11:00 am dai dai na rana ya musu a Zaria don haka straight su ka dauki hanyar Samaru zuwa Jami'ar Ahmadu Bello. Kowa a Faculty insu za a mai Screening in sabanin lokacin Post Utme da dukkan su centers kawai aka tura su, Engineering Muhsin ya sauke Suraj hade da kiran Abokin shi da ke lecturing a wurin ya hada su sannan ya daukin hanyar social Sciences. Har theatre in da ake yi ya taka ma Suhaila yana gaba tana binshi a baya, he can feel the stares from different people, sai da ya tambaya wurin da ake na department insu sannan ya bar ta a wurin "ki kira su Asmau in kin gama ni zan shiga seminar and behave ur self nan University ne, ki kula da kanki" kala bata ce mai ba har ya bar wurin.
Sai da aka kira Azahar ta gama komai hatta Admission letter an bata sai dai dole zuwa washegari zata amsa. Tana gamawa ko ta kira su Asmaun su ka sanar mata inda suke, a cafeteria in hostel ta same su suka ci abinci, sun dade suna hira kafin friends in Suhailan su ka zo su uku, kowacce shigar ta abin kallo ce don ba na arziki, har gwara ma ita Suhailan, Faran faran dai su ka gaisa da su Asmaun, ba su dade ba su ka wuce.
Gidan Abokin Abbah kabeer da ke hayin malam nan kusa da Aviation su ka sauka, Matan gidan mai kirki faran faran ta amshe su da ke suma yan katsinan ne, aiki ya kawo mijin nata Zaria.
Zaune su ke a dakin da ya xamo masaukin su suna hira sama sama yayin da suhaila ke chatting a wayan ta duk bayan yan mintuna. "Wai kinsan me Asmy"
"Sai kin fada" Asmau ta fada tana kallon wayanta kaman tana expecting call ne, rabin hankalin ta ke ga Fadilan rabin kuwa tuni yayi nisa cikin duniyan tunani. "Wai Aslam ya kira ni jiya yana tambayana Wai da gaske an sa rana na sai nace mishi eh, that guy really surprise, he starts ranting da naci Amanan sa kuma ko labari babu na sa shi a wani hali... Like he even ends of crying fa sosai" Dariya Asmau tayi sosai sannan tace "gsky mutumin naki kam bai da lfy, a bi wani jirgin kuma mu kam mun mi shi nisa" wani innocent smile Fadeela tayi sannan tace "ni ko sai ya ban tausayi Allah ni ma sai da nayi kukan" tsaki Asmau ta ja wannan karon "
"Ke dawa kike ta smiling haka In-law" Fadila ta zunguro Suhaila cike da tsokana.
Wani murmushi ta saki "kun san me? prince said he is coming to see me"
Tabe baki Asmau tayi sannan tace "aikin kenan kullum prince kaza prince kaza but you can't even marry him, ina nan kika ce aure zai yi January"
"Eh mana, ai ina da biki" da mamaki Fadila ke kallon ta "stop the ogling sister ni daman ba auren shi zan yi ba"
A tare su ka fadi "to me za ki mishi?"
"Kawai muna tare" ta basu su ko suka shiga girgiza kai suna fadin Al'amarin ki sa ke Suhaila"
"Toh Ya Yusuf fa shi auren shi za kiyi" kallon lafiyan ki kalau tayi wa Fadila sannan ta mike tana kokarin sa kaya.
"Ya iso ne?" "Ya aka yi ya gane location in?" A tare su ka tambaye ta.
"He used his car navigator to locate me" ta amsa, "kaji manyan mutane" Asmau ta fada cike da tsokana ita dai Suhaila murmushi kawai ta musu ta nufi wajen, gab da za ta fita gate in gidan ne ta hango a wurin ya tsaya bai da alaman wucewa hasalima waya ya ke yi hankalin shi kwance, dubawa tayi taga za ta iya wuce wa Sai dai matsalan za ta gogi madubin Motan. Without thinking other wise ta karasa wurin motan ta sa hannu ta kwantar da madubin motan sosai, ba ta damu da kallon mamakin da ya bita dashi ba ta sa kai ta wuce abinta "key!" Ya fada da karfi sai dai ina ko gizau ba tayi ba balle ta juyo ta kalle shi, shiru Tahir yayi cike da mamakin wacece wannan mai halin a gidan su bai ida mamakin ba ya hango prince ya fito daga motan sai bin ta ya ke da kallo mai cike da zallar soyayya. Sai dai ta isa wurin shi sannan Tahir ya samu daman kare mata kallo, nan ta ke zuciyan shi ta buga, shin wannan wata Aljannar ce ta fito daga cikin gidan su, ya jima yana kallon su yanda ta ke ta sarautar ta prince in ko kaman ya durkusa mata, tsab ya gane shi saboda sun yi karatu tare, da kyar ya shige gidan cike da tunanin ta.

YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...