Babi na sittin da takwas ( 68 )

1.2K 96 11
                                    

A gajiye likis ta fito daga ma'aikatar da ta ke siwes. Two weeks kenan da ta fara IT in, 8:00 am to 4:30 pm haka ta ke fama kullum. Wuni suke suna aiki, a hakan ma Wai don IT student in na dayawa... Fatan ta daya Allah ya sa an zo daukan ta, don kwannan haka Suraj ya ke barin ta jira. Ba Daman tace za ta tafi Abbah ya hada su duku biyu ya musu tatas. Ilai kuwa ba ta ga motan Suraj in ba sai dai wani hadadden motan Ash Avalon ta hango. Kaman jira ya ke ya hango ta ya fara zuba Mata horn. Mamaki ne ya kamata ta tsaya tana kallon motan. Daya daga cikin wacce su ka fito tare ne tace ma ta "Suhaila wancan fa ke ya ke wa horn" tabe baki tayi tace "Ni kam ban San kowa da motan Nan ba"

Wata ta kara cewa "kika sani ko sabon kamu ne"

Dayar tace "da rana akan ta" dariya tayi tana mamakin yanda aka yi su ka San an sa mata rana. Ita dai ba ta fadawa kowa ba.

Horn mai motan ya kara yi Amma sai ta yi juyawan ta ma kaman ba ta San anayi ba. Ganin dai da gaske ba za ta zo ba yasa yayi giving up ya bude motan ya fito. Ta gefen ta ne ta juya ta kalle shi. Ji nayi suna furta "wow! Kinga handsome in da kika share kuwa"

Kaman ba za ta juya ba sai kuma ta juya. Ware idanu tayi tana kallon shi cike da mamaki. "Suhaila" ya Kira sunan ta da karfi.

Wata ce tayi saurin cewa "ko dai angon ne?" Murmushi tayi sannan tace "My brother" sallama ta musu sannan ta karasa inda ya ke. Kafin ta isa har ya shiga motan. Tana shiga tace mishi "Yaushe kazo?"

Hararan ta yayi yace "ba gaisuwa sai yaushe nazo?" Ita ma wani kallo ta mai tace "remember ni fa yanzu Antyn ka ce"

Dariya yayi yana reverse yace "Su beauty manya Amaryan Ya Muhsin. I still can't believe this Allah, I mean tun yaushe aka fara ban sani ba"

Siririyan dariya tayi tace "You were in Lagos remember"

"Ba wani Nan. I've been suspecting the both of you tun can daman na Sha fada Miki Ya Muhsin yana ciki Amma you never believe me"

Hannun ta tafa "well, Yanzu na yarda Angon Fati"

  "People thought we were dating kin tuna?"

Nodding Kai tayi yace "Ni kuma nasan i can't go for my brother's Choice"

Hararan shi tayi tace "as if Shiri kuke da shi a da"

Zaro idanu yayi "nasan ba mu dasawa dashi but I've always see him as a good figure, I love him in my own ways. Yanzu dai please alfarma mu ke nema, za ki taya Fatima wasu siyayya ne pls, you have a Good choice.

.....

Tana kitchen ta fara jin knocking  sanin ba kowa a wurin ya sa ta nufi kofan. Ba tare da ta duba ba kawai ta bude, sake baki tayi tana kallon Wanda yayi appearing a gaban ta. Sakaka haka ta tsaya tana kallon shi, ita ba ta motsa ba kuma ba ta bashi wuri ya wuce ba. Abu daya ne ke yawa a kanta shin yaushe ya dawo? Tafi ya Mata a saitin fuska, sai a lokacin ta gane bashi kadai bane. Saurin basu hanya tayi tana fadin "sannun ku da zuwa"

Murmushi Rahma da ke bayan Muhsin ta ke. Cikin ta ya fito sosai, duka duka bai Kai one month ba EDD inta. Kallon Suhaila tayi tace "Yauwa mun same ku lfy?"

Shi dai Muhsin ciki ya nufa yana fadin "Mami na gida kuwa?" Ba Wanda Suhaila ta amsa a cikin su sai dai ison da ta ma Rahma a kujerun Falon.

Dai dai lokacin Yusuf ya shigo falon yana fadin "maraba da babban Yaya"

Hannun ya bashi su ka gaisa sannan ya juya su ka gaisa da Rahma cike da tsokana ya kece Mata "Sannu maman babyn mu" hararan shi Muhsin yayi yace "Mami fa?"

"Mami na falon ta bara na Mata magana" Yusuf ya fadi yana tfy. Dauke da tray Suhaila ta fito daga kitchen ta ajiye akan stool in da ke gaban Rahma. "Nagode Sister" Rahman ta fada, murmushi kawai tayi ta juya, unfortunately su kayi four eyes da Muhsin. Kasa Fassara kallon da ya Mata tayi don haka kawai ta basar. Kitchen in ta koma tana mamakin dalilin da yasa bai fada ma ta dawowan shi bayan sun yi waya. Yanzu ta gane dalilin da yasa ta Kira numban shi bai shiga. In har tace ranta bai bacci ba to tabbas tayi karya. Tana iya jiyo maganan Mami daga kitchen tana fadin "maraba da bakin turai" sannan su ka gaisa da Rahma tana tmbyn ta jikin ta.

ABINDA KAKE SODove le storie prendono vita. Scoprilo ora