Babi na arba'in da Bakwai ( 47 )

986 94 8
                                    

Akwatunan ta kadai aka sa a mota, driver in gidan su Yusuf da ya zo dashi daga Abuja ne ke jan motan. Sai su biyu da ke zaune a gidan baya. Har yanzu kukan ta ke kasa kasa.

A zuciyan shi ya ke ji kukan nata Amma he is not courageous enough to console her, zama kusa da ita kadai da yayi yana ganin is enough challenge. Kusan 2 hours ta deba ta na zuba kukan, shi kanshi kan shi ya fara sarawa balle ita mai kukan. Da ma samu yayi ya yai kukan shi ma da ya dan samu sauki.

A hankali ya Kai hannayen shi fa ke ta shaking kan nata ya rike ga gam. Sannan yayi using dayan ya yaye veil in ta ya dan dago kan ta. Addu'a ya ke tayi a zuciyan shi, a hakan ya ke samun karfin guiwa. Idanuwan ta a runtse su ke sai ruwan hawayen da ke ta malala. Hanky ya sa yana goge Mata hawayen a hankali yace "Dan Allah is enough kinji, Kar ki sa wa kanki fever" yana maganan ne voice in shi na cracking.

Jin hannayen shi a jikin ta kadai ya sa jikin yayi sanyi, ita kanta ta gaji da kukan Dan haka ta sa ma kanta salama. musamman ya nemi su tsaya su ci abinci akan hanya Amma fir taki yarda ta Sha ko da ruwa. Bai son takura ma ta, hakan ya sa ya kyale ta.

Sai da za su shiga kaduna ta dago Kai a hankali tana magana "please Ina so inga Fadila in ba matsala" dagowa yayi ya zuba Mata idanuwan shi, yai kaman bai jita ba. Tabe fuska tayi kaman za tayi kuka. Murmushi yayi ganin ta na neman fara zubda wani ruwan hawayen yace "it's okay na jiki" Shi ma da gangan yayi hakan saboda ya tsokano ta. 

Wayan shi ya ciro ya latso numban kanwar tashi, ringing daya ta dauka.

"Hello Ya mukhtar" loudspeaker ya sa ta yanda Asmaun za ta iya sauraron fadilan.

"Hey Sis, ya dai? Are you at home?"

"Ina gida, za ka zo ne?" Ta fada cike da zumudi.

"Muga... Okay we are coming for flash visit Nan da 20-25 minutes in Sha Allah"

"Wow! Kai da wa? Wait! Asmau? OMG! Sai kun iso" kashe wayan yayi yana smiling. Hakika amintakan Asmau da Fadila na burge shi. Despite all the obstacles, they always find a way to stick together.

Murna kaman ya kashe Fadila ganin Mukhtar da Asmau a gidan ta. To yaran ma ba a bar su a baya da ke dan zaman su a katsina sun Saba da mutane. Kaman wasu baki haka ta dinga gabatar musu abubuwa. Kaman ta cinye kawar ta ta daga karshe ma Jan ta tayi su ka nufi daki. Mukhtar da Najib dai Yan kallo su ka zama a ranar, da ke Najib in ya dawo ya same su a gidan.

30 minutes su ka diba a gidan kafin Mukhtar ya bukaci ta fito su tafi. Nan fa aka koma rau rau da idanuwa. Musamman la'akari da za su dade ba su ga juna ba. Da kyar da sudin goshi su ka rabu cikin kuka. Mukhtar dai sai hararan Fadila ya ke domin ya San ta janyo mishi aiki ne sanin kukan Mutuniyar tashi ba mai karewa bane a kusa. Tun can Daman ya San abin shi da rigima balle kuma ga dalili... Ai ko ta dade tana kukan, gabadaya ta rikita shi. Ji ya ke kaman shi ya kwalla karan kowa ya huta. The worst shi ne shi din ba Wai ya iya lallashi bane Amma da alama yanzun dole ya tsage damtse.

Tafiyan six hours ya Kai su Abuja. Duk sun jigata. Direct cikin gidan su Yusuf ya Kai ta, dake Daman sun San da zuwan na ta tuni aka fara haba haba da ita. Mum in su Yusuf ne ta sa ta a gaba dole ta ci abinci ta Sha tea kafin ta barta ta kwanta. Ba wani baccin kirki ta samu ba, mum in ta tashe ta tayi wanka domin flight in 2:00 am za su bi. Ba su wani dade a airport in ba aka fara boarding.

Jikin window ya zauna ya barta a kusa dashi. Sai dai gabadaya they are acting like strangers. Ba wani magana da ke shiga tsakanin su sai ya zamana kowa na jin nauyin Dan uwan shi. Idanuwan shi kyam akan ta lokacin da jirgin ke tashi sararin samaniya, yana kallon yanda ta runtse idanu. If he can remember this is her third time ta shiga jirgi, suna Yara sun je Umrah ita da su Fadila sai kuma aikin Hajj in da su kaje last year. A hankali ya kamo hannun ta ya sakale da nashi tunowan da yayi tana da height fright ne, gashi kuma Allah ya hada ta da miji pilot.

Ta dau mintuna kafin ta samu natsuwa. Pocket qur'an ya ciro ya miko mata, ta sa hannu ta amsa. Suratul Yaseen ta bude ta fara karantawa a hankali. Lumshe ido yayi yana sauraron voice inta na sauka cikin kunnen shi. Ta dade tana karatun kafin bacci yayi awon gaba da ita, ba ta San lokacin da ta daura kanta kan shoulders in shi ba. Kara gyara ma ta kwanciyan yayi.

Ko da ta farka ta dauka sun iso Amma sai ta ji alamun jirgin har yanzu tafiya ya ke. "What are you ordering?" Ya tambaya yana kallon fuskan ta. Sai a lokacin tayi realizing a jikin shi ta kwanta, saurin mikewa tayi. Abubuwa masu ruwa ta sa a kawo Mata sai fruit da ta hada da.

Gabadaya she is tired and he can sense that. Daman ya San za a Rina, non stop flight ya samo musu from ABV To MIA wato Nnamdi azikwe international airport Abuja to Miami international airport. Approximately time in na daukan 14 hours ne. English novel na collen Hoover mai title its ends with us... Ya ciro ya bata. Musamman ya tanaji novel in sanin ta tana son karance karance fiye da kallo. Smiling ta amsa tace "Thank you" murmushin ya mai da Mata sannan ya juya ga abinda ya ke yi.

Karfe Sha dayan safe su ka isa Miami da ke Florida. Wanda yayi dai dai da karfe biyar na yamma a gida Nigeria. Six hours difference ne tsakani. Taxi ya dauko musu zuwa apartment in da ya Kama da ke Nan kusa da na Yusuf. A gajiye dukkan su biyu su ka shiga gidan, shi dai kam in da sabo daman ya Saba. Ita dai Asmau bin garin tayi tayi da kallo. Yau ga ta wani kasa da ba ta San kanshi ba gabadaya. At first sight apartment in ya tafi da ita, she trust his taste and everything. Komai na gidan ya Mata tsaf tsaf, sai bin gidan ta ke da kallo tana hamdallah ga Ubangiji. Kaman estate haka unguwan ya ke duk ginin kusan kala daya ne. Gidan ya na dauke da parking space da zai dau mota kusan biyar. Yana dauke da babban parlor da su ka Sha royal chairs Wanda su kan su abun kallo ne sai dakunan bacci uku, duka well furnished da babban kitchen da store. Gida dai normal na zaman mutane 5 haka. Wallpaper in gida ya Mata kyau sosai.

Dakunan baccin da ke facing juna ya nuna Mata "you can use both of them" nodding tayi kawai ta hau duba su.

Daya is well decorates in purple while the other one in ash. Da sauri ta nufi purple room in, she have always dream of it. Hatta kayan auren ta da su ka siya in purple ne. Ko ya za ayi dasu? Share thought in tayi tayi saurin shiga dakin. Ba ta jima a ciki yayi knocking ya kawo Mata boxes inta. Tana ji yana ordering abinci ta waya. Bai Mata magana ba saboda ya San za tace ba za ta ci komai ba.

Wanka ta shiga sannan ta fito ta hau sallolin ta. Ko kafin ta gama ya kawo ma ta abincin har daki ya fita. Ya bar Mata note kaman haka. Please do eat something.

Chicken kebab ne sai Irish and egg da liver sauce. Sai frozen yogurt. Tas ta cinye abinci da ke ta ji yunwa sosai. Sannan ta watsa ruwa, da kyar ta iya say kayan bacci ta bi lafiyar gado.

ABINDA KAKE SOजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें