A gajiye likis mima ta shigo gida daga schl, bag park inta ta cire a bayan ta ta ajiye, da sauri ta nufi Falon Maman ta tana zaune da baki a tare da ita. "Sannu da gida mum" ta fada sannan ta gaida bakin da ke tare da Maman nata.
"Sannuki Halima har kin dawo da wuri haka"
"Ehmm mum ba a wani dadewa yanzu ai" tana magana ta nufi fridge in dinning in da ke kusa da falon, chocolates da fiddo da cake da Kuma Habeeb yoghurt a hannun ta. "Oh ni halima ba zai ki daina cin tsaki Nan ba ko"
"Am sorry mum Allah yunwa na ke ji"
"Kuma su zasu kosar da ke Koh?"
Murmushi kawai tayi ta nufi dakin ta, sauran Yan uwanta duk suna school, she is the first born, hutun semester ake yi shiyasa tayi deciding shiga Languages classes. coz already tana level 300 kasancewar an Mata jumping tun a primary school sannan SS2 ta zana waec. Meema yarinya ce hazika tana da kokari sosai ga hankali da natsuwa sai dai ko kadan bata tolerating raini ganin ta ke she deserves respect wurin kowa kaman yanda ita ma ta ke kokarin ba kowa nashi respect ko da kuwa kanne ta ne, a cewarta ko wani Dan Adam ya kamaci a girmama shi. Halima kenan tun tana 16 ta zana waec in which means yanzu shi is only 19 ko da wasa ba ta hulda da samari, ba za ka taba nuna wani kace saurayin ta bane don gani ta ke bata da Lokacin su ma gabadaya, ko kadan ba ta da hayaniya haka Kuma ba ta da yawan kawaye sai dai sama sama, wannan dalilin yasa ko a University ita kadai ke Zama apartment in ta da kenan samaru a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ta ke karantar BSC Nursing. Sai dai yanzu a Nan Abuja ta ke inda su ke Zama kenan. Mum Nabeela ita ce mamarta Baban ta ko da asalin garin Gombe ne Amma a Katsina babansu yayi aiki, Babban Custom ne gashi Yana da Babban kasuwanci, shi din Yana dukiya sosai da shi kanshi bai tunanin ya San adadin su, Allah ya hore mishi sosai sai godiya.
Mum ce ta kwalla wa Meema Kira ta fito da sauri "mum fita Zaki yi ne?" Ta tambaya cike da mamaki ganin Mahaifiyar ta ta ta fito a Shirin fita.
"Am traveling to kaduna halima, kin manta gobe za a Kai kayan yayanku Faisal" Dan zaro ido tayi "wlh na manta, poor lady i pity her" dariya mum ta yi "ku dai kun cika tsugudidi an gaya muku ita haka zai Mata ne" girgiza Kai tayi a ranta tana fadin shiya sani.
"I will be leaving now, nasan ki ki jira kannen ki su dawo kafin ki fita company da ke kin Zama workaholic, mahaifin ki kuma ya biye Miki""Allah sarki mum ba ruwan Dad Ni na ta kura Ina so"
Murmushi kawai mum tayi "and Faisal inma is coming today, be a great host" squeezing fuskan ta tayi in annoyance, ganin expression ya sa Mahaifiyar ta ta bata rai "ban fa son haka halima Yar yar uwata kike wa haka ko? Kija min ace ba kwa son mutane"
"Sorry mum" Meema tayi saurin cewa kafin ta raka mum har mota, driver ya Kai ta train station.
Ko da Faisal ya iso kannen ta sun Riga sun dawo daga Schl so da su jabir ta bar shi illa iya ka ta gaishe shi, nodding Kai kawai ya Mata ya cigaba da harkan gaban shi.
Tayi mamakin ganin shi a kamfanin Dad kwarai don mum ta dai ce Mata zai zo ne Amma ba ta San Mai ainihin zai kawo shi ba, a gaban ta ya shiga office in mangern wurin, sunfi 1 hour suna magana sannan ya fito ya wuce.
Successfully aka Kai kayan Faisal, biki dudu sauran wata biyu kacal ya rage.
•••
Ko da ta koma daf da magreeb ne hakan ya sa sai bayan tayi Sallah ta nufi gun Mahaifiyar ta, ga mamaki zaune ta tarar da ita da Faisal suna Hira. Tana mamakin yanda ya ke iya sakewa Yana Hira da mum haka, ko Mahaifiyar shi bai sake da ita ba kaman yanda ya sake da mum in.
A hankali ta yi yunkurin gaida mum "Mum an wuni lfy?"
Harara mum in ta bita dashi, nan ta ke ta Sha jinin jikin ta "Wani irin aiki Kika tsaya yi a company in da sai yanzu za ki dawo gida?"
Sai a Nan ta ji hankalin ta ya kwanta Jin ba maganar Faisal bane "mum fa wani delivery na Kai, Maman Yasmeen ce ta yi ordern and kinsan ta in aka yi Mata ba daidai ba ta dinga mita kenan, that's why na yi delivery da kaina kafin na dawo gida Kuma a gidan nayi magreeb"
Shiru mum tayi sanin halin Matan, cousin in Dad ce, akwai ta da rigiman bala'i Don dukan su sai ta hada ta musu tas."Ya Faisal Ina wuni?" Ta yi saurin fada kafin mum ta Mata magana, as usual nodding Kan shi kawai yayi sai dai wannan karon har da daga Mata hannu. Ko a jikin ta ta wuce side in Dad insu don Kam ba zata iya Zama kusa da mum ba alhalin su na tare.
Eminent delicacies shi ne sunan company in da su kayi a cikin Abuja, shaharrare ne wajen sarrafa duk wani nau'i na abinci Kama daga nau'in local, international and intercontinental dishes, different varieties of local and modern drinks, every kinds snacks including the locals and traditionals one's, birthday and wedding cakes, smoothies and everything about food. Ana ordering daga different hotels, for weddings, different occasions da ma Kuma home delivery gabadaya. Sannan Kuma suna classes musamman every month suna yaye kusan 100 students har online ma suna classes.
Dad insu Suhaila shine CEO in company in Kuma ya samo asali ne ga son irin business in da Suhaila ta nuna ta nayi tun tana karama, a hankali ya dinga bunkusa abun har yayi fice sosai, is something unique da ba a cika yi a Nigeria ba ma gabadaya, ita kanta Suhailan a can ta koyi komai da ta ke sha'awa and Alhmdlh she is a very good chef da ba abinda za a nuna mata a fannin girki.
•••
Faisal Abdulhamid, mahaifin shi Dan asalin jahar jigawa ne a karamar hukumar Ringim. Sai dai tun suna kana kana su ka dawo kaduna a sanadiyyar aikin mahaifin nasu daya dawo Nan.
Recently ya gama second degree in shi a Dubai, Architecture ya karanta. Tun da ya gama first degree ya dawo gida yayi Service sannan ya koma so yanzu aiki kawai ya rage Mai. He insists bai son yin aiki karkashin wani ya fi so ya gina nashi na kanshi which already sun yi planning da Friend in shi da suka yi karatu tare shi civil engineer ya karanta, family friends ne. so they decides working together but of them iyayen nasu sunyi insisting sai sun yi aiki wani wuri sun samu experience tukunna.
A Abuja su ka Samu aikin karkashin wani building/construction company Mai suna SPDC. Ganin opportunity ya sa suka yi deciding bude small restaurant. Abinda ya Kai shi Eminent delicacies kenan domin samun shawarwari akan harkan da Kuma workers tunda suna yaye mutane ko yaushe.
Faisal miskilin mutum ne sosai bayan abokanan shi har Yan uwa ma complain in halin shi su ke, sai dai fa canji da kamar wuya domin ance Hali zanen dutse. Fiancee in shi ko ita ma a Dubai su ka hadu cousin in Faroukh ne abokin nashi. they were just friends at first even though ko sun hadu rabin hiran ita ke yi ko kadan bai son magana kaman Mai ciwon Baki. He only get interested in her because of her career, she is a planner so Yana ganin za tayi matukar taimaka wa gurin establishing company in da suke da dreams a Kai. Shiyasa ko da ta Zo da maganan aure yayi accepting, gashi da ma Yana tausayin ta sosai a cewar shi da wuya ya samu wacce zata Mai soyayyan da Fa'iza ta ke Mai coz abubuwan da ta ke jurewa akan shi ba kadan bane. Ita dai duk da wannan halin nashi ta yarda ta amince Tana son kayan ta a hakan. Duk da halin ko in kulan shi Yana da kirki sosai ga son zumunci, bini bini za kiji yayi hanyar jigawa ko katsina gaishe da kakannin sa, sai dai fa koya je ba wani maganan arzikin da zai shiga tsakanin ku, zai dai je Miki da tsaraba. Gabadaya yan'uwa ma mum insu Meema ce ya ke sakewa da ita sosai har su kan Dan taba Hira. Ita ko meeman ko kadan jinin ta bai hadu dashi ba don har gwara sauran suna Dan taba shiri barin ma Ya Najib yafi kowa kirki dan dai Anty Sumayya ta dauke musu shi ne sai Kuma MK Shima ba baya ba shi ko Muhsin Shima bai wani magana yawancin in ka ji bakin shi to wa'azi ya ke ma mutum shiyasa su ka sa mishi malam ma. Faisal Kam kwata kwata ba abinda ke shiga tsakanin su bayan gaisuwa ko dan taga ya shanye ta a miskilanci ne? In ba haka ba a Kira Wanda yayi karatu a Dubai da bagidaje?
More are coming...
Please share and suggest the story.
Thank you.
ŞİMDİ OKUDUĞUN
ABINDA KAKE SO
RomantizmCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...