin haka ya tashi ya bar wurin, ta Kai 10 mins a wurin kafin ta tashi ta nufi cikin gida, direct dakin Fadila ta wuce ta same ta tana kallo ko kallon ta Bata yi ba. Murmushin karfin hali Asmau tayi sannan ta kalli faddi "kawata fada muke yi ne?" In ku da kuke wurin Kun tanka to Fadila ta tanka. Hawa kan gadon Asmau tayi ta janye System in da ga gaban Fadila ta kashe sannan ta jawo hannun ta, wani irin harara Fadila ta bita dashi, saurin hada hannu ta yi alamun neman gafara "sorry kawata Mana, Friends don't fight please raka ni in dauko wasu clothes ina a goruba road mu dawo" sai a sannan Fadila ta tanka "Kinga Daman dawo wa kenan" kawai smiling Asmau ta yi ta ja hannu Fadilan ba musu ta Mike ta biyo ta suka tafi. Amina juna kenan kuma kawayen asali.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
ABINDA KAKE SO
RomantizmCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...