Babi na Ashirin da daya (21)

875 79 0
                                    

Asma'u da Safiyyah na shiga falon gidan su ka tarda kawayensu sun sa music a falon sai rawa su ke. Tsaki Asmau ta ja sannan ta ba wa Safiyyah wuri ta zauna ta kalli meema "Yah meema har yanzu ba a fara mata kitson ba?"

"Wai da sai lallen ya bushe ko kuwa?" Ta bata amsa.

"No gsky we don't have the time of the world fa, tunda dai jan lallen ya bushe why not a fara kawai"

"Bara in kira Mama toh a turo mai kitson kawai" meema ta fada tana kokarin neman numban Mama Aisha.

Kitchen Asmau ta nufa ta fiddo tray cike da abubuwan marmari ta ajiye gaban Safiyyah "sannu koh, ko za ki dan taba kafin a gama Abinci"

"No am okay" tayi saurin fadi hade da girgiza "ban dade da yin breakfast ba ma" hararan wasa Asmau ta aika mata sannan tace "kin ma isa? Ba zai yiwu ba" meema ma da ta gama wayan ta juyo tana kallon ta "kaman Safiyyah Kado koh?"

"Eh ita ce" ta amsa tana kallon meema tunda ta shigo ta gane meeman ita ce dai ba ta gane ta ba da wuri.

"Allah Sarki na dade ban ganki ba da su Mummy kuka zo?" Nodding kai Safiyyah tayi "Da Ya Yusuf?" Nan ma nodding kan nata ta kara yi "Duniya ni ko ina Halima kado ta ke?"

"Tana nan Covenant University ta ke karatu ta ma kusan gamawa"

"Ikon Allah, ni dai nasan daman da wuya in tana Abuja. Tsaya ma Halima ba tayi aure ba"

Girgiza kai tayi tace "An dai sa month in December Next year amma ba a riga da an sa date ba tukun"

In shock meema tace "wa zata aura?"

"Brother" ta bata amsa kai tsaye

"Ya Yusuf?" Ta fadi cike da mamaki . nodding kai Safiyyah ta mata.

"Allah yayi kenan" a tare su kayi murmushi tuno yanda haliman ke haukan Son Yusuf da su ke secondary shi ko shareta ya ke bai son zance, da ke Allah yayi da kanshi ya neme ta daga baya...

"Ya meema kin ja ta da surutu right? Ai kya sa ta taci wani Abu dai ko, yanzu fa su ka isa nasan ba taci komai ba" Asmau ke ta zuba mita tana kallon meeman.

"Ai fa ta fara kenan, safiyya rufa mana asiri kici wani abu kinji in ba haka ba baza ta bar mu ba" harara Asmau ta je fa mata. Safiyyah murmushi tayi sannan tace wa Asmau "Bara dai na fara shiga bayi ko" ta fadi tana kallon Asmaun.

"Okay mu je mana" daki su ka nufa a nan su ka tadda Fadila na zaune tana chatting,lallen hannun ta ya gama bushewa sauran na kara. Suhaila ko idanunta a lumshe tana sauraron music da ear piece.

Nuna wa Safiyya toilet in tayi bayan sun gama gaisawa da faddi sannan ta juya wurin Fadilan "Ai sai ki tashi ki shirya, mai kitso yanzu za ta iso kin zauna kina chatting Mara amfani"

"Hmm Kawata kenan wlh posts na ke gani a IG, abin mamaki dai bai karewa a duniya"

"See save it please" Asmau ta yi saurin katse ta dan ta San Aminiyar ta ta in ta fara ranting akan Instagram har haushi ta ke bata. Wardrobe ta bude ta dauko ma ta wani gown na atamfa, duk cikin sabbin kayan da za tayi fitan biki da su ne "kinyi wanka kin yi shafa sannan ki kara lafga nightie a jikin ki, sai dai kace ba amarya ba? Come on tashi ki sa kaya" wulla ma ta tayi, haka nan tayi maneji ta sa ba tare da lallen ya taba ba, da kema sauran kadan ya karasa bushewan.

Dukkan su zaune a falo da wasu cousins insu da kuma friends da su kazo daga wani gari suna hira, har Safiyya ma duka. Suhaila ce ta fito da nightie inta Wanda bai kai guiwa ba gashin kanta kuma gabadaya ya barbaje alamun tashin ta kenan daga bacci. Suhaila kenan ko matan sai da su ka yaba balle kuma namiji, straight kitchen ta nufa ba tare da ta kalli kowa ba ta debo Abu a tray ta wuce dinning tana sauraron waka tana ciye ciyen ta.

"Suhaila ba za kiyi lallen bane?" Meema ta tmby bayan an gama nata. "Am coming" kawai ta fadi ta cigaba da harkan ta, sai bayan kusan 10 minutes ta tura ma Asmau text "its noisy there why not ki turo ta nan inda na ke mu yin" siririn tsaki Asma'u ta ja bayan ta gama karanta text in sannan ta juyo ta kalli Suhaila duk da suna Dan nesa da juna ta dago murya "Daman tun da muka taci nagane yau yan abubuwan na kai, ta ya za kuyi lalle a dinning ki taso Ku yi a can. Gefen Falon ta nuna kofan dakuna, wurin na shimfide da carfet, its like a second parlor saboda girman shi sai dai babu Kujeru a wurin.
Kaman ba zata ta tashi sai can ta mike ta nufi wurin, kan kujeran da Safiyya ke zaune ta tsaya tana hararan Asmau alamun zaki Sani. Tabe baki Asmau tayi ta dauke idon ta kan Suhaila. Safiyya jin mutum a kanta ya sa ta dago, four eyes su kayi da Suhaila da mamaki su ke bin juna da kallo sai zuwa can Safiyya ta daure ta furta abinda ke ranta "Yar uwa ke ce?" Lumshe ido Suhaila tayi sannan ta mata nodding da murmushi kwance akan fuskanta.

"You know each other? How?" Fadila Amarya ta tmby tana kallon su.

"We are Friends on social media ai since, she is my partner on..." Girgiza ma ta kai Suhaila tayi sannan ta zagayo ta riko hannun Safiyya su ka karasa wurin da za ayi lallen.

"Ba sai kin hana ta fada ba Suhaila I know, you are a writer on social media" Meema ta fada tana hararanta.

"Ghost writer?" Asmau da Faddi su ka fada a tare.

"Divergent_Muslima ai kun gane ta"

"Unbelievable! I love her stories"

"Her poem and quote are ethereal!" A tare Fadila da Asmau su ka fada suna kallon Suhaila da ko a jikin ta sai kafan da ta mikawa a ka fara mata lalle hankalin ta kwance "Yar uwa za kiyi henna koh?" Ta fadi tana kallon Safiyyah da ta girgiza kai "No way, you have to do it"

Lokacin mai kitson Fadila ta shigo in no time su ka fara, ita ma Asmau wata friend insu da tazo farida ke mata kitso. Sai hiran books Suhaila ta ke. Ita da meema Daman sunce ba za suyi kitso ba. Ana musu lalle suna hira da Safiyyah, gabadaya labarin book in da su ka fara tunanin collaborating su yi su ke magana. Daman dai kullum in suna chatting maganan kenan haka sai suyi 1 hour suna hiran a ways duk labarin rubutu kawai su ke.

"Ya meema how kika gane ta wai?" Faddi ta tmby.

"She wrote something associated to her kind of r/ship with Ya Muhsin on her book and i become suspicious and she write something again on her poem and i accidentally purposefully saw her writing on her system randa muka so KT still na jita tana waya da Safiyya, busy talking about book"

"Kai Ya meema sa ido" Asmau ta fad...

2:00 O'Clock dai dai Mukhtar ya yiwa Asmau 3 missed call tana gani ta ki dauka ganin haka yasa ya kira meema "Ance zaki make up ko? Kun shirya gamu nan zuwa" toh kawai tace ya katse wayan. Lokacin aka gama kitson Amarya don haka Sallah kawai tayi ta shirya hade da daukan kayan da zata sa "Asmau tashi Ku tafi mana ya mk ya kira yana waje fa"

"Ya meema Gsky na fasa zuwa kawai Ku je tare ga zee ma"

Da sauri zainab ta tashi ta dauki gyalen ta tana fadin "mu je to kawai meema" haushi ya kara tamke Asmau ganin yanda zee ke rawan jiki kuma tasan duk akan MK ne. Tabe baki tayi a ranta tana fadin ba wanda zai sa min ciwon kai shi ya ma Sani.

Haka su ukun su ka tafi wurin meenamesh a can su ma assistant inta za ta musu. Su Asmau ko Deejamah su ka gayyato ta zo ta musu. They all looks elegant and adorable.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now