Karfe biyar dai dai su ka isa katsina, sai da su ka gaida ummi sannan su ka shiga hutawa, ko da aka je kai musu abinci suna shirin tafiya masallaci don haka Ummi ta ce a bari kawai sai sun yi Sallah tunda sun sha shayi.
Bayan an dawo Sallan isha'i tukunna su ka dawo gida don haka Ummin ta sa Asmau ta kai musu Abincin. Sallama tayi a bakin kofan amma shiru ba Wanda ya amsa, hakan ya sa ta kara yin sallaman, sama sama ta ji muryan Yusuf ya amsa sannan ta kutsa kai cikin dakin. Kallo ya ke a system Mukhtar kuma na sallan Nafila, a hankali ta ajiye abincin sannan tace "sannu da hutawa Ya Yusuf" ko dagowa ya kalle ta bai yi ba balle ta sa ran zai amsa, jiki a sanyaye ta juya ta bar dakin.
Tana fita ya jawo abinci yayi serving kan shi ya fara ci hankalin shi kwance. Mukhtar na idar da sallah ya daka mishi duka a cinya "Y wai miye haka ne kake min?"
"Ita ma taji in da dadi tunda ka ki in mata magana ni wlh haushi ma ta ke bani kwata kwata ba ta da tausayi balle kuma a zo batun kirki"
"Asmauna na da tausayi Yusuf kaga in ina gidan nan to sai ta tabbata ban zauna da yunwa ba"
"Na banza" ya fadi hade da jan tsaki "shiyasa fa ban cika son harka da kananan yara ba wlh, the girl doesn't even know what she wants balle ta kwato wa kanta Yanci, its so clear kawai yace yana sonta ita kuma because he is matured she is ready to marry him kuma ba za ta iya cewa Aa ba yanzu saboda kar a zo ana magana, Mk leave me put some sense into her head, just 30 minutes talk will do"
"Ban son takura ma ta Y shiyasa"
"Kai kuma ka takura wa kanka, kaga ka zabi daya either ka hakura da ita ka yi moving on with your life instantly ko kuma ka kyale ni in mata karatun ta natsu"
"Is not that easy Y bazan iya cire ta daga Rayuwata ba" Tsaki Yusuf ya ja ya jawo ear piece in shi ya sa a kunne don kar ma ya ji bayanin da MK ke kokarin mishi.
Suna zaune a falo Mukhtar da Yusuf su ka fiddo tsaraban da su ka siyo wa yaran gidan kowa sai da aka bashi kason shi har da Ummi suna ta godiya. "To ni dai na ga tsaraban kowa ban ga ta diyata ba yar lelen ku ba dai manta wa kuka yi ba" nan fa kallo gabaday ya koma kan Asmau da ta cika kaman za ta fashe ba wai don rashin tsarabar da ba su kawo mata, Aa ganin irin kallon hararan da Yusuf ke aika mata sai cewa yayi "rabu da ita Ummi laifi ta mana shiyasa muka share ta" fadin Yusuf kenan yana bin ta da wani mugun kallo, Mk dai ya zama speechless ganin ba yanda ya iya da abokin nashi. Fadila da ta San kan zancen ko sai cewa tayi "kai Ya Yusuf ana Uzuri fa a rayuwa"
"Muma ba a mana uzurin ba ai"Ummi da ta fara zargin wani abu tayi caraf tace "ba Ku dai kyauta ba gsky..." Ai basu karasa zancen ba su ka ji sheshekan kukan Asmau ko da su ka juya har ta yi daki da gudu, Fadila ce ta tashi zata bita Mk yayi saurin dakatar da ita ya bi bayan ta da kanshi, nan fa zargin Ummin ya kara karfi Amman kuma sai ta samu su ido ta ga ikon Allah.
Samun ta yayi ta sa kanta a gado sai kuka ta ke.
"Asmau" ya kira sunan ta da karfi, jiki a sanyaye ta dago tana kallonshi ya hada hannayen shi akan kirji yana kallon ta, kallo ne mai ciki da ma'anoni dayawa hade da bege saurin kawar da idanuwan tayi lokaci na farko taji wani irin tausayin shi ya darsu a ranta domin kuwa in har idanuwan ta ba gizo su ke mata ba abinda ta hango a idanuwan shi bata taba hango makamancin a idon wani da namiji ba. "Tashi ki wanke idanuwan ki" ba musu ta tashi tayi yanda ya ce "Ya MK me ka cewa Ya Yusuf ya tsane ni" murmushi ya mata sannan hannun ta ya riko yayin da wani abu ya ratsa ta jinin shi zuwa jikin shi gabadaya har ko kwakwalwar shi amma duk da haka ya kasa sakin hannun nata to fah a bangaren Asmau ma hakan ne ya kasance, yayin da wani irin zufa ya fara keto mata, dai dai lokacin ta fara zargin kanta anya ba ta son Mukhtar kuwa? A haka su ka cigaba da tafiya kowa da abinda ya ke sakawa a cikin ransa har su ka iso falon, jakan system in shi ya jawo ya fiddo wasu haddadun set in bracelet da ring, designers silver color sai sheki ya ke tayi. Ba tare da la'akari da mutanen falon ba ya jawo hannun ta yasa mata su, nan ta ke falon ya dauki dariya ana tsokanan Asmau shi dai Yusuf kallo kawai ya bi Mk dashi, ya tuna lokacin da yayi ta kallon su amma bai yi zaton ya dauko su ba.
Washegari da safe bayan sun gama karyawa mukhtar ya shirin shi domin haduwa da wani abokin kasuwancin shi da ke cikin kasuwan "ba za mu je ba Y?" Girgiza kan shi yayi sannan yace "sai ka dawo Allah ya tsare" kala Mukhtar bai ce mishi ba ya fita abin shi da ke daman yana kule dashi saboda abinda yayi wa Asmau.
Bai dade da fita ba Yusuf ya tashi yayi wanka, numban Asmau yayi dialling kai tsaye bayan ya gama shiryawa. "Ki kawo min bakin shayi" kawai ya fada bayan ta dauka ya katse wayan, Asmau ba ta day dogon lokaci ba wurin hada shayin ta kai mishi, Yau Faran Faran ya amsa sallaman ta sai dai attention in shi na kan TV. "Gashi Ya Yusuf" ta fadi hade da kokarin mikewa zata fita, saurin dakatar da ita yayi "Na ce ki tafi ne? Zauna magana zamu yi" sum sum ta koma ta zauna.
Sai da yayi Jim yana tunanin abinda zai fada mata da har zai kai shi da yin nasara a abinda ya ke bukata daga wurin ta "Gaki dai physically kaman mai wayau amma na fahimci abin ba haka ya ke ba" dago tayi ta dan kalle shi sannan tayi saurin mai da kanta kasa "haba Asmau, nayi tunanin kina da tunani, tausayi da kuma Sanin yakama ta, Yanzu har akwai Namijin da zai fi miki Mukhtar a duniya?" Shiru yayi alamun yana jiran amsan ta gane hakan yasa tayi saurin girgiza kai "a ganina Yau ko aure aka zo za a daura miki ki ka gano Mukhtar na son ki zaki hakura ki aure shi amma ina abin ba haka ya ke ba a gunki ke yanzu ke duniya akwai abinda yafi karfin mukhtar a wurinka, a yanda kuke ko ce miki yayi yana son abu duk wuyan abun nan ke mai nemo mishi ne ballantana kuma ke Ya ke so Asmau, so na gaskiya da hakika, burin shi ya mallake ki a matsayin mata, shin kinsan wahalan da ya sha ko ince wahalan da ya ke sha akan ki? Haba Asmau wannan ma abun dubawa ne kar fa ki manta Mukhtar da kike gani ba irin matan da zai gani a rayuwar shi kala kala kuwa amma kuma ya nace ke din da kika taso a gaban shi ya raine ki ya ke so, wlh a duniya duk Wanda zai miki haka ba karamin soyayya ya ke miki ba, you should be proud and lucky to have him, nasan cewa kina da saurayi but call him, talk to him and makes him understand na tabbatar in mai tunanin ne zai fahimce ki na tabbatar dai ba za kice min kin fi jin shi a rai fiye da yanda kike jin Mukhtar ba, Allah ya gani ina sonki da MK Asmau saboda ba zan so kiyi asaran babban masoyi irin Shi ba sannan kuma kisa min abokina cikin hali na tsaka mai wuya ba, ina kallon ki kaman kanwata, shiyasa na kira ki, shawara fa nake baki amma ba tursasa miki nake ba"
Wani ajiyan zuciya Asmau ta Saki kafin ta fara magana a hankali "nagode ya Yusuf sosai, Allah ya gani ba zan ce ban son Ya mukhtar ba sai dai har yanzu kwakwalwata ta kasa daukan hakan, zuciya ta ta kasa amincewa da hakan sannan kuma in ma hakan ta kasance ban San ta yadda zan fuskanci iyayenmu ince musu na fasa auren Ya Umar ba bayan ni da kaina na nuna amincewa da haka"
"Asmau kenan maganan Umar ki bar mu dashi, abu daya nake nema a wurinki ki bawa MK daman ya nuna miki irin son da yake miki, nasan ba za ki kishi domin tun asali akwai kulawa da mutuntaka a tsakanin Ku, I can't believe you never expects this ma Asmau, Mukhtar ya dade yana sonki, infact tunda nasan mukhtar na gano hakan zai faru tsakanin Ku because of how he loves and care for you Asmau tun kan ki San kanki tun kina yar kankanuwar ki"
Wani zufa Asmau ta ji yana keto mata domin ganin yanda Yusuf ke kokarin daure ta da jijiyoyin ta, gabaday ma ji tayi she is feeling guilty akan abinda ta ma mukhtar in, he deserves a chance. Infact ma tun lokacin da Mukhtar ya bayyanar mata abinda ke zuciyan shi ta rage damuwa da Umar da Al'amuran shi, yanzu wayan shi ma sai ta ta dama ta ke dauka, gabadaya duk ya damu amma ko a jikin ta "how i wish Ya mukhtar ya fada min da wuri before Umar"
"He made a mistake but I guess still akwai lokaci its not to late" sai da Yusuf ya bata amsa sannan tayi realizing maganan zucin da tayi ya fito fili, she is totally confused about the whole thing.
"Nasan you are confused Asmau but go and think kinji and my advice ki je kiyi istikhara ki roki Allah matsalar ki ya zaba miki mafi alkhairi duk Wanda kika ji ya kwanta miki bayanan then follow your mind, I promise i will support you ko da ko ba MK bane" sai a nan ta Saki murmushi da shi kanshi sai da ta bashi dariya.
"Thank you Ya Yusuf nagode sosai" murmushi ya mata sannan ta bar dakin cike da farin ciki.
A ranar ta ce ma Ummi za ta gida, ganin ta cikin farin ciki ya sa Ummin ba ta tuhume ta ba Fadila ma tayi mamakin tafiyan nata amma kuma she decide not to intervene.
A/N: Slm, ya azumin ya ibada? I hope you are all enjoying it? Allah ya bamu ladan watan nan mai albarka. Ameen
Nagode.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...