Babi na talatin da daya ( 31 )

847 83 11
                                    

Fir Asmau taki komawa makaranta har su meema su ka tafi su ka barta. A cewar ta sai a sallame shi, kukan da ta ke musu ya sa suka hakura su ka barta. Abin kuma sai yazo da sauki saboda sallaman da Mukhtar ya samu daga wurin doctor, bayan sun daura shi akan magunguna da kuma shawarwari.

Kwanan shi biyu a gida ya matsa yana son ya koma bakin aikin shi saboda ya kwana biyu da dawo wa har Yusuf ya tafi ya barshi.

Ba don Ummi ta so ta barshi ya tafi bayan ta mishi dogon nasiha mai cike da gargadi da kashedi, duk dai akan Asmau ne. Murmushin takaici kawai ya ke a ranshi yana fadin "In kika rasa ni ba shikenan ba" sa wa ummin tayi ya sauke Asmau a Zaria in zai wuce Abujan.

Ba wani hiran arziki da ya shiga tsakanin su har su ka kusa Zaria, gaza hakuri Asmaun tayi a hankali tace mishi "yanzu in ka koma sai yaushe kuma?" Siririn murmushi ya saki yana kallon ta ta gefen ido yace "sai bikin ki, in kuma na Yusuf ya riga toh zan dawo lokacin"

Dum! Ta ji gaban ta ya buga sakamakon ambaton bikin ta da yayi. "Am so sorry Ya Mk, Wlh nima Ina sonka I have no choice ne" tunda su ke da Asmau, yau ne rana na farko da ta yi confessing feelings inta towards him, amma maimakon yayi farin ciki sai tausayin su day ya mamaye shi. "Na sani Asmau ko da ko ba ki fada ba, ki kwantar da hankali. Ko wani Dan Adam da kaddarar sa, may be shi din ne alkhairi a gare ka. Ki maida hankalin ki kan karatu sosai, i trust so don't let me down" murmushi ta saki mai ciwo tace "I will miss you terribly"

"I won't let you to miss that much ai, we will always talk. I will always be there for you and its a promise"

"Ka kula da kanka please Ya mk, banda kin shan magani da rashin cin abinci, Just don't let your self fall sick again please."

Wannan karon juyawa yayi gabadaya ya kalle ta, irin kallon da ke cike da zallar kauna da kullawa, murmushi ya sakan mata a hankali yace "I shall try to do that, just for you" kasa cewa komai Asmau tayi sakamakon halin da ta shiga a sanadiyar kallo da murmushin da ya mata, sai lokacin ta kara tabbatar wa kanta tana son Mukhtar, komai na shi tafiya ya ke da imanin ta. She is madly, truly and deeply in love with him. Sai dai kash! Feelings yayi karfi a lokacin da hakan ba zai amfane su ba. Yanda ya nuna mata ya hakura da ita itama hakanan za ta daure ta basar da duk abinda ta ke ji. Sai dai ta San ba karamar wahala za ta sha ba, sai yanzu ta fuskanci halin da Mukhtar ya shiga a baya a kanta saboda sai yanzun ne ta fahimci soyayyar shi ya mata mugun kamu mara misaltuwa.

Saurin shanye kukan da ke Shirin taso mata tayi tace "Please kayi branching kaduna, faddi will love to see you ta damu sosai"

"Ban so inyi missing flight Ina but i will squeeze in je in gantan"

Murmushi kawai tayi har ya sauke ta a bakin apartment insu ba wanda ya kara magana. Waving hannu su ka ma juna ta na kallo har motar shi ya bace sannan da kyar ta daga kafan ta ta shiga ciki.

...

Kaduna.

Tun kafin ya shiga garin ya Kira Najib, da ke weekend ne dukkan su suna gida. Direct gidan ya nufa. Da Najib in su ka fara haduwa a falo, bayan sun gaisa ya tafi kirawo Fadilan.

Ilham na manne akan cinyan ta tana hada musu kaya a bag zasu tafi wurin maman su. Turo baki Arif ya kara yace "Anty ni fa in ba zaki bi mu gidan su mummy ba nima ba zani ba?"

Kallon shi tayi cike da mamakin rigiman yaron tace "My boy why? Ba ka son kaga mummyn ka ne?"

"Ina so mana but together with you please"

Ta tunanin amsan da za ta bashi Najib ya shigo da gudu Arif yayi wurin shi yana fadin "Daddy please kana kacewa Anty har da inta zamu wurin mummy"

Dago yaron yayi hade da shafa kanshi yace "My boy ka cika rigima Allah, Anty babba ce so no way za ta je hutu yara kawai ke zuwa" turo baki yayi.

Najib ya kalle ta yace "Mukhtar na falo, ki zo ku gaisa he is in hurry" ai ba ta ma jira ya karasa ba ta ajiye ilham ta nufi falon da gudu ba tare da ta lura da kukan da ilham in ta saki ba. Tana ganin shi ta fada jikin shi hade da sakin kuka, dagota yayi yace "Fadila are you okay" nodding kanta tayi tace "Ya Mukhtar kaine ka dawo haka, ka rame sosai" murmushi kawai yayi a ranshi yana fadin halan ita ba taga raman da tayi ba ta ke fadin nashi. Bai kawo komai a ranshi ba illa tunanin kila laulayi ta ke.

"Ya jikin naka? Are you well?"

"Fadila am okay, na ji sauki fa kukan me kike? Oya share hawayen ki" da sauri ta goge tana fadin bara in kawo maka Abinci.

"No am in hurry, ko kina so inyi missing flight ne?" Girgiza Kai tayi hade da fadin "duk da haka bara na kawo maka drinks ka tafi dashi. Murmushi yayi yana fadin "iyyeh Fadila an girma" dariya tayi cike da kunya ta tafi dauko mishi.

Najib ne ya fito tare da yaran, Arif na ganin yaje wurin shi duk da ba Wai ya wani San shi bane. "Arif ashe ka zama big boy" Mukhtar ya fada yana shaking yaron. Ko da ya so daukan ilham ki tayi sai ma hannun da ta ke mikawa Fadila ta dauke tana kukan rigima. Da sauri Fadila ta amshe ta hannun Najib, harara ya maka mata ba tare da Mukhtar ya gani ba. Ilham kam har da sakin ajiyan zuciya jin ta a jikin Fadila. Har mota su ka raka Mukhtar sannan su ka dawo. A falo Najib ya fara fada "What are you doing Fadila, meye sa zaki ajiye yarinya ta na ihu ki wuce ki barta, wato you don't care ko?" Ba tace kala ba har ya shiga daki ya dauko bag insu yana fadin "shknn bara in kaisu wurin wacce ta damu dasu tunda ita ai tasan ciwon su" wani siririn hawaye Fadila taji na zubo mata tayi saurin sharewa "Allah ya baku hakuri" tace ta yi hanyar dakin ta. Hade baki Arif yayi kaman zai yi kuka yace wa baban "Daddy ni dai ka daina wa Anty fada bana zo"

Kallo daya baban ya mishi yayi putting yaron into place "come on my friend let's go" kaman zai yi kuka haka ya shiga motan, Ilham har ta gama kiriniyar tayi shiru na amso ta da akayi agun Fadila.

Ranar gabadaya haka ta wuni sukuku, tunda ya fita bai dawo ba. Itan ma ba tayi wani tsammanin dawowan nashi ba. Sai dai Asmau ta Kira ta tukunna ta warware sun dade suna waya da Asmaun. Inda gabadayan su sun fuskanci junan su ja cikin matsala duk da ha wanda ya furta wa wani. "Next weekend in Sha Allahu za ki ganni kawata"

"Kawata please ki zo mana, haba tun bayan aurena ace bamu hadu ba? You know is not fair ai, tunda ke kina da dama kizo mana"

"Da gaske na ke zan zo. I need to see you"

Murmushin fadila tayi tace "toh sai na ganki, ki gaida Anty meema da mutuniyar ki in kun hadu" tsaki Asmau ta ja sannan ta katse wayan.

ABINDA KAKE SOWhere stories live. Discover now