Bayan Sallan isha'i suna zaune da Suhaila tana bata labarin abinda ya hado su da Muhsin "Mami ta ce wani taro a Kaduna gobe fa zasu dawo shine wai dan jaraba irin tashi wai bazan kwana a gidan ba duk maza"
"To ke banda abinki suhaila ai da gaskiyan shi in banda ke da ke da tsaurin ido ma ai ni bazan iya kwana ba" tsaki Suhailan ta ja tana fadin "an gaya miki akwai namijin da zai iya min wani abin ne?
" Allah ma dai ya tsare" Asmau ta yi saurin fadi sannan ta canja akalar zancen "ance min wai he is getting married da gaske ne" kyabe Suhaila tayi fuskan ta ya canja, kana kallon ta kasan ba ta maraba da wannan zancen haka dai ta daure ta fara maganan don ba ta so a gano ta "can wata Ustaziyya ce a layin mu fa in kin ganta kullum da hijabi dogo da socks hadda fa Niqab da safan hannu kina ganin ta kinga bagidajiya, su Abban ma na zuwa baban ta ya bada hakuri wai ya bada ita ga dan wan shi daga shi har yarinyar sai da su kayi ciwo"
"Allah sarki ka ji masoyan gsky Allah ya zaba musu abinda yafi alkhairi" tsaki Suhaila ta ja tana fadin "shirmen banza dai" sun dan jima suna hira sannan Mukhtar ya turo ma Asmau text ta zo su je wurin kayan.
Tare da suhailan su ka tafi hakan ya sa ba abinda ya faru tsakanin su duk da haka Suhailan sai da ta lura da irin kallon da MK ke faman aikawa Asmaun amma da ke ita ba mai shiga harkan wasu bane ko a jikin ta.
Suna zuwa ba su jima ba su ka dauko kayan da ke already an tafi dashi shop, kayan kam sunyi sai Sam barks, sosai suhaila ta yaba kayan tabbacin kayan ba na wasa bane domin ko in kaga suhaila ta yabi abu to ba fa karya abin yayi ne, ba ta harkan karanta Sam Sam. Tare su ka zabi colors in da zai yi matching da furnitures inta. Shi dai yana gefe ya nannade hannu har su ka gama aka kai musu mota.
Ga mamakin su maimakon yayi hanyan gida sai su kaga ya nufi wani hanya, suhaila kam ko a jikinta hasalima ear piece ke makale a kunnen ta tana jin waka, Asmau dai ce tayi ta mai kallon mamaki amma ganin ba Sani gari tayi ya sa ta yin tunanin kila ya bi ta wata hanya ne ganin dai ana ta tafiya ya sa ta zuba mishi ido tana kallon shi.
Ado bayero mall ta ga ya shigo sai a sannan ya juya ya kalli suhaila dake ta faman sauraran wakan Chris brown. Ganin yana kallon ta yasa ta gane magana ya me son mata ta cire ear piece. "Nace hope dai ba zan takura miki ba kina kallon Nigerian films" Dan hade rai tayi tana tabe baki kaman wacce ta tuno wani Abu kuma sai ta saki murmushi "Ya Mk Up North za ka kalla?" Nodding ya mata da Sauri ta bude motan ta fita tana murmushi, this was all her plan tare da wani sabon new catch da tayi mai sunan El-mustapha, the guy is classy ga iya dressing shiyasa lokaci daya su kayi mugun kulewa da ita, Rahama sadau mutuniyar ta ce sosai dan yanayin yanda ta ke living life inta na burge ta shiyasa su kayi planning su zo kallon sabon film inta coz Sons of the caliphate was her favourite Nigerian movie shiyasa tayi tunanin wannan ma zai hadu.
Asmau kam sakan baki tayi tana kallon Mk tana tuna hiran su randa yazo ya iske ta tana kallon sons of the caliphate Wanda suhailan ce ta mata recommending. "Nigerian film kuma kika koma kallo?" Ya fada yana zama kusa da ita "Aa wlh wannan an ce min yayi dadi ne sosai Rahama sadau dai ta dage tayi fice industry gabadaya, her acting was just so nice kaman ba yar arewa ba"
"Kwanaki ko na ga tallan wani sabon film inta da su banky w da adesua"
"Yeah nagani so sad a kano kawai za a nuna a cinema insu da INA kano sai naje na kalla"
"Ki zo muje mana zan shiga kano nan da 3 weeks na San by then ya fito" dariya kawai tayi don duk a zaton ta wasa, sau daya ya kara maimaita, ko da yace tazo su je kano kwata kwata bata kawo abin a ranta ba. Murmushi kawai tayi tana tuno faddi,akwai abinda ta ke son fada mata but tunda ya amshi wayan yaki bata duk don saboda Umar kar ya kirata.
Ticket uku ya siya sannan su ka shiga. Suna shiga suhaila ta hango Elmustapha rai a bace yana kallon agogon shi sannan ya dago ya kalli kofa, da sauri ta karasa wurin shi tana smiling. Ya na ganin ta ya juya kai alamun yayi fushi, bata rai tayi itan ma tace "au dan ma nazo koh?"
"But you keep me waiting bae"
Murmushi kawai tayi ganin ya sauko, side hug su kayi sannan ta zauna a gefen shi. Tsaf akan idon Asmau sai dai mukhtar bai gani ba saboda hankalin shi bai wurin.
Sai da aka gama film in gabadaya sannan su ka dawo gida, ita Asmau mamakin suhaila ta ke tayi a ranta yanda ta iya rungume namijin da ba muharammin ta ba. Shin lafiyanta kuwa? Ko ba ta San hakan a addini bane.
Ba su kara wani hira sosai ba har washegari su kama hanyan katsina ita da Mukhtar Wanda shima ba wani hiran su ke ba.
"Ya mukhtar ina son waya na please" banza yayi da ita kaman bai jita. Ganin haka yasa ita ma ta share ta San kanta a gefe. Ya tsaya a hanya kusan sau uku yana siyan drink da fruit, komai ya bata cewa ta ke ba za taci ganin yanda ta dau abin da zafi sosai ya sa yaji ba dadi kuma.
"Asmau" ya kira ta, juyowa tayi ta dan kalleshi sannan ta kauda kai.
"Fushi kike dani?" Banza ta mishi har sai da ya kara cewa "ina magana"
"Aa" kawai tace
"Am sorry please kinji bazan kara bata miki rai ba, ga wayanki"
"Na bar maka" kallon ta yayi yaga yanda ta ke ta kokarin cin magani, dariya ma ta bashi. "Okay thank you" ya fadi yana murmushi.
Layout ya wuce dasu suna shiga katsina ita dai kala bata ce mishi. A kofar gidan baba kabeer ta hango Umar a tsaye, murmushin mugunta tayi sannan ta nufe shi suna gaisawa. Ganin yanda ta ke murmushi kadai ya bata mishi rai, ita ko da gangam sai da ta lura ya kusa karasowa India suke zai iya sauraron su yasa ta marairaice murya ta fara magana "sorry please dear tafiyan ne yazo da gaggawa na so in sanar maka kuma amma wayan bata hannu na" murmushi umar yayi hade da jin wani sanyi a ranshi "bakomai Asmau yanzu ai gashi kin dawo kuma na ganki ai"
"Ya Umar nayi missing inka sosai duk banjin dadi kwana biyu" shi kam Umar mamakin yaushe Rabin da suyi irin hiran nan da Asmau ya ke "ki shiga gida ki huta zamuyi magana anjima zan kira ki"
"My phone is not with me fa" ta dadi hade da kara narkar da muryanta" mukhtar da ke bayan su ko idanun shi har sunyi ja tsaban kishi har hucin zafi yake, sai a sannan su kama hada ido da Umar, jiki na rawa umar ya Ciro babban wayan shi ya mikawa Asmau sannan ya nufi mukhtar sai dai tuni ya sha kwana ya nufi gidan baffah. Bin shi Umar yayi yana kiran shi, ita dai shigewa cikin gida tayi abinta ta bar su a nan.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...