Babi na sittin da tara ( 69 )

1.1K 94 4
                                    

Turo baki tayi tace "please mana, I won't go for an eventless wedding"

"Ya Allah! You are so persistent wlh tun yaushe mu ke magana daya? Why aren't you satisfy with all ladies event wai?"

"Tabdijam tou hotunan bikin fa?" Dariya ya fara har sai da ya ga ta kulu sannan ya daina.

"Zan zo muyi pics in. Is it okay?" Kallon shi tayi kawai ta shige cikin gida ta bar shi a tsaye yana kallon ta.

.....
A week to the wedding Asmau da Mukhtar su ka dawo. A gidan su na katsina su kayi masauki duk da ba haka Asmaun ta so ba Amma kuma ba daman musu.

Gabadaya ana washegari kamu su ka rankaya birnin Dabo. Suhaila tayi farin cikin ganin su sosai barin ma Asmau da aka dade ba a hadu ba. Meema ta yi bulbul da ita kana ganin ta kasan tana cikin kwanciyar hankali da natsuwa. Hakan ya ke gun Fadila, babyn ta tayi wayau sosai har tana kokarin fadin wasu kalmomin.

A nan backyard in gidan Abbah aka yi organizing kamun. Anyi decorating komai ya fito tsaf tsaf. 

Ta Sha Jan lalle da ya matukar amsan ta don cewa tayi ita Sam ba za a Mata baki ba. Haka outfit inta na kamun so simple, she is really a fashionista in a unique ways, just so simplistic... Ana cikin Mata makeup call in Muhsin ya shigo wayan ta. Kin dauka tayi don tasan in har ta daukan to fa sai ranta ya bacci, ba ta San dalili ba tunda auren ya gabato abu kadan ya ke Mata ranta ya bai shiyasa ta ke ta kokarin avoiding in shi.

Meema ne tace Mata "Hala ba ki ji wayan ki na ringing bane?" Tabe baki tayi tace "Ya Muhsin ne, kawai ba zan dauka bane" dariya meema ta sa tace "au duk soyayyan har kin fara kin daukan waya? Ko da ya ke gama jan ajin ki daga gobe shknn" shiru tayi ba tace komai instead ta tsaya aka cigaba da Mata make up in. Ganin ta ki dauka ya sa ya tura Mata text. "The photographer is around, ki sa a shigo da ita. Luv yhu"

Kallon su tayi bayan ta gama karanta Sms in "Wai photographer in ta iso"

Fadila ce tace Mata "Wai ke miye na bata rai?"

"I choose a photographer and he insist Wai sai dai mace" dariya ta basu dukkan su Ukun. Fadila tace "da fa gskyn bai so na miji ya kalle mishi mata kin ga laifin shi?" Fita su kayi su ka shigo da ita. Ana gama makeup in aka fara snapping. Rantsatsen gown na purple lace ke jikin ta. Sai plain alkyabba a kan shi. Ta yi kyau sosai.

Midway through the kamu ya zo as he promised, to her surprise tare da photographer in da ta zaba tun farko. Daga shi sai Yusuf a friends, sauran duk Yan uwa ne. Ba ta wani mishi magana ba sai shi sa ya Mata whispering a kunne "You look ethereal" siririn murmushi tayi tace "Thank you"

"You have been smiling but not to me, me ya faru baby love?"

"Am afraid, scared, it so frightening... I mean i feel like i love you too much"

Kallon ta yayi sosai yace "Are you doubting? Or rather reconsidering?" Nodding kan tayi tace "Aa nasan i can't go back but i can't help been afraid ne kawai"

"Then trust me please Suhaila. I can't love you enough so please let do this okay?" Nodding ta mishi hade da sakin murmushi.

Ana gama pictures gabadaya mazan su ka watse. Dole sai da ta watsa ruwa bayan gama event in. Tana kokarin tada sallah call in shi ya shigo don haka ta bari sai ta idar tayi calling back. Ko da ta gama want sha'ani ne ya dauka ma ta hankali unknown to her he keeps calling ba ta dauka.

Sai da ta dan natsa tukunna ta tuna ya kirata. Da sauri ta nemo wayan ta tarar da missed calls rututu. Tana kokarin calling back call in shi ya shigo.

"Why will i be calling you ba ki picking?" Cikin fada ya ke maganan.

"Sorry.."

"Don't you dare tell me sorry, ban son ji. Ai ba tun yau kika fara ba. Sau nawa Ina Kiran ki ba ki dauka? Na Miki Uzuri Amma ba ki gani ba shiyasa kika cigaba ko? To ba zan dauka ba sanin kanki ne ban tolerating rainin wayau. Like you can't even call back, in ma Uzuri gare ki ai sai ki dauka ki fada min ko tunda kin San ba takura Miki zanyi ba, Amma kika share ni wato in tayi..." Tun tana tunanin abin na kare ne har ta ga ba alaman hakan. Kala ba tace mai ba Amma ranta ya mugun bacci. Daman gabadaya jikin ta a sanyaye ya ke yanzu ko tabbas ta kara tsorata. Tana sauraron shi har ya gama fadan shi sannan ya kashe wayan. Bai nemi cewan ta ba ita ma ba ta tanka ba. Cigaba da abubuwan ta tayi sai dai kana ganin ta kasan ba lfy ba. Su Meema sunyi tmbyn har sun gaji. Abin mamaki sai gani tayi call in shi na kara shigowa wayan ta kin dauka tayi ta sa wayan a silent gabadaya har Fadila na tsokanan ta "Wai ke ana fadan za ayi auren haka?" Ba tace kala ba ta cigaba da abun gaban ta.

After some minutes call ya kara shigowa wayan ta, ga mamakin ta Ya Najib ne. Kallon Fadila tayi ta kakalo murmushin dole tace "and somebody's boo is calling me"

Dariya Fadilan tayi tace "to ai sai ki dauka ko"

"Hello big b" ta fada bayan ta dauka. Sallaman da taji ne ya sa ta bata rai ba shiri, saurin kashe wayan tayi ta ma yi switching off gabadaya sannan ta yi kwanciyan bacci. A bisa dole ya kyale ta ba don ya so ba, ba karamin bacci ranshi yayi ba tun farko da ya ke ta Kiran ta ba ta dauka ba. Dalilin da yasa yayi tunanin deliberately ne saboda kwana biyu ya kan kirata ba za ta dauka ba sai in ya kara kiranta. Ko da ya tmby ta dalili ce mai tayi at times ba ta kusa da wayan ne. Shi dai ya San da ba haka bane ba so bai San me ke faruwa ba now. Bayan ya gama fadan ne jikin shi yayi sanyi kuma yana tunanin ya kamata ya saurare ta. Ko ba komai dazu ta fada mishi abinda ta ke feeling, it means yayi worsening abun kenan. Kira yayi domin su yi magana ta fahimta Amma ta ki dauka. Amsan wayan Najib yayi ya Kira saboda ya San za ta dauka. Gabadayan shi wani iri haka ya samu ya kwanta.
.....

Friday, 13th December 2019.

Tun karfe Uku na dare ta farka tana juye juye kan gado. Ganin abun ba na kare ba ne ya sa ta tashi domin yin Sallah. Raka'a Hudu tayi tana mai rokon Allah bukatun ta gabadaya. Sannan ta zauna ta cigaba da azkar har zuwa lokacin Sallann
Comparabilityn Asuba. Sai da tayi Sallan sannan ta samu natsuwa a zuciyan ta bacci mai karfi ya tafi da ita.

Hayaniya ya tada ta wurin karfe bakwai da rabi sakamakon kaiwa da kawo wa da ake tayi a cikin gidan. Wanka ta yi kokarin shiga tana fitowa ta iske Mami ta shigo ma ta da breakfast. "Mami Ina kwana?"

"Lfy kalau Yar mami, an tashi ko?" Murmushi tayi. Mamin tace "to maza shirya kici abincin a fara kitso"

Tana gamawa ko a ka fara kitson ba su suka tashi ba sai wurin 12:30. Da ke ma kanwar Mami ce, Anty Muniba da tazo daga Gombe tayi kitson. Ranar gabadaya Muhsin bai kirata ba haka itan ma ba ta bi ta kan wayan ba ma gabadaya.

Suraj ne ya kirata a waya "Sister Wai inji Ya Muhsin  ki bani kayan da kika shirya da duk wani abinda kike bukata in Kai Miki can gidan" shiru ta danyi tace "bari in ba Yusrah ta kawo ma ka" Yusrah step sister inta ce. Akwati babba ne da wasu abubuwan ta ta ba da aka fita dashi.

Ana gama kitson wanka ta shiga ta karayi ta shirya. Tana jin an fara tafiya Sallan juma'a cikin ta ya badada kululu. Obviously, she is nervous.

Suna nan zaune suna hira, ana karasa yin abinda ba ayi ba. Kabbara Sallah tayi bayan ta tabbatar an idar. Tana cikin Sallah Mssg ya shigo wayan ta.

Ana sauka daga juma'a kaman yanda addini ya tanadar aka daura auren. Na Su Suhaila aka fara yi kafin na Yusuf. Meema ta shigo tana tsokanan ta "Ta zama ta zama ta zama"

Asmau da ke kokarin hada sauran kayan Amaryan ne tace "Ba dai har an daura ba? An sauko juma'an" Asmau ta tmby

"Yanzu F... Ke fada min, an riga an daura"

"Ayyah Allah ya sa alkhairi" kusan a tare su ka fada. Wani irin faduwan gaba ta ji ya shige ta, kana kallon ta kasan jikin ta yayi sanyi. Asmau da ta fahimci yanayin ta ne tace "Calm down Suhaila, you will be fine I promise" Nan dai su ka haduwa su ka babbata baki har ta samu natsuwa.

Daukan wayan tayi ta duba Sms in da ya shigo.

My Sweet Suhaila,

I promise to love you every day for the rest of my life, even when it gets hard. But knowing us, it's going to be way more good times than bad and way more smiles than tears. I am so thankful for you. You aren't just the lady of my dreams—you're the lady beyond my wildest dreams. Welcome to a new phase of life babe! Congratulations Mrs Muhsin Abdulrahman Malumfashi.

Wani nannauyar ajiyan zuciya ta saki bayan ta gama karantawa. Shirin tafiya Walima aka fara yi domin ba wani abinda za ayi in an Kai Amarya.

A filin ma'aikatan su Abbah aka shirya waliman/budan Kai. Tare aka hada da na Yusuf. Don haka around 2:40 pm aka tafi daukan Amaryan Yusuf in. Ana bada Amaryan direct wurin waliman aka tafi da ita da sauran Yan uwan na ta.

wannan karon ma lace Suhaila ta sa. Dukkan Amaren da laffaya a jikin sanye a jikin su. Sai da aka fara budan Kai sannan aka zarce da Walima. Gabadaya gidan Mami aka wuce kafin aka tafi da Fatima gidan ta.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now