Babi na sittin da daya ( 61 )

886 85 3
                                    

Kaman yanda su ka tsara all ladies event in ya tafi. Ba wani mutane dayawa da ke meeman ba wani kawaye gare ta sosai ba. Ba su da wani yawa yawancin duk Yan uwa ne. Subtle glam aka ma bride in. They really had fun.

Ko a jikin ta ba ta wani Jin faragaban aure kwata kwata. To mai ma zai dame ta ita da za tayi for a mean time kawai. Kuma is not like real marriage. Har mamakin ta ake yanda hankalin ta kwance sannan kuma ba ta cika shiga abun bikin ba. Sai dai Suhaila don Fadila fama ta ke da baby ga su ilham ko Ina suna manne da ita.

Gaban ta bai fadi ba sai da aka daura auren shima na yan minutuna ne ta basarwa tunawa da tayi fa ba real marriage bane. Duk da haka lokacin da aka so tafiya da ita sai da tayi kuka musamman da aka Kai ta wurin Daddy. Mutane dayawa sun fi shakuwa da mahaifiyar su sai dai bangaren meema fa an Sha ban ban. Kaman Aminiyai haka su ke da Daddy, bai da wani abokin shawaran da ya wuce ta. Tun tana karama ya sa ta a jikin shi sosai musamman don sunan mahaifiyar shi da ya sa Mata.

Lallashin ta yayi sosai ya Mata nasiha har sai da ta ji jikin ta yayi sanyi ganin yanda iyayen ta ke farin ciki da auren. Shin ya za su ji in sun San na bogi ne? Ni dai nace Ehmm.

Gwarimpa Estate gidan ta ya ke. Yanayin dukiyan da aka narka a gidan ko har ba a magana duk tasan aikin Daddy ne Amma a side In ta kawai ne wato upstairs.  Parlon in kasa da dakin shi ne nashi. Ba karamin tsaruwa yayi Kai yanayin gidan ma kadai abun kalllo ne. Tmby ta dinga ma kanta shin Daman haka Faisal ke da kudi? A na Kai ta ba a dade ba aka fara Shirin Dinner in da aka musu organizing. Har gida makeup artist in tazo ta Mata make up. Tayi matukar kyau cikin dark blue Gown da aka ma mishi kwalliya da silver stones. Abin ka da fara mace ya matukar karban ta.

Ko da su ka isa Hall in abin ya zo da sauki domin Entrance Amarya da ango daban daban ne. Kowa friends ya rako shi. Shima din blue shadda ya sa da ya aiki. Yayu kyau sosai. Sai da ya zauna gefen ta ya dan kalle ta yace "Amarya Congratulations kin kyau fa" juyowa itan ma tayi ta kalle shi In suprise tace "pretense have never been that easy, Congratulations too on your fake marriage" murmushi yayi mai kayatarwa yace "Thank you"

Tuni MC ya fara aikin shi. Anyi performance dayawa kafin ya bukaci a zo yanka cake. Ita ta fara yanka cake in, kallon shi tayi ta mai alama da tana son mishi magana. Dan kasa yayi da kunnen shi yanda za ta iya fada mishi tace "am sorry you Know we have to pretend everything is alright, so you have to take the care" shu'umin murmushi yayi. A hankali ya riko hannun ta ya Kai bakin shi sannan ya ciri cake. Tafi aka sa gabadaya hall in. Ita ko mamakin karfin halin shi ta ke. Da yanko na shi pieces in ya bata sai da ya dau cup in ya bata drink a bakin still. Mc ko fadi ya ke lallai ba ma shakka wannan Angon zai kula da Amaryar sa.

Lokacin da aka kirasu rawa kowa. Kowa sai da yayi mamakin likin da ya Mata duk ba tayi rawan ba. Shin wani irin kudi gareshi haka? Anya ba tafka babban kuskure ba? Tmbyn da ta dinga ma kanta kenan har a ka tashi event in.

Ba Wanda ya kwana a gidan. Yana zuwa da friends in shi, Al-amin ne yayi addu'a ya dan musu nasiha sannan ya ciro 50k ya ba Suhaila na sallaman kawaye. To duka ma friends in su  5 ne.

Friends in ne su ka maida su gida sannan aka bar Amarya da angon ta.

Suna fita ya kalle ta yace "Amarya ya gajiyan biki" tabe baki tayi tace "ba wani gajiya ai"

"Koh? Gaskiya ni kam na gaji" ya fada hade da mikewa. Leda ya ajiye Mata a gaban ta yace "let me take some nap, have a nice night pls" bai kara cewa komai ba ya fita

Ko a jikin ta bude ledan. A koshe ta ke jin ta don haka drink in kawai ta Sha ta sa sauran a fridge sannan ta shiga dakin ta kwanta. She really miss her bed, ta na kwanciya ta ji kewan. Ni dai nace Asuba na gari.
....

Florida.

Da dan fara'an shi ya bude front door in gidan. A ranshi yana addu'a Allah ya sa ya ga canji, 5 days kenan ba ya gidan. All his hopes lost lokacin da yayi stepping kafan shi cikin gidan. One month kenan da rayuwan su ta samu sauyi. kuran da ke falon kadai ya isa tabbatar mishi har yanzu ba a samu canji. Rike kanshi yayi da yaji yana faman Sara mishi. Anya ba hakkin Ummi bane ya kamashi? Ya tmby kanshi question in har ba adadi yanzu.

Daurewa yayi ya karasa dakin na ta. As he expects tana zaune kan gado ta jingina kanta na sama. Girgiza Kai yayi ya Mata sallama. Da kyar ta amsa daga nan ba ta kara ce mishi komai ba.

Kallon ya kara yo cike da takaici sannan ya dubi dakin. Rasa abinda zai ce Mata yayi ya Kira yayi requesting room service mace. Nan da nan ta zo ta fara gyaran gidan.

It all started on one terrible Saturday. Tana hutun school unfortunately shi kuma yayi kwana biyar bai garin Amma a Daren zai dawo. Cikin dare ciwon ciki hade da mara ya rike Mata. Tun tana tuna kokarin daure har abun yaci tura. Sanin Halima matan Yusuf friend in shi bata Nan Ya sa tayi saurin dialling numban shi. Ringing In da ya fara ne ya tabbatar ma ta ya iso cikin garin Amma bai dauka ba. A ta ke sai da ta mishi kusan 10 missed calls Amma shiru. Lokacin da ya biyo missed calls in already ta riga ta jigata. Da kyar ta ke iya magana yana ji a rude ya ke tmbyn me ke faruwa. Ganin ta kasa magana ma ya sa ya katse wayan yayi nemi taxi zuwa gidan. Sai dai ko kafin ya isa har ta fara bleeding, a galabaice ya dauke ta su ka tafi hospital. Ko da su ka isa aka shiga da ita she already lost the baby so wanki ciki kawai su ka Mata aka sa Mata drip.

Tun da likitan ya fada mishi tayi miscarriage ya je jin gaban shi na wani irin faduwa. Gabadaya jikin shi yayi sanyi har wani kwalla ya ji yana biyowa idon shi. He knows how the pregnancy meant to them most especially her. Is like she find a reason for eternal happiness, ko auren su bai ganin ta ma farin ciki kaman samun cikin ta. She was very fond of the baby, har kayan babies ta fara siya. She is planning on having a nursery for the baby a room in kusa da ita. She plan for every sadly her plans is shattered. Bai son yanda za ta dauki zancen ba a lokacin Amma want thing is for sure zai Sha fama musamman in ya tuno abinda kadai ya iya ji ta fada mishi kenan "Kazo da sauri cause am not forgiven if i lost the baby" that sentence have echoing in his ears since then.

Yana zaune a gaban ta lokacin da ta farka. Da shi ta fara having eye contact, tana ganin irin kallon da ya Mata tayi saurin shafa cikin ta. Kaman ta kasa yarda da lamarin ta Kai idon ta da wuri. Kallon shi tayi alamun tana neman Karin bayani. Pitiful looks in da ya ke aika ma ta kadai ya tabbatar da zargin ta. Da sauri ta fara girgiza kanta tana kiran "No please don't tell me" da sauri ya isa gare ta yayi wrapping inta cikin arma in shi "calm down please, ki dinga ambaton innalillahi wa'inailaihi raji'un" da kyar ta amsa ta nayi har ta samu tayi shiru. Tun daga asibitin ake binta ta ci wani abu Taki. She start acting gloomy ba ta wa kowa magana ba ehm ba Aa da an matsa Mata sai hawaye. Sallama ya nema a ganin shi it will be easier in su ka koma gida.

Maimakon sauki abin ma sai worst yayi. Ya Mata nasihan har ya gaji. "Shin ba ki yarda da kaddara bane Asmau?" Dago manyan idanuwan ta tayi ta zuba mishi kallon kasan me kake fadi kuwa. "You have the right to say Anything Mukhtar? Ya kake so inyi bayan na rasa abinda da nafi so fiye da komai a rayuwata. Do you even care? Ko da yake since from the start ba Wai kayi welcoming babyn bane, is not like you care and you cause it all."

He can't believe what she is saying, Nan ta ke idanun shi suka rikide yace "Asmau are you blaming me"

Gaggawan daga kanta tayi tace "it all your fault i lose the baby. intentionally by refusing to pick my calls."

"It also mine Asmau for God sake Ina da imani"

"Maybe you don't want to have it with me tun da ga farko. I even doubt if you ever love me" tana gama fadin haka ta fashe da kukan, irin mai cin ran Nan.

Tun daga lokacin magana ma ba sa yinta cikin kwanciya hankali. Ta daina komai na gidan Kai Abinci ma tsakura ta ke ba wani abin kirki. Duk ta kare raman har yayi worst, manyan idanuwan ta ko sun fito sosai kaman wacce ta ke fama da wani cuta. Ya rasa yanda zai bullowa al'amarin gabadaya ya gagare shi.
 

ABINDA KAKE SOTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang