18

102 12 1
                                    

*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

*SHAFI NA 18📑*

*__________📖* "ki kwanta kiyi bacci ki huta zan fada maki, amma kidena tunanin sa".

Wani hawayen ne sabo ya zuba a fuskar ta tasa hannu ta share tare da daga wa Mama kai, daga ta tayi daga jikin ta ta share mata hawaye tare da girgiza mata Kai.

Tace, "Nasan Siyama ta bata da saurin kuka amma yanzu gashi tana nema ta zama Mai saurin kuka ya akayi haka?"

Da murmushi a fuskar ta ta fada kuma cike da tsokana shine ya bawa Siyama dariya ta rungume Mama yayin da Mama ta Shiga shafa kan ta cike da kulawa, har tayi bacci sannan ta kwantar da ita ta dauko hula tasa mata tayi mata addu'a tare da kashe mata wutar dakin dake saman gadan ta, sannan ta fita.

Washegari da safe taji ta ras sai dan abinda ba'a rasa ba na gajiya dana Zazzabi  haka ta fita ba Wanda ya tashi kamar yarda tayi tsammani Bude kofa tayi ta fita waje direct wurin Takunya tana zuwa kuwa suka fara mata kuka rungume su tayi tafara musu surutu sannan ta zuba musu abinci ta dan jima a wurin su sannan ta fito kitchen ta Shiga ta wanke hannun ta fridge ta bude taga dabino dariya tayi ta dauko babban robar dabinon ta fito parlour sai da ta kunna kallo sannan ta fara ci, taci kusan rabi bata damu ba da taci hakan ba.

Tace, "daman ma da Zuma".

"Bari na tashi naje na dauko Allah yasa ba'a canja mata waje ba".

Kitchen ta koma ta bude inda suke ajje kayan cin su ta dauko kwalbar zumar ganin su Cincin din ta abin ya bata mamaki ita Tama manta da tayi, plate ta dauka ta deba ta fita fuskar ta cike da farin ciki haka ta hada tana ci tana kallo bata re da tasan ta cinye dabinon ba ta shanye zuma tas ta cinye.

Agogo ta kalla taga tara ta wuce, tashi tayi ta Shiga dakin su batare da kwashe kayan da ta ci ba, dakin su Baffa ta fara Shiga suna kwance sai sharar bacci suke abin su a bakin kofa ta tsaya tana tunanin me zata musu har ta juya sai kuma ta dawo ta Shiga toilet ya debo ruwa ta tsaya a Kan su.

"Sultan, Ya Baffalo oya a tashi gari ya hawaye bakyau baccin asara Ku tashi".

Juyi sukayi tare da jan bargo, ruwan dake hannun ta ta watsa musu a fuska ba shiri suka tashi zaune a firgice, ita kuma ta arta a guje tana dariya ta shiga Mujahid Shima baccin yake zuwa tayi ta tsaya akan sa.

Tace, "Ya Mujahid, ya Mujahid".

"Mtsww! Meye?"

Ya fada Yana kallan ta, cuno baki tayi ta tayi folding hannun ta.

Tace, "Yaya yace kaje Ka siyo min immm Yama immm yawwa kosai nake san ci ka taho min da sim card shikenan abinda yace".

Ta karashe da dar waja baki, wani tsakin yayi ya koma ya kwanta.

Tace, "laaa, humm nidai ba ruwana sako makoko kuma wallahi..."

Pillown daya wurgo mata ne yasa tayi hanyar kofa tana gunguni taje ta zauna tana kumbura baki.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now