Babi na hamsin da tara ( 59 )

1.2K 100 13
                                    

Gabadaya ta kasa tunanin mai za tace mishi in ya tmby ta. Tun tana tsoron zuwan shi har ta saki ranta. Sunje asibiti da mami kan batun ciwon maran da ta ke, unfortunately shi ne doctor in da ta gani. Normal ya Mata tambayoyi ya tura ta tests, bayan ya ga results in ya rubuta ma ta allurori. Ba Wanda yayi wani Magana daban. Ta kanyi mamakin yanda ya saki jikin shi da itan har wani lokaci ya dinga tsokanan ta kaman ba shi ya Mata confessing abinda ke ranshi ba. Namiji kenan ta fadi a ranta. Though ta kanji tsoron ko he didn't mean what he is saying ganin yanda ya share zancen. Zuwa yanzu ta fara tunanin Muhsin ko wasa ya ke da zuciyan ta don ya fuskanci abinda ta ke feeling akan shi.

One week da maganan su aka tura shi conference Abuja. Sai da yayi sallama da iyalin shi sannan ya nufi gidan Mami. Yana shiga ya iske malam Ado drivern Daddy na sa akwatuna cikin mota. Hannun ya Mika mishi su ka gaisa sannan ya karasa cikin gidan a ranshi yana fadin waye kuma zai yi tfy. Daga mamin har Abbah da sauran yaran gidan su na zaune a babban falo yau da ke weekend ne.

Bayan sun gaisa ne Abbah ke ce mishi "Ah Muhsin ba dai tun yau za ka tafi Abujan ba?"

"Ehmm Abbah ai taron gone da safe ne so i can't make it dole na tafi yau"

Kafin yayi magana ne yaji Mami na fadin "Suhaila Wai ha zaki fito ku tafi bane? Sai Yamma tayi"

Suhaila da ke kitchen ne ta amsa "Mami ganin zuwa fa"

A ranshi ya ke mamakin Daman Suhaila ce za tayi tfy? To Ina zata? Kasa shiru yayi ya tmby Mami "Mami ina Suhailan za ta?"

Hararan shi Mami tayi tace "Ko za kaje ka tmby ta? Oh ni Muhsin"

Abbah da ya fuskanci abinda mamin ke nufi yayi dariya yace "Ah ah Mami banda bin goyon baya da yar wariya fa. Makaranta za ta koma kaji"

Murmushi Muhsin yayi dan ya fuskanci abinda Mami ke nufi. Tunda su kayi magana da Abbah ya fada ma ta ta Kira Muhsin in ya zo ta neman shi. Kashedi ta mishi sosai akan ita ba ta yarda a wa yarta auren dole ba don haka dole shi ya je ya nemi yardar ta. Ganin har yanzu ba taji wani Magana akan ya ma suhailan magana bane ya sa ta ke jin haushi gashi kuma Abbah ya fara maganan bikin za a hada Dana Yusuf so gani ta ke kaman karfa karfa kawai za su wa yarta.

"Abbah to me zai hana in sauke ta a Zarian kawai ba sai malam Ado ya wahala ba tunda hanya ne"

"To ai sauki ne ma suraj je ka cewa malam Ado ya fiddo kayan"

Tashi yayi ya fita ita dai Mami tabe baki tayi tace "Ehmm" daga Abban har Muhsin sai da su ka dara ganin draman mamin.

"Ehm Ehm Mami ba fa a shiga"

"Ai bance komai ba"

Tashi yayi ya fita wajen ya mikawa suraj key in motan shi ya maida akwatunan ciki.

Dai dai lokacin da ya ke komawa falon lokacin ta fito daga ita sai handbag inta. Sanye ta ke da wani hadadden dark purple Abaya ke jikin ta an mishi kwalliya da golden stones. Veil in shi ta yafa akan ta. Kayan ya matukar karban ta. Ya lura da ita tana son Abaya haka kuma ta ke kaunar abu purple. Tuni ya daura ido akan ta ya kasa saukewa kasa cigaba da tafiyan yayi kawai ya tsaya kaman yana wani abu. Jin alamaun ana kallon ta yasa ta dago ai ko four eyes su kayi. Za mu iya cewa kusan a tare zuciyan su ta buga. Saurin basarwa tayi kaman ba ta ganshi ba ta karasa falon. Ganin haka shi ma ya karaso. Sai da ya zauna ta gaishe shi ya amsa sama sama.

"Suhailan kin fito" Abbah ya fada yana kallon ta.

"Eh Abbah"

"Tou Shknn za ku tafi da Muhsin zai sauke ki shi zai wuce Abuja" a take a lokacin sai sa yanayin ta ya canja. Fuskewa tayi tace "Tou Shknn Abbah"

"Muhsin tashi ku tafi Kar dare ya ma ka a hanya"

"To Abbah" ya fadi hade da mikewa. Har mota gabadaya su ka raka su. Kaman kullum ji take kaman Kar ta rabu da Mami. Tabbas ta yi rashi mahafiyar ta ta haihu Amma Allah ya bata mahaifiya na nuna ma saa. Domin ita shaida ce akan yadda Mami ke nuna ma ta So fiye da yaran da ta haifa a jikin ta. Dan kwanta tayi a kafadan tace "Zanyi kewan ki Mami na"

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now