Babi na ashirin da tara ( 29 )

853 88 3
                                    

Zaune ta ke a cikin motan prince tana sauraron kukan da ya ke kawo mata. Har ga ranta tana tausayin shi domin yana mata soyayyan da bata mai kashi daya cikin Dari. Sai dai kuma a halin da ta ke ciki da zai barta ta ji da damuwanta da tafi jin dadi. Kiran meema ne ya shigo wayanta, rabon ta da yan uwan na ta duka biyu ya kwana biyu. Tun ranar da su kayi kaca kaca da Asmau akan ta gan ta a jikin El mustapha. "Kinga ni ban shiga harkar ki so please let me be" tsaki Asmau ta ja "tana fadin Suhaila ba ki da rayuwar da zan shiga in dai wannan kike kira da rayuwa" a kaukkauce ta dau jakan ta ta bar wurin suhailan tana fadin "ki kara gani na a wurinki sannan ki fada min haka" kala suhailan ba ta tanka ba har ta bar gidan. Tun daga ranar ko a hanya ba su hadu ba. Sun dai hadu da meema ta mata fada a fakaice, sai dai ita ba ta gan dalilin da za su dinga shiga rayuwar ta ba. Kowa ya ji da rayuwar shi kawai, you become what you wanted to be.

Ba tare da sun gaisa ba meema ta fara koro ma ta bayanai "Zamu je katsina gobe, Ya Mk na asibiti zamu je dubo shi"

"Me ke damun shi?"

Dan jim meema tayi sannan tace "to an dai ce high bp da kuma heart"

"Allah ya bashi lfy, just call me in za Ku wuce"

Ajiyar zuciya ta saki sannan tace "prince gobe za ni katsina" a dan tsorace ya kalle ta yace "shona lfy?"

"My cousin brother is on admission, zamu je dubo shi" zufan da ke fito mishi yayi kokarin sharewa sannan yace "Allah ya bashi lfy but what about the dinner"

Side kallo ta mishi hade da rolling eyes inta "na taba fada ma ka abu ban aika ta" shaking kanshi yayi.

"I keeps on my words" ta fadi hade da kokarin bude kofan.

"Shona are you leaving now? Its soon"

Tabe ba ki tayi, a ranta tana mitan abinda prince in ya ke mata. Tabbas da ba shi bane ba zata dauka ba. Shi din yana da wani girma da kima a idanun ta ne shiyasa ta ke raga mai. Without a word ta bude kofan ta Dan kalle shi. Waving kawai ta mishi sannan tayi tafiyan ta.

Washegari ya kama weekend, tun 11:00 am meema ta kira suhaila tazo. Ai ko ba tayi mintuna goma masu kyau ba sai ga Faisal ya iso daukan su. Bai San cewa dukkan su ukun za su zo ba don haka da abokin shi Al-amin    su ka zo. Saukin ma mutum daya ne kawai.

As usual su suhaila ne kawai su ka gaishe shi amma meema ko gezau ko kunyan shiga motan shi ba tayi ba. A ranta tana cewa ko an gaishe shi sai ya ga daman amsawa don haka ba zata wahalar da kanta ba.

Direct gidan Baffa su ka nufa da niyyan su huta bayan la'asar su je asibitin. Asmau dai kawai ta amsa da eh ne, tana idar da Sallah ta yi waje da hijab in da ke jikin ta. A waje ta tadda su muhsin da abokin shi Faroukh da alamun isowar su kenan. Gaishe su tayi za ta wuce muhsin yayi saurin tsayar da ita "ina zaki Asmau?"

"Asibiti" ta bashi amsa kai tsaye.

"Ina su Faisal in ba an ce tare kuka zo ba"

"Suna ciki" ta fadi

"To ki jira su mana, daga zuwa sai hawa napep" ba yanda ta iya ta bisu su ka koma cikin gidan dakin Hajjah Fati sai dai duka suna tare da su Goggo Fulani da Mama Amarya suna hira a falon na ta. Autan mama Amarya Aliyu Ya leko ya ce "Goggo mu je ko zan kai wa Ummi sako tana jira na" zumbur! Asmau ta mike daman hijab in ta na jikin ta

"Aa ma'u ba za ki jira yan'uwan na ki bane?" Girgiza kanta tayi tana fadin "Aa Goggo gsky ni ke zanbi"

"Toh Abincin fa?" Hajjah ta bukata.

"Ummi fa na can zanci a can" ba wanda ya kara magana haka nan ta fita ta bi su Goggon zuwa Asibitin yayin da kirjin ta ke ta faman bugawa cike da fargaba. A wajen asibitin ta hadu da babanta ta tsaya su ka gaisa sannan ta karasa ciki.

Da mama Aisha ta fara cin karo su ka gaisa tana fadin "ina sauran yan uwan na ki?"

"Za su zo anjima" kallon zargi mama Aisha ta bi yar ta ta dashi yayin da su ke gaisawa da Umar in da ke kokarin barin dakin ganin ga mama Aisha ba zai iya zama tare da ita ba a matsayin ta na surukar shi sannan gasu Goggo na shigowa. gabadaya shine mai jinyan Mukhtar. A lokacin bacci ya ke shi ta bi da kallo tana ganin yanda ya rame yayi baki kaman ba MK inta ba.

"Ma sha Allah ya samu bacci kenan" Goggo ta fada tana duban shi. Mama Aisha tace "ni ma tun da nazo baccin ya ke ai yau kam sai godiya jikin yayi kyau"

Fat! Fat! Gaban Asmau ke bugawa jin ance a haka ma jikin yayi kyau. Wani irin hawaye taji na biyo ta ai ko su na hada ido da Ummi ta fito daga toilet hawayen su kayi Nasarar gangarowa kan kumatun ta. Ummin kanta ta fada tayi duhu, ba dole ba Mukhtar inta guda. Da sauri ta karasa wurin Ummin hade da fadawa jikin ta, kuka ta saki mai kara Ummin na lallashin ta. Sanin kowa ne Asmau ta fi shakuwa da Ummi akan mahaifiyar ta, ana yi alakanta hakan dalilin kasancewar ta yar farko, in dai kan Asmau ne to fa Maman akwai kara.

Mama Aishan ce ta musu magana "Haba Ummin yara ya zaki biye mata, kuka na maganin cuta ne" saurin share hawayen da ya fara zubo mata Ummi tayi tana murmushin karfin hali. "Ai tsakanin Ma'u da Mukhtar sai Allah banga laifin ki dan kinyi irin kukan nan ba" Goggo ta fadi tana binsu da kallo yayin da sheshekar kukan Asmau ya karade dakin.

Zamu iya cewa sheshekan na ta ne ya farkar da Mukhtar da ke ta faman baccin wahala. Kar idon shi akan ta ya sauka, jin alamun ana kallon ta ne ya sata waiwayo wa. Ido hudu su ka hada yayi saurin sakar mata murmushi. "Asmau" ya kira a hankali irin yadda yan dakin za su iya ji sai lokacin su ka lura ya farka.

Barin jikin Ummi tayi ta karasa kusa da shi idon ta na faman zubda hawayen har yanzu "sannu ya Mukhtar ya jikin"

"Alhamdulilah, kukan me kike" murmushin karfin hali yayi ya jawo tissue a gefen ta da dayan hannun shi da ba drip, yana mata alama ta goge hawayen ta. Yin yanda yace tayi sannan ya ce mata "Me yasa kika zo ba karatu ake ba" kallon lafiyan ka kuwa? Ta mishi.

Sai a sannan ya lura da su Goggo da mama Aisha ya fara kokarin musu magana "sai yanzu ka ganmu" Goggo ta fadi cikin tsokana, murmushi kawai ya musu hade da amsa gaisuwan da su ke mishi.

Mama Aisha kam gabadaya jikin ta yayi sanyi, ba shakka zargin ta ya kasance gaskiya. Kallo ta bi Ummi dashi sai ta lura Ummin ma kallon ta take cike da ma'anoni a fuskokin su.

Isowan su Faisal ne ya katse shirun da dakin ya dauka, hira su ka taba sosai. Ba shakka Mukhtar ya ji dadin ganin na su don ko ya daure sun yi nishadi duk da halin da yake ciki. Ganin yana bukatan nishadin ya sa Dr dara bai yi fada akan cikan da aka yi ba.

  Yan matan Zaune a farfajiyar asibitin gab da magriba suna hira sai ga Yusuf in mami ya shigo asibitin. Fitowar muhsin kenan zai gabatar da alwala ya ce mishi "kai kuma ina ka tsaya haka tun dazu"

Wani murmushi rainin hankali yayi yace "Abu na je yi cikin gari" wucewa muhsin yayi domin yin alwala ya ji Yusuf in na fadin "oyoyo baby" hade da bude hannayen shi. Ba kunya suhaila ta isa gare shi hade da hugging in shi ta side. Wani bakin ciki ne ya mamaye zuciyan muhsin ba shirin ya runtse ido ya zaune don tsayuwan na neman gagaran shi. Neman kara jawo ta jikin shi Yusuf ya ke ta harare shi ta janye jikin ta. Wani bakin ciki ya turnpike muhsin ya ji ya kasa yin alwala saboda kan shi na sarawa. Fita yayi kawai ya wuce masallaci da niyyan yin alwalan a can. Daga bays su Faisal da sauran su ka biyo shi amma fa banda Yusuf bai je ba kuma ko a jikin shi.

Asmau kam gabadaya ta gama sarewa da al'amarin yan gidan mami in aka cire muhsin da kuma kananan yaran. Tabbas akwai aiki, meema ma dai ido ne nata. Duk sun watse amma fir Asmau ta ki barin Asibitin a cewarta za tabi Ummi in za ta koma gida.

ABINDA KAKE SOOnde histórias criam vida. Descubra agora