53

89 12 0
                                    

🤍🤍🤍
*A RAYUWAR MU
      🤍🤍🤍      
*1442AH/2020M•*
 
          
   

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼

*NA MARUBUCIYA:-*
*HIJJART ABDOUL•*

*SADAUKARWA GA:-* '''IYAYEN NAH 🥰🤗🥰'''

*TUKUICI GA:-* _Sweetheart_ 😘

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook Page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*SHAFI NA 53📑*

*__________📖* Da safe suka tashi suka shirya tsab abin su suna fitowa sukaga Daddy be tafi wurin aikin ba yana zaman jiran su d'auke Kai Hajjon Gombe tayi ta wuce kitchen ta d'auko musu abinsu, yayin da Hajjon Gumel ta zauna a kujera ganin haka yasa Daddy saukowa k'asa ya dawo kusa da ita ya gaishe ta, ta amsa cike da fara'a, sai kuma yayi shirun ya rasa taya zai fad'a masa har Hajjo ta fito suka fara ci abinci suka fara hira ya gaida Hajjo ta amsa a tak'aice kar ma ya kawo mata wargi can de ya daure.

Yace, "Amm Hajjo daman nace ko zaki sa baki a saki ita sirikar ta Siyama..."

"Waya ce ma sirika ce? kaka ce fa, yanzu ina ruwan kaka da shiga rayuwar sabgar jikan ta a'a sai ita shine muma a matsayin na Kaka muka shiga muma ayi da mu kuma Wallahi 'yar mu da ta b'atar sai an biya mu ato yanzu ma can zamuje muji ta fad'a ko bata fad'a ba".

Hajjon Gumel tace, "Nafiso suyiwa 'yar banza rugurugu idan basuyi bazata fad'a ba naga taurin kaine da ita kamar  d'an taure naga haka take magana ma bata dame ta ba".

"Sai mugunta fal ciki".

Daddy yace, "Kuyi hakuri ku sake ta tou, kunga d'anta bazai ji dad'i ba, yanzu idan kune aka kama ai kunga baza ba muji dad'i".

Hajjon Gumel tace, "Wanne hali ne mukuwa zamuyi 'dan nan ai halin na d'aya ba ina mu ina wannan hali?"

"Yoo Hajjaju kema da kika bashi amsa, da ace muna wannan halin irin na matar nan wallahi da baka zauna lafiya da iyalin ka ba".

Mama ce ta sauko ta zauna kusa da Daddy ta gaida su suka amsa a tak'aice.

Tace, "Dan Allah kuyi hakuri abi komai a sannu..."

"Fatima ki kiyaye ni ba kunyar Babar ki nake ji ba yanzu nan sai na maki tatas anan wurin".

"Ai basan yarinyar take ba shiyasa zata bamu hakuri, yanzu de a zamanin nan kin tab'a jin inda ace 'ya tayi sati har uku ta shiga na hud'u da aure ko gidan bata sani ba amma tana da lokacin aiki".

"Fatima? ashe daman haka kike? yanzu haka kika yiwa Iman? to d'auke ta zanyi daman itama basan zaman gidan nan take ba can d'in ma anyi rashin sa'a bata so daga ita har mijin idan yana san ta ya biyo ta su zauna acan".

Daddy ya kalle ta, ta b'alla masa harara.

Hajjon Gumel tace, "Kinyi dai-dai hakan shine dai-dai ai haka ma za'ayi Allah yasa ta fad'i inda suke".

"Idan bata fad'a ba mu ma zane ta ta fad'a".

"Haka za'ayi kuwa".

Daga haka babu wanda ya k'ara yin magana har Muhajid daya fito iya iyayen sa ya gaidar koda ya gaida su basu amsa sai harara da Hajjo Gombe ta zuba masa ko ajikin sa ya wuce ya ci d'auko abinci ya wuce dining besan makara hakan yasa shi zurzurawa da sauri kawai ya tashi zai tafi.

A RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now