*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°*
*1442H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.**SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_
*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_
*SHAFI NA 26📑*
*__________📖* "Shine musabbabin canzawar ta ta canza fiye da tunanin mai tunanin bata da zurfin ciki amma dalilin sa tana yi, bata da tsoro amma saboda Shi tana yi, tana jin tsoron ta sanar dashi gamu mu kuma muki mara mata baya babu wanda ta sanar wa sai ni, nima sai da na matsa sannan ta sanar dani".
"Wata rana ina zaune a k'ofar gida yazo ya zauna kusa dani bayan ya min sallama na amsa daga gaisuwa ya fara min bayanin anan unguwar wacce yake so take na tambaye shi wanne layi yace min besani unguwar ma dak'yar ta fad'a masa sunan unguwar ya kuma ce sunan ta Maryam Ahmad yana fad'a nasan lalle shine Abubakar dan na tabbatar na tambayi sunan sa koda na tambaya shi d'inne kamar yarda nayi tsammani bance nasan ta ba kawai shiru nayi na k'yale shi azaman da nayi dashi anan nagane shima yana san ta wani aiki ne ya kawo shi makarantar shima kamar Abban ku yana aiki yana kasuwanci a cikin lokaci kad'an muka saba dashi kullum sai yazo muyi ta yawo muna neman gidan sai da na tabbatar dagaske yake san ta kuma a d'an zaman da mukayi dashi nagane mutum ne da beda matsala ta ko ina sannan daga k'arshe na fad'a masa yayi murna sosai da hakan na gabatar dashi a wurin su Hajjo da kawun mu duk da ita bata sani ba har sai da aka sa rana sannan yaji labari ba k'aramin murna tayi ba sai dai bata nuna ba dan harda kunya soyayya Abubakar ta sa mata wanda a da sam bata san wata kunya ba kamar de ke".
Shiru yayi yana kallan ta ganin ta k'ura hoto d'aya ido Maryam d'in ce da yaran ta, duk hoto baya concentrating wannan kawai taga ya juyo shima da'alama kiran shi akayi ya juyo dan hannun sa na kan sark'ar ta ya rik'e chain d'in sark'ar ba shi d'in take kallo abin sark'ar take kallo imaging kamar wacce ya bata, jin Daddy yayi shiru yasa ta d'agowa.
Tace, "Kuma anyi aure?"
Murmushin yayi wanda kana zaka san na had'iye wani abu mai d'acin gaske.
"Ba'a wani ja lokacin bikin ba semester d'aya kawai ta k'ara dayake ban d'auki hutu ba a weekend kawai aka yi bikin Yaya kuwa daman bezo bikin ba taji haushin rashin zuwan sa da beyi ba, sai ranar da za'a kaita yazo shima be jima ba ya bata hakuri sannan ta hakura shima dakyar ya bata hakurin kasancewar basa jituwa shi bazai bawa k'auwar sa hakuri ba, ranar kuwa ansha kuka ranar da za'a kai ta nima kai na naji ba dad'i bare kuma Hajjo, Hajjo harda kukan ta".
"Dayake Kano ne har dani aka kai ta gidan kawai nagani na Kona gidan da nake zama, a haka ban tab'a zuwa ba duk da muna gari d'aya Yaya kuwa daman be san gidan ba shi yake hanani zuwa duk sanda naso ganin ta amma sai ya hanani dayake muna haduwa duk jummu'a idan yana gari. Sai da ta shekara sannan naje shima ban fad'a masa ba ranar da naje kuwa a cikin wani hali na ganta tana labour da'alama Shara take dan da tsintsiya a hannun ta da gudu na k'arasa kusa da ita na d'ago uwar mijin ta.
Tace (Hajjaty's voice),"Subhanallahi k'ato a gidan mu? uban me ya shigo da kai?"
Ko kallan ta banyi ba bare tasa ran zan tanka mata na wuce ciki na ajje ta hijabin da nagani bansan ko na waye ba nasa mata muka fito inajin ta tana magana.
YOU ARE READING
A RAYUWAR MU
General FictionTa kasance ta samu kulawa iyaye da kuma 'yan uwa babu Wanda yasan halin ta sai su, bata fushi ko kadan bare kuma tayi zuciya. yayin da ya kasance ya samu soyayyar Mahaifi bayan ya Rasa Mahaifiyar sa tun Yana karami sai dai kuma Hajjaty tayi masa...