15

90 11 0
                                    

💝💝 A RAYUWAR MU 💝💝

Wannan shine littafi na uku, ga wanda ba su sami damar karantawa su karanta a yanzu, na kawo muku a A BAKIN WAWA. FARIN CIKI NAH, yanzu kuma na kawo muku A RAYUWAR MU. Zan kuma ƙara kawo muku SHAHEED sai a A SOYAYYAR MU. Ba zama lalle na kawo shi ba kwanan na gama. Nagode sosai da ƙaunar da kuke bani.


Not Edited
POST 2020
REPOST 2023






*°🔘° A RAYUWAR MU°🔘°* 
    
       *1441H/2020M.*
      

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL✍🏼*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SADAUKARWA GA:* _IYAYEN NAH 🥰🤗🥰_

*TUKUICI GA:* _sweetheart😘_

*SHAFI NA 15📑*

*__________📖* Waigawa ya fara yi ganin babu wani wurin boya gashi ga dukkan alamu sun kusa zuwa dasauri ya nufa wurin da yaga kamar Yana kusa da shi ya buya ganin kofa ce ma a wurin yasa Shi budewa yaga a bude take fita yayi ya rufe sannan ya zaga ya fita daga gidan da sauri ya dawo ganin Daddy da yayi dashi da Mai gadi lafe wa yayi yana kallan Shi dayake gari ya dan fara yin haske Yana kallan shi har ya wuce shima Mai gadin ya koma daki da saurin sa na dingishi ya fice daga gidan a Hankali ya fita kada Mai gadi yaji karan bude kofa.

A cikin gida Mama ce ta sauko dan tana darwa da Daddy abin da zai ci kasancewar Monday ce kuma Shi da wuri yake fita motsin ta da yaji shine ya  tafi, saukowar tayi zata Shiga kitchen kamar ance juyo, ta juyo ta kalli Siyama dake kwance a Kan kujera gaban ta taji ya Fadi ba shiri ta matsa kusa da ita aikuwa ita ce, tsayawa tayi ta kasa tantance wanne Hali take ciki, hawaye ne da dariya kawai suke zuba a idan ta tana kallan 'yar ta ta yarda ta kode cikin kwana uku kacal, a tare su mujahid suka Shiga Gidan daman sune  suke kunna hasken parlourn idan zasu fita masallaci ganin Mama na kallan kujera tana kuka yasa su karasowa zasu fara tambayar lafiya bakin su ya makale ganin Siyama a kwance sultan ne ya fara taba ta.

Yace, "Mama ta dawo? Ita ce ta dawo? Me yafaru? Yaushe ta dawo? Siyama tashi ki fada mana waye ya sace ki Dan Allah mana ki tashi, Mama taki tashi bacci take?"

Daddy ne ya shigo.

Yace, "Meye haka? Muryan sultan nake ji da asubar nan lafiya?"

Babu Wanda ya bashi amsa sai da ya zago ya gani zama yayi ya daura kan ta a cinyar sa Yana kallan ta kaf yaran sa yafi san ta besani ba ko soyayyar da yake ma 'yar war sa ce ta dawo kan ta kasancewar sunan ta yasa mata.

Shafa fuskar ta yayi Idan sa fal kwalla ya kalle su yarda suka yi wani carko carko suna kallan su sultan a tsugunne Yana kallan ta.

Yace, "da kanta ta dawo?"

Mama na hawaye.

Tace, "Anan na ganta nima amma Dana fito naji motsi".

"Kenan kawo ta akayi?"

Mujahid ya fada muryan sa a raunane.

"Maybe".

"Haka ma".

Daddy yace, "Inaga hakanne  amma waye? Ku duba, nidai banga kowa ba anan da muka dawo".

"Ko ta kofar baya yabi".

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now