*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 31📑*
*__________📖* juyowa sukayi jin muryan Hajjo, Siyama kuma ta sunkuyar da kan ta tayi kalar tausayi Hajjo na tahowa ta zauna a kujera.
Tace, "Sannu kinji kin rame Baban ku yace mun jiya ne kacal ashe shanya ni yayi ke kina nan sun zabgar min dake kin rame kamar wanda ake tsakurar ki sai k''ashi".
Mujahid yace, "Hajjo magani fa zata sha kuma babu abinda taci".
"Ahh yarinya ta ci abinci kinji yarinyar kirki maza ci".
Baffa yace, "kin d'au shayin kin sha ko kuwa?"
"Bana ce taci ba kuma ku muzguna mata ran ku ne yanzu nan zai b'aci".
Tashi tayi ganin an kawo mata kayan ta ta shigar dashi d'akin, dawowa kusa da ita yayi ya d'auki cup d'in ya fara bata a baki sam taji komai ya fice mata a rai bata san jin cin komai ba ko rabi ba ta sha ba ta kelo masa a mai a jiki daga ita har shi b'ata su tayi.
Mujahid yace, "iskancin banza baki da bakin cewa kin k'oshi ko kuwa? kalli yarda kika sa mutane aiki".
"Uban wa ya matsa ta data sha? ina kune yanzu dan tayi masa amai a jiki shine za'a ke yi mata fad'a, ban tab'a ganin yaran da suka tsani 'yar uwar su irin ku ba idan mutum beda lafiya tausayin sa ake amma ku fad'a kuke mata yanzu kun kyauta?"
'Bata fuska sukayi suna cin magani Siyama kuwa kuka tasaka aganin Hajjo kukan fad'an da suka mata ne sai dai ita ba haka bane kukan rashin had'uwar su tayi da kuma cewan wai basu san zai dawo ba.
Babu wanda ya tanka mata bare ta kuma cewa wani abu tana zaune suka gyara wurin tsab suka gyara mata jiki sannan aka mayar mata da drio d'in ta bayan tasha magani ganin tayi bacci yasa suka tafi Baffa yaje kai Hajjo gidan Abba ganin tayi bacci, Mujahid kuma ya koma d'aki ya kwanta jin basa nan yasa ta bud'e idan ta tana kallan parlourn taga bakowa ta jayo plate d'in da take shan romo ta m cire drip d'in ta tsiyaye shi tas aciki a d'auki ruwa tasha ajje akan plate d'in ta mayar da carnularn ta kwanta abin ta a haka bacci ya d'auke ta.
Mujahid na zuwa beyi wata wata ba ya cire wannan d'in ya sa mata wani ya fice dan yin sallah koda ta tashi taga drip rabi sai ta k'ara bud'e idan ta taga de rabi sannan ta kalli ina daka ajje d'ayan taga babu.
Mujahid yace, "ki k'ara tsiyayar da ruwan kiga nayi ta d'aura miki kenan''.
Turo baki tayi gaba s ta gyara kwanciyar ta sai ga Hajjo nan ta zo ta shigo tana masifa.
Mujahid yace, "Gaskiya Hajjo gaba d'ayan ki ciwon kai ce".
"Albasa batayo halin ruwa ba wai a haka ne Fatima take cewa kafi kowa rashin magana da'ace ka biyo mai sunan ka ko kunama ta cije ka bazaka yi magana ba".
Baffa yace, "sai bai biyo shi ba".
"Ina kuwa ya biyo ai ko mafari beyi ba balle su hanya kuma".
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...