Driving Mukhtar ya ke Amma zuciyan shi gabadaya na ga tunanin ta yanda zai Fara hakura da soyayyan Asmau, shin anya hakan Abu ne Mai yiwu ma kuwa? Ko dai ya fada ma Umar ne kawai ko kuma Ummi? Amma Ummi goyon bayan Umar za tayi, haka dai ya ke ta fama tunane tunanen shi wayar shi ta dau ruri, ga mamakin shi ita Asmaun ce ke Kira da sauri ya dauka yayi shiru Yana sauraron ta ita ma in kuwa shirun tayi sai zuwa can yace "Lafiya ko Asmau?" Kaman jira ta ke yayi magana sai ta sa kuka, shi abin mamaki ma ya bashi, shin a tsakanin su wa zai yi kuka? "Ya Mukhtar shi ne da ka yi tafiyan ka ko Sallama babu ko?" Ajiyar zuciya ya saki Jin yanda zazakan muryan ta ke sauka cikin kunnen shi Yana zagaye kwakwalwarki "Har rakoni Kika you fa ko kin manta ne?"
"Sai fa da ka fito nasan za ka tafi, after all ma why do you leave"
"On business purpose besides I need some peace of mind" Dan jim tayi zuwa can tace "to yaushe zaka dawo?"
"In na gama abinda na ke yi" jiki a sanyaye ta Kira Sunan shi "Are you angry with me?"
"Why will i not Asmeey?"
"I thought kayi Understanding ina amma"
"Its okay am driving, will call you later bye" dif ya kashe wayan.Juyawa Asmau tayi su kayi four eyes da Fadila, murmushin takaici Fadila tayi "What are you hiding Asmau, what's going on between you and Ya Mukhtar"
"Me me Kika gani?" Ta tambaya cikin in Ina.
"Haba baiwar Allah kallo daya na miki na San cewa ba ki da gaskiya, saboda ke Ya Mukhtar ya bar gidan Nan ko?"
Kwalalo manyan idanuwan ta Asmau tayi sannan tace "Nima ban sani ba Fadila"
"He said he love you and you rejected ko?"
"Waya fada miki?" Ta tambaya cike da mamaki.
"Asmau na dade da sanin Ya Mukhtar na son ki Amma da naga har an Dade bai fada miki ba kuma bai sanar wa kowa ba a San da maganan i thought nayi misunderstanding in shi ne but from your action these days nagane"
Murmushi Mai ciwo Asmaun tayi kaman ta fashe da kuka "Fadila i don't know what to do am confused"
"Since you decides not to tell me then i can't interfere" kafin Asmau ta ce wani abu Fadila ta yi saurin fita daga dakin saboda ko da zata ba ta shawaran ta tabbatar da akwai son Kai, Mukhtar Dan uwanta ne da suka fito ciki daya so dole akwai son kan dukka Umar in shi ma Dan uwa ne a gare ta Amma fa Wata kusan tafi wata.
Bara mu gangara garin Abuja.
Meema ce tsugunne gaban Mummy, sai fada mummyn ta ke a dalilin sim card inta da ta ballah, kanta a sunkuye har mummyn ta gama fadan ta ba ta ce kala ba. "An Gaya miki burin mu mu saki a gaba muyi ta kallo ne?" Dai dai nan Daddy ya shigo falon da murmushi kwance akan fuskar shi, yasan ba abinda ke hada halima da mahaifiyar ta in ba maganan aure ba, ako da yaushe shi ke shiga tsakanin su ya dai dai ta lamarin "mummy me muka yi miki ne?" Ya Fadi hade da sama ma kanshi wurin zama. "Gsky Daddy na gaji da halin meema, ya za ayi ace ke shknn ba ki da lokacin wani da namiji a rayuwar ki, wai fa ta je dauko su Tahir a school ne yayan abokin su ya ganta ya nemi numbanta, yaron Dan mutunci har nan yazo gaishe ni wai dan ya kirata shine ta balla sim inta."
Murmushi Dad in yayi sannan ya Kara kallan meema "gsky Halimatu a nan ke ce baki da gsky tunda mum ta yaba dashi ba sai a bashi dama ba a gani, tunda an kosa ki yi auren" da biyu ya Fadi zancen Yana kallon mum, hade rai mum tayi sannan tace "Daman na San Kai ke biye mata ai"
" To ni Kuma mai nace?" Yayi saurin tambaya.
"Ki yi hakuri Dad in Sha Allah in lokaci yayi zan fiddo mijin" murmushi Dad yayi "bakomai haleema shi aure lokaci ne in Allah ya kawo to tabbas dole a yi shi Amma ina so ki sani Allah ya ce tashi in taimake ka so why not kin dinga ba wa mazan da sure ka kawo kokan baran su chance? As long as they are responsible ko dan saboda soyayayan mahaifiyar ki akan ki ga kinyi auren?""In Sha Allahu Daddy" ta Fadi hade da mikewa wurin kofan da taji Ana knocking, Faisal ta gani a bakin kofan dan haka da wuri ta matsa ta bashi Daman shigowa Sai dai straight library tayi saboda ba ta son gaishe shi domin ko tayi Sai ya ga daman amsawa in dai Kuma a gaban mummy ne she have no other choice, ita ko ba ta iya jure rainin wayon nashi abun na matukar Kona mata Rai. Sai dai me? Ba ta Kai ga bude English novel in da ke hannun ta ba Mummy ta kwala mata Kira, fuske a hade ta fita don ta San ba zai wuce akan faisal in bane, ba ta Kai da gama magana ba taji mummyn na mata fada "lafiyan ki meema? Ba ki ga yayan ki bane? Can't you entertain him? Ke ko Mai Sai an fada Miki"
"Am sorry mummy" ta Fadi hade da saurin karasawa kitchen ta dauki side plate, dinning table karasa domin debo snacks in da ke wurin hade da soft drinks. Ba ta San meye sa mummy ta tado ta ba after all ba yau Faisal in ya fara zuwa gidan ba, infact ya wuce a Kira shi da bako Sai dai dan gida Amma tsabagen gidadanci da rashin son magana har yanzu bai gama sakewa ba hatta Daddy bai sake dashi ba da Mummy kawai su ka Saba, har ma gwara gwara brothers inta ta ga suna dan hira sama sama, ta rasa wani irin mutum ne shi haka don abin nashi yafi karfin a Kira shi da miskilanci Sai dai gidadanci. Ko da ta koma falon shi kadai ta iske dan haka ta karasa ta ajiye Mai kan stool in da ke gaban shi, kaman yanda ta zata ko dagowa ya kalle ta bai yi ba balle Kuma ya mata godiya. Kasa jure ta after all abin ta yi a hankali ta fara magana "its good to say thank you, you know?" Dan dago yayi Yana kallon ta da mamaki Sai dai ko 1 minute bai ba ya saukar da idanun shi, kala bai ce mata ba coz he can't remember wani abu ya taba shiga tsakanin su, a wurin ya bar mata abubuwan ta ya wuce falon mummy domin Daman ita ya zo gani ya ko bar meema cike da takaici, ta San ko da ta koma daki mummy Sai ta Kara kiranta don haka bisa dole ta dauka ta bishi falon mummyn, a kasa ta same shi kusa da mummyn suna hira, itan ma kasa kasa ya ke mata magana, a center table in falon kawai ta ajiye ta bar wurin don takaici ko Kara kallon su ba ta yi don ko ya matukar Kai ta bango. Komawa dakin da tayi ta Kira Asmau domin ta mata murnar admission in da suka samu ne ya dan kauda mata takaicin abin barin ma da Asmau ke bata labarin bikin fadila ya taso gadan gadan, tuni ta share komai tana fadin za ta shigo katsina kafin a koma school domin su tattauna sosai akan bikin. "Ya meema me dai kin ki aure gashi har za mu riga ki saura ni da Suhaila" wani abu Mai daci meema ta hadiye sannan tace "gwara ma ke Asmau da naki maganan a kasa Amma Suhaila gwara ma ni" dariya Asmau tayi tana fadin "ai Suhaila ba a gane kanta, Ai Ya mukhtar ma kuwa Yana Abuja yau ya taho"
"Allah sarki zan so kuwa in ganshi kinsan shi Yana da kirki ba kaman..."
Da sauri Asmau ta karasa mata "Ya Faisal ko? Ke dai kin sa mishi Ido wlh" dariya meeman tayi ba tare da ta ba Asmau labarin draman su na yau ba don ko dariya za ta mata ita Kuma za ta ji kunya, Nan su kayi sallama sannan ta fara karanta English novel in nata.
YOU ARE READING
ABINDA KAKE SO
RomanceCike da takaici ya ke kallon ta yayin da idon shi su ka kada su kayi jajawur. Da kyar ya ke iya magana saboda zafin da kirjin ke masa "Asmau? Meyesa za ki mana haka bayan kin San muna son junanmu?kin cuce ni Ku kin cuci kanki. Ina kike so in saka ra...