Babi na sha Uku ( 13 )

975 92 0
                                    

8:00 AM, Wednesday
Abuja.

Sanye ta ke da farin kayan su na nurses, riga da Wanda hade da Dan karamin hijab, kayan sun matukar karban ta. Da sauri ta karasa Falon mummy domin ta gaishe ta kafin ta wuce clinic in, ga mamakin ta a can ta tadda Faisal, to kenan a gida ya kwana? Tambayan da ta ma kanta kenan kafin ta gaida mummy. "Kin shirya kenan, kinyi breakfast Amma?" Mummyn ta bukata, dan yamutsa fuska tayi sannan tace "na Sha Tea mummy" ba ta rai mummyn tayi "ayi mutum bai son abinci, ba ki tsoron sharrin ulcer ko?"
"Aa zan ci a clinic Allah Mummy Kinga am late Kuma kinsan ban son cin abinci da safe" tabe baki tayi sannan tace "ai Sai Ku je Faisal ya sauke ki, Daddy ya fita da Muhammad da Sagir, Isa Kuma ya je Kai yan makaranta"

"Mummy da ma ki barni inyi driving kawai" hararan ta tayi da sauri ta yi shiru tabi bayan Faisal da har ya kusa isa surrounding in gidan. Already ya shiga motan kafin ta iso don haka itama ta bude ta shiga wurin Mai zaman banza, har ya fita street in ba abinda ya ce mata har Sai da Suka kusa wurin securities sannan a hankali ya ce mata "put your seatbelt" juyo tayi tana kallan shi, surprisingly for the first time in years ya mata magana bayan Nan har su kayi nisa kala bai Kara ce mata ba, tun tana jiran ya tambaye ta hanya har ta fahmci mummy ta fada mishi ne kafin tazo. "Thank you" ta ce mishi bayan ta sauko a bakin clinic in ko kallon ta bai Kara yi ba ya ja motan shi ya bar wurin.

11:30 pm

Mukhtar ne lullube a cikin bargo a dakin abokin shi da ya ke zaune a unguwan garki.

"MK wai ba Za ka tashi kayi breakfast bane?" Abokin nashi Yusuf ya tambaya hade da kokarin yaye bargon. Saurin rike hannun shi Mukhtar yayi Yana girgiza Kai "Dan Allah Y leave me alone, am feeling tired and exhausted" tsaki Yusuf ya ja Yana fadin "nasan already ka huta so ba gajiya ke damun ka ba please stand up and get some food inside your stomach" banza yayi dashi, ringing in wayan mukhtar in ne ya katsewa Yusuf abinda ya ke son fadi, da kyar ya lalubo wayan ya amsa, Asmau ce akan layin don haka Yana dauka yayi shiru.

"Hello ya Mukhtar kana jina na?"

A hankali ya amsa mata da "eh"

"Ina ka shiga tun jiya ina ta Kiran ka besides ma you said you are calling me back"

"Sorry i was tired so i slept up"

"Are you sick" she enquired Jin yanda ya ke magana in a very low tone.

"No am okay am still sleeping ne"

"You didn't take your breakfast?"

"Am going to do so, will call you later" ya Fadi hade da katse wayan ba tare da ya jira ta Kara magana ba, Yana Gama wayan ya Mike. Wani tsakai Yusuf ya ja hade da girgiza Kai "ba fa a dole MK, You confessed and she rejected then leave her alone, I don't even know Kiran me ta ke maka bayan abinda ya faru, please let her be she is not the only one"

Wani Irin kallon mukhtar ya bishi dashi sannan ya Mike ya nufi bayi, a daddafe yayi brush sannan ya fita falo domin yin breakfast in. Coffee kawai ya iya Sha, chips in da ke gaban shi da kyar ya Kai spoon uku, haka yake kwanan Nan gabadaya bai da appetite, Yana Jin kaman wani abu na sama kaman shi saboda yanda zuciyan ke yawan buga gashi at times Yana mishi wani Irin zafi mara misaltuwa.

Yusuf abokin shi ne da su ka hadu tun SS1 Allah ya hada jinin su, tare su ke Zama a Florida in ma tare su kayi first and second degree in su saboda mahaifin Yusuf in ne sanadiyyan samun Admission in nasu. Iyayen shi a Abuja su ke da Zama Sai dai shi a cikin gidan part in shi daban ne shiyasa ko yaushe Mukhtar ya je Abujan a can ya ke sauka.

Yana gama wanka ya nufi cikin gidan ba tare da ya nemi Yusuf in ba domin gaishe da iyayen shi "Lah Ya MK yaushe kazo" Safiyya kanwar Yusuf in ta fada cike da fara'a sannan ta gaishe shi, Jin muryar shi kadai Dada tayi ta fito cike da fara'a Suka gaisa cikin Dan gutun fulatancin da ya koyo wurin goggo, duk da ba ita ta haifi mahaifin shi suna dasawa da ita sosai. Yusuf fulanin Gombe ne asalin su aiki ya kawo mahaifin su Abuja. Har babah Sai da ya fito musamman Suka gaisa da Mukhtar, sosai ya kwanta musu a rai suna son tarayyan su day dansu don ko su amince Mukhtar in yaron ne Mai hankali haka iyayen shi abun yabawa ne don har katsinan sun taba zuwa domin kawai ayi zumunci, haka kanen Yusuf in duk su ka hadu wurin shi suna ta Jan shi da Hira, da ke Mukhtar in mutum ne Mai fara'a tuni Suka saba da gabadaya yan gidan.

Girki na daban Safiyya ta mishi musamman da drinks in gargajiya kusan kala uku, yanda yarinyar ke Kula dashi kaman yanda Asmau ke mishi shi yasa Shima ta ke matukar birge shi.
"An gama school ko Sofy?" Ya tambaye ta.
"Lah Ya Mukhtar ban fada maka har fa na fara karatu a Nile"
"Ma Sha Allahu wani course kenan?"
"Mass communication"
"Good girl hope dai evlerything is going smoothly?"
Murmushi tayi sannan tace "to Muna dai coping"
"Tou a dai dage Sai ki ga komai ya zo Miki da sauki, a dinga Mai da hankali a class sannan a dinga kokarin karatu kinji Koh?"
"In Sha Allahu"
"Sai batun aure ko? Ko ba yanzu ba?" Cike da kunya ta rufe fuskan ta sannan ta tashi ta bar wurin da gudu, shi Mukhtar ma abin dariya ya bashi.

Sai bayan la'asar su ka isa gidan su meema, yaran sun dawo daga school kenan, meema Kam Sai dab da magrib ta shigo ta iske su harda Faisal a gidan, faran faran su ka gaisa da sauran amma mutumin nata ko kallo bai samu ba Sai dai shi ma bai San tana yi ba. Karshe maganan auren Najib su ka koma tattaunawa Sai a sannan Faisal yayi wani maganan arziki akan rashin mutunci da Sumayyan ta tafka Yana fadin bai San dalilin da Najib ya bar mata yaran shi ba.

Kano.

Muhsin ne tsaye gaban motan shi rike da key a hannun shi yana jiran su Suhaila su fito daga cikin gidan, Faroukh abokin shi yana zaune cikin motan yana kokarin kunna music, Wakan na fara tashi a cikin motan muhsin ya juya ya zuba mishi wani harara da ya sa shi kyalkyalewa da dariya "Malam ka cire kidan shaidanan nan a mota na pls" ya fadi hade da bin abokin na shi da wani harara. Dariya faroukh ya kara yi sannan yace "Afuwan Malam Ustaz tuba nake, na manta motan ka na shiga ne" tsaki Muhsin ya ja hade da duba agogo "wai wannan wani irin nawa ne? Yaran nan za su Sani lattin Seminar in nan fa. Bai gama rufe baki ba Suraj ya fito Suhaila na biyo shi a baya, kalo daya yayi wa Suhaila yayi saurin dauke kai saboda numfashin shi da yaji na kokarin daukewa, da kyar ya natsar da kanshi hade da fadin " Subhanallah" to shi ma fa kenan mai kokarin kiyaue dokokin Allah balle kuma wani can daban.

Suraj ya faro ya aika mishi harara sannan yace "Go and change that trouser my friend" Kallon Crazy jeans in da ke jikin shi Suraj yayi yana kokarin gano fault in kayan, haka dai ya koma yana tura baki. Da kyar ya daga kai ya kalli Suhaila da ke tafe
Tana tauna Chin gum tana kokarin shiga motan ya buga mata wani tsawa, sai dai fa mutuniyar ko dar ba ta yi ba sai ma wani disgust kallo da ta bishi dashi, ganin suna kokarin hada ido ya sa suka yi saurin dauke idanuwan su, shi dai faroukh kala bai ce musu ba yana dai cikin motan yana kallo.

Wani peach crep material fitted gown ke jikin ta, rigan yayi matukar kokarin fiddo mata da shape in jikin ta gabadaya, kallo daya zaka mata lace she looks sexy, kanta ko head be da tayi daurin bow dashi gabadaya ta tsakiyan ana ganin gashin ta. "Kema kinsan ba za ki bini a haka ba dai ko? Ko kunya ba kiji see your dressing" kallon jikin ta tayi don ita bata ga laifin kayan nata ba "I don't get you ni kam kuma ni duk kayana haka suke"
Tabe baki Muhsin yayi sannan yace "You can put hijab on top" kallon are you okay ta bishi dashi sannan tace "ban dashi biyu kawai gare ni na Sallah and ba zan iya fita dasu ba" ta fadi hade da girgiza kanta zuwa yanzu issue ya fara annoying inta.

"Just change into something better Young lady" tsaki ta ja hade da komawa cikin gida, ita daman ta San hada su tafiya da Muhsin is not a good idea.

Ganin kusan 10 minutes bata fito ba tana kokarin bata mishi time ya sa yayi kokarin kiran Abba "Abba ko za ka hada su Suhaila da driver ne kawai" ya fadi cike da girmamawa. Nan ta ke Abban ya nemi ba'asi aiko Muhsin ya sanar mishi yanda su kayi da ita.

Bayan 7 minutes ta fito tana gunguni, black veil kawai ta sa akan kai ba laifi ya dai fi da amma daurin ta fa ba abinda ta canja, zai yi magana Faroukh yayi saurin rufe mishi baki. Tana kallon su ta tabe baki, seriously she is tired kullum Muhsin galaba ya ke ci akan ta, abin ya isa haka barin ma ita da zata shiga jami'a.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now