1

698 40 2
                                    


*💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝*


Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.

Not Edited
POST 2020
REPOST 2023

Allah yasa yarda na fara rubuta wannan littafin nawa na gama shi lafiya tare daku, ina kuma godiya ga dukkan masoya na babu abinda zan ce da ku sai godiya,
Allah ya kijikan wanda suka ragamu gidan gaskiya, Allah ya bawa marasa lafiya lafiya,muda muke da lafiya Allah ya kara mana Love you all😘



If one advance confidently in the direction of his own dreams and endeavours to live the life that he has imagine, he will meet with success unexpected in common hours.'''



1.

Gidan Alhaji Hussain Ahmad gida ne,wanda ya amsa sunansa gida, na dai_dai mutanen dake cikin sa,yana 'ya'ya da mata d'aya mai suna Fatima da 'ya'ya biyar mata biyu maza uku, 'yar sa ta farko Hajara wacce ake ce mata Iman, su kuma k'annan ta suke ce mata Anty, sai Ahmad,suna masa Mujahid, Sulaiman Ana ce masa Baffa, Maryam wacce suke ce mata Siyama, sai k'aramin su Faisal shi kuma suna ce masa Sultan,wasu kuma su ce masa auta, mahaifin su dan asalin Gombe ne, mahaifiyar su kuma 'yar jigawa ce a Gumel, a yanzu suna zaune a Kano aiki ya kawo shi,ma'aika cin banki ne, mahaifiyar su kuma nurse ce.

Suna zaune cikin wadata da farin ciki, da kyakykyawar tarbiyar da suka bawa yaran su mai ban burgewa, kowa yana san yaran basu da nak'asu ko kad'an, sai dai Maryam wacce suke ce mata Siyama sam halin ta da nasu ba d'aya bane.

A waje bata nuna komai amma da zaran ance ta dawo gida kuma shikenan babu zaman lafiya ita ce tsokana, ita ce surutu damun su, kowa yasan halin ta a gida suka dai suka san halin ta.

Tafiya suke a cikin mota su shida har wanda yake tukawa, babu abinda suke sai zancen wata da suke yi, kowa da abinda yake fad'a a kanta,
wanda yake tuk'a motar kana gani zaka san mahaifin su ne.

Magana yayi da cewa.

"kunga ya ishe ku haka nan, idan kuwa ta jiku kuda ita ne".

Matar dake zaune a gaba,wanda ita ce mahaifiyar su tace.

"Tana nan babu wanda ya isa yayi magana, sai dai idan taran numfashin ta akayi"

Anty tace.

"Ai wannan yarinyar halin ta sai ita, Amma wai Daddy baya gani".

Daddy yace. "Idan tana nan kuyi ta zancen ta amma sai ta dawo ku addabeta ta addabe ku".

Sultan wanda shine k'arami a motar,
yace.

"Ai ni bama so ta dawo wallahi, tana dawo wa zata addabe ni".

Mujahid ne ya karb'e maganar da cewa.

" Takaici na ma yanzu idan ta dawo babu batun koma wa, tayi candy''.

Baffa yace.

"Wallahi Yaya nima abinda nake tunanin kenan tunda na tashi kafin mu shirya, bana san takura, idan kuwa ta dawo shikenan zaman gidan ya dena dadi".

Daddy ne yayi dariya yace.

" Duk ku gama,zan fad'a mata, kowa abinda yace a kanta".

Mama tace. "Ai yarinyar nan, bam bata jin magana,kana gama mata fad'a kamar ta d'auka,tana yin gaba tama manta abinda kace".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now